Ali Mustapha Maiduguri

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ali Mustapha Maiduguri
Rayuwa
Haihuwa 1968
ƙasa Najeriya
Mutuwa 2019
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a scholar (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci

Sheikh Dr. Ali Mustapha Maiduguri (1968-2019), Shahararren malamin addinin Musulunci ne wanda ya shafe rayuwar sa a fannin koyo da koyar da Ilimi na addinin Musulunci a Najeriya.

Farkon Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Sheikh Dr. Ali Mustapha a anguwar Fezzan da ke birnin Maiduguri jihar Borno Arewacin Najeriya a shekara ta 1968. Mahaifin shi Alhaji Shettima Bukar Mustapha Konduga dan asalin karamar hukumar Konduga ne, mahaifiyar shi Hajiya Yakaka Bukar 'yar asalin karamar hukumar Dikwa duka a jihar ta Borno.

Tarihin karatun sa[gyara sashe | gyara masomin]

Shi dai Dr. Ali Mustapha, ya fara karatun shi na farko a wurin mahaifin shi inda kuma ya fara da karatun Tahiya, Sallah da Al-qunutu. Daga bisani ya shiga makarantar Allo (tsangaya) a wajen wani malami mai suna 'Mallam Awa' a nan unguwar Fezzan a shekara ta 1972, ya yi karatu har zuwa lokacin da malamin nashi ya samu larurar tabin kwakwalwa sakamakon hatsarin mota. Hakan ya sa mahaifin shi yasa shi a makarantar Islamiya mai suna Madarasatul Nurul Atfan wadda a yanzu aka canja mata suna Usman Islamiya School a shekara ta 1975. Bayan ya kammala aji biyar a wancan lokacin, sai Mallam ya garzaya zuwa makarantar High Islamic College Maiduguri a shekara ta 1982, inda ya yi shekaru hudu a matakin sakandare, daga nan ya ci gaba da karatun DiFuloma a Fannin harsunan Hausa da Larabci da kuma ilimin Shari'a a wannan makarantar. Bayan ya gama a shekara ta 1990, sai aka musu jarabawar daukan malamai inda ya samu nasarar zama malami a nan High Islamic college a mataki na grade ll teacher. Malam ya kwashe shekaru bakwai yana karantarwa, daganan ya samu ci gaba zuwa Jami'ar Musulunci ta Madina a shekara ta 1997, sakamakon jinya da ya yi wadda ta yi sanadiyyar jinkirin zuwa, hakan ya sa hukumar Makarantar ta ajiyeshi a Matakin Shu'ubah (remedial) inda kuma ya yi shekara daya daga nan ya soma karatun shi a fannin Shari'a da harshen larabci a nan ma malam ya yi shekaru hudu. Kammalawar shi keda wuya, sai malam ya nemi damar ci gaba da karatun shi na digiri na biyu wato Masters degree a Fannin Usulul Fiqihi. A jarabawar da suka rubuta, malam ne ya zo na daya a cikin daliban da suka zo daga Najeriya a shekara ta 2002, amma bai samu damar fara karatu a wannan shekarar ba sabo da mutum biyu kacal aka dauka a cikin mutane 27 da suka ci jarabawar daga kasashe daban - daban. Daga nan malam ya dawo gida Najeriya inda ya fara karatun babbar difiloma wato (National Diploma) a makarantar El kanemi College da ke Maiduguri a fannin Shari'a a shekarar 2003. A shekara ta 2004 kuma, malam ya garzaya Jami'ar Jos a garin Jos inda ya yi karatun shi na digiri wato (Masters degree) a fannin larabci, kuma ya yi nasarar kammalawa a shekara ta 2006. A shekarar 2015, malam ya fara karatun digirin digirgir wato (PhD) a fannin larabci a Jami'ar Jahar Nasarawa (Nasarawa State University) inda ya kammala a shekarata 2017. [1]

Ayyukan da matsayin da ya rike[gyara sashe | gyara masomin]

  • Malam ya taba zama grade ll teacher a shekara ta 1990 - 1997
  • Limancin Sallolin Juma'a da na Idi na tsawon shekaru 25
  • Malam ya yi aiki a matsayin Daraktan shari'ah a ma'aikatar harkokin addinai ta jihar Borno daga shekara ta 2005 har zuwa rasuwarsa
  • A mataki na kungiya kuma, Malam shi ne shugaban Majalisar Malamai na farko a mataki na MMC, sannan shugaban majalisar malamai na jahar Borno.
  • Sheikh Ali Mustafa an zabe shi mamba na majalisar koli ta kasa shekaru da dama kafin Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau ya nada shi matsayin babban Sakataren Majalisar Malamai na kungiyar Izala ta kasa bayan rasuwar Sheikh Dr. Al Hassan Sa'id Jos.

Iyali[gyara sashe | gyara masomin]

Sheikh Ali Mustafa ya bar mata daya da 'ya'ya 15.


Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://mobile.facebook.com/JibwisNig/posts/1835000553234533