Jump to content

Ahmed Bolori

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mukala mai kyau
Ahmed Bolori
Rayuwa
Haihuwa Maiduguri
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Kanuri
Hausa
Turanci
Sana'a
Sana'a ma'aikacin gwamnati

Ahmed Umar Bolori jakadan zaman lafiya ne kuma dan fafutuka daga jihar Borno, wanda a halin yanzu yake rike da mukamin mai baiwa gwamnan jihar Kogi shawara kan hulda da jama’a sannan kuma shine shugaban sadarwa da hulda da hukumar bunkasa zuba jari ta jihar Kogi.[1][2]

Gwamna Yahaya Bello yana gabatar da Ahmed Bolori ga shugaban kasa Muhammadu Buhari

Ahmed Bolori ya yi digirinsa na farko a fannin hulda da kasa da kasa a jami'ar Ecotes dake Jamhuriyar Benin. Ya kuma yi wani digirin a fannin harkokin gwamnati da kuma digirin digirgir a fannin harkokin kasa da kasa da diflomasiya, duka a babbar Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

A matsayinsa na mai sharhi kan zamantakewa, sau da yawa ya sha fitowa a BBC, Jazeera, DW, da sauran kafafen yada labarai na cikin gida da na waje.[3] Kafin nadin sa a matsayin mai ba da shawara na musamman, Ahmed ya yi aiki a matsayin Babban Darakta a ma'aikatar sakai ta Exit Lanes, gungiyar sa-kai mai zaman kanta da ta kebe don bunkasa zaman lafiya, hadin kai, da cigaban al'umma. Bayan ta'addancin Boko Haram a Najeriya, Chadi, Nijar, da Kamaru, da kuma wasu tashe-tashen hankula na siyasa da suka haifar da takarkarewar tattalin arziki, talauci, da rashin tsaro, karkashin ma'aikatar ta Exit Lanes, Ahmed Bolori ya jagoranci wani tsari na yin kira da hada kan jama'a kan yaki da ta'addanci don inganta ilimi, samar da zaman lafiya, da kuma kawar da matasa daga goyawa ta'addanci baya, da tsattsauran ra'ayi.[4]

Kana ya yi aiki tare da kungiyoyi daban-daban a kan batutuwan da suka shafi inganta rayuwar al'umma, kariya da bunkasa harkokin kasuwanci.[5][6][2]

Domin tinkarar wadannan kalubalen da ake fuskanta ta fuskar ta'addanci, Ahmed ya halarci taruka da dama da kuma ganawa da masu ruwa da tsaki na yaki da ta'addanci na kasashen waje da na cikin gida kamar rundunar sojojin Najeriya, da hukumomin tsaron Najeriya, da masu ruwa da tsaki daga Birtaniya, da Gabas ta Tsakiya da sauran su daga sassan duniya. Ahmed ya gana da shugaban Addini na Tibet, Dalai Lama, kai-tsaye, don koyo game da wanzar da zaman lafiya. Shi dan kasuwa ne wanda ke goyon bayan tsarin SDGs na majalisar dinkin duniya.

A shekarar 2017, Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka (USIP) ta zabi Ahmed Bolori a matsayin daya daga cikin gogaggun shugabannin Matasa guda 25 na duniya da ke aiki a yankunan da aka fi fama da ta'addanci a duniya domin bunkasa karfinsu wajen aikin samar da zaman lafiya a kasashen su.[3] Horon wanda aka gudanar a fadar Dalai Lama da ke kasar Indiya, an yi shi ne da nufin horar da wadannan shugabannin matasan akan yadda za su gudanar aiyukan su cikin sauki. Wadannan da sauran nasarorin da suka samu, sun sanya Ahmed ya yi tasiri a tsakanin takwarorinsa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, inda ta’addanci ke kawo cikas ga cigaban al'umma. Hakan yasa kungiyar wanzar da zaman lafiya ta duniya ta nada shi a matsayin jakadan Zaman Lafiya.[7]

Bayan kokarin sa na shiga tattaunawa domin kawo karshen rikicin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa tana nemansa a shekarar 2016 tare da Ahmed Salkida da Aisha Alkali Wakil.[8][9] Nan take ya mika kansa bayan samun labarin neman nasa, amma hukumomin sojin Najeriya sun ki tsare shi, sai dai suka buƙaci ya koma gida ya dawo washegari.[10][5] Wannan dai ya haifar da cece-kuce inda da dama ke nuna rashin jin dadin matakin da sojoji suka dauka na gaggawar bayyana neman sa ruwa a jallo ba tare da bin ka'ida ba. Sai dai daga baya mahukuntan tsaron kasar sun wanke shi, lamarin da ya sa matasa da masu fafutuka a fadin Najeriya suka yaba masa.

Don karfafama wasu, ya yi sharshi da dama game da kwarewar sa akan kafafen sadarwar zamani har ma akan shirin TEDx.[11][2]

  1. ABDULHAMID, IBRAHIM. "Kogi gov. appoints Ahmed Bolori special adviser, public relations -..." Yerwa Express News. Archived from the original on 2021-05-07. Retrieved 2022-07-05.
  2. 2.0 2.1 2.2 "TEDxAsokoro | TED". www.ted.com. Archived from the original on 2022-07-05. Retrieved 2022-07-05.
  3. 3.0 3.1 "AIA Spokesman". Africa Intelligence Agency (in Turanci). Archived from the original on 2021-05-10. Retrieved 2022-07-05.
  4. "Nigerian journalist wanted over Boko Haram video". www.aljazeera.com (in Turanci). Archived from the original on 2022-07-05. Retrieved 2022-07-05.
  5. 5.0 5.1 "Nigeria: Sojoji sun saki Ahmed Bolori". BBC News Hausa. 2016-08-18. Archived from the original on 2016-08-22. Retrieved 2022-07-05.
  6. Bolori, Ahmed (2020-03-30), In The Pursuit of Peace, Fear is Useless, archived from the original on 2022-07-05, retrieved 2022-07-05
  7. "(Ambassador) Ahmed U. Bolori – Channels Television". Archived from the original on 2022-07-05. Retrieved 2022-07-05.
  8. "Boko Haram Video: Bolori, Wakili On Wanted List Report To Army". Channels Television. Archived from the original on 2020-08-05. Retrieved 2022-07-05.
  9. sunnews (2016-08-20). "Boko Haram: Salkida, Wakil and Bolori: The quest for mediation that went awry". The Sun Nigeria (in Turanci). Archived from the original on 2016-08-21. Retrieved 2022-07-05.
  10. Ishaq, Mudathir (2016-08-18). "An baiwa Bolori da Aisha wakil beli". Legit.ng - Nigeria news. Archived from the original on 2022-07-05. Retrieved 2022-07-05.
  11. ProgressVideo 2022. "ProgressVideo.TV: In The Pursuit of Peace, Fear is Useless | Ahmed Bolori | TEDxAsokoro via TEDx". ProgressVideo.TV. Archived from the original on 2022-07-05. Retrieved 2022-07-05.

Hanyoyin hadi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]