User talk:BnHamid

Page contents not supported in other languages.
Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Barka da zuwa!

Hausa Wikipedia na buƙatar gudummuwarku domin ta bunƙasa!

Barka da zuwa Hausa Wikipedia, BnHamid! Mun ji daɗin gudummuwarku. Kuma ina fatan zaku tsaya ku ci gaba da bada gudummuwa. Anan ƙasa ga wasu shafuka da zasu taimaka wajen fahimtar Hausa Wikipedia da yadda ake gyara ta:

Zaku iya yin sayinin rubutunku idan kuna akan shafukan tattaunawa ta hanyar alamar tilde guda huɗu, kamar haka (~~~~); yin hakan, zaisa sunanku da cikkaken kwanan wata. In kana buƙatar wani taimako, ku duba Wikipedia:Tutorial, ko kuma ka tambayeni a shafina na tattaunawa. Na gode.~~~~(Aliyu shaba (talk))

Gajerun rubutu ba maƙala bane![gyara masomin]

Assalam naga kana ta ƙirƙirar shafuka masu taƙaitaccun bayanai da basu wuce layi ɗaya zuwa biyu ba. Waɗannan rubutu ba su cancanci zama maƙala ba, dan haka za'a goge su duka. Domin ƙarin bayani game da yadda zaka rubuta cikakken maƙala ga bayanai nan a sama a saƙon maraba. Nagode. Em-mustapha talk 16:13, 13 ga Yuni, 2022 (UTC)Reply[Mai da]

Godiya da kara Janyo Hankali[gyara masomin]

Assalamu Alaikum BnHamid, muna godiya da gudummawa da kake bayarwa a wannan shafi kuma ayyukanka suna yin kyau matuka. Ina so in dan janyo hankalinka ta yadda ayyukanka zasu fi armashi. A yanzu muna fuskantar cigaba a wannnan shafin namu ta Hausa Wikipidiya sai dai akwai karancin mukalai/articles akan muhimman jigogi da suka shafi asalin Hausa, Hausawa, ire-iren abinci, al'adu, gidajen watsa labarai, wasan kwaikwaiyo na Hausa wato Kannywood, jaruman fina-finanmu na Hausa, abubuwan da suka shafi arewacin Najeriya, kudancin Najeriya da ita Najeriya baki daya, 'yan siyasanmu da makamantansu. Wadannan shafuka sunfi mahimmanci kan mu rika fassaro mukalai da suka shafi wata kasa, da fatan ka fahimce ni kuma zaka kara bada karfi wajen sanya mukalai da suka shafi wadancan muhimman jigogin. Muna fatan zaka tsaya ka cigaba da bada gudummawarka. Mu huta lafiya Patroller>> 10:46, 7 Oktoba 2022 (UTC)Reply[Mai da]

Wa'alaikumssalam, Malan Bashir. Na fahimta sosai, kuma inshaallahu zan yi hakan. Nagode. BnHamid (talk) 11:02, 7 Oktoba 2022 (UTC)Reply[Mai da]

Inganci:Mustapha Ado Muhammad[gyara masomin]

Aslm user:BnHamid, nayi wa wannan mukala da alamar gogewa saboda watakila wannan shafin bai cika ka'idojin Wikipedia, saboda anyi tagging dinshi don gogewa a Wikipedia ta turanci. Tabbas indai aka goge shafin nan a can to muma zamu goge wannan. Da fatan zaka cigaba da bada gudummawarka mai albarka a wannan shafin. NagodePatroller>> 22:50, 14 Nuwamba, 2022 (UTC)Reply[Mai da]

Ok. @Uncle Bash007 BnHamid (talk) 06:37, 15 Nuwamba, 2022 (UTC)Reply[Mai da]

Gyara akan Mukalai da aka wallafa sau biyu[gyara masomin]

Aslm BnHamid, barka da asuba da kuma kokari. Hakika naji dadin janyo hankali da kayi akan mukalai da aka wallafa har sau biyu kuma na duba na goge guda. Da fatan zaka cigaba da bada gudummawa kuma idan ka ga wani gyara zaka gyara ko kuma ka nemi masu ikon hakan. Mu huta lafiya.Patroller>> 06:11, 29 Disamba 2022 (UTC)Reply[Mai da]

Wslm @Uncle Bash007 inshallah. BnHamid (talk) 06:57, 29 Disamba 2022 (UTC)Reply[Mai da]

Janyo Hankali[gyara masomin]

AslmMal. BnHamid da fatan kana lafiya. Ina mai matukar jinjina maka da gudummawa da kake bayarwa a wannnan shafi na Hausa Wikipedia. Sai dai ina kara jayo hankalinka kan wasu abubuwa guda biyu kacal; na farko hujja wato references na biyu kuma na ga an fassara wata mukala kuma akwai muhimman bayanai wadanda babu su a cikin wannan shafin kamar misali a wannan shafin na Fatima Massaquoi da Fatima Yusuf inda duka ba'a sanya hujja ko daya ba kuma babu wasu muhimman sassa wadanda akwai su kuma a ainihin shafin na Turanci da aka fassaro daga su. NagodePatroller>> 08:06, 4 ga Janairu, 2023 (UTC)Reply[Mai da]

Wslm. @Uncle Bash007 Waɗannan shafin kwara biyu da ka ambato asama. Maƙalar farko ba ni nayi translation nataba. (Idan ka duba history na shafin zakaga ainafin username na Wanda yayi translation ɗin). Sannan Makala tabiyu, Gwanki yayi translation nata (idan ka duba historyzaka tabbatar itama). Bugu da ƙari na dai yi Editing akan su amman bani nayi translation ɗin su ba. Kuma Inshallahu duk maƙalar da na tarar idan ba references zanyi ƙoƙari insaka. Nagode. BnHamid (talk) 08:27, 4 ga Janairu, 2023 (UTC)Reply[Mai da]
eh hakane.. tabbas sai daga baya na lura da hakan. Da fatan ka tashi lpia, fatan alheriPatroller>> 07:21, 5 ga Janairu, 2023 (UTC)Reply[Mai da]
Alhamdulillah. Ina godiya da fatan alheri M. @Uncle Bash007 BnHamid (talk) 19:07, 5 ga Janairu, 2023 (UTC)Reply[Mai da]

Vital articles[gyara masomin]

07034373521 wannan itace number ta Whatsapp ka turo min link ɗin ta Whatsapp Muhammad Idriss Criteria (talk) 08:22, 24 ga Janairu, 2023 (UTC)Reply[Mai da]

Sannu da Aiki[gyara masomin]

A matsayin admin a wannan shafi, na turo maka wannan sako ne domin na jinjina maka yadda kake ƙirƙirar ingantattun maƙaloli a Hausa Wikipedia. Da fatan za ka cigaba da wannan aikin. Nagode Gwanki(Yi Min Magana) 17:18, 26 ga Janairu, 2023 (UTC)Reply[Mai da]

Ina godiya sosai M. Abubakar A @Gwanki. Inshallah zan cigaba da bada gudunmawa. BnHamid (talk) 05:39, 27 ga Janairu, 2023 (UTC)Reply[Mai da]