James Peace

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
James Peace
Rayuwa
Haihuwa Paisley (en) Fassara, 28 Satumba 1963 (60 shekaru)
ƙasa Birtaniya
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a mai rubuta kiɗa
Kayan kida piano (en) Fassara

Kenneth James Peace an haifeshi ranar 28 ga watan Satumba, shekara ta alif ɗari tara da sittin da uku 1963) a garin Paisley. Shi marubucin waƙoƙin yaren Scotland ne, mai kaɗa fiyano a taron mawaƙa da makaɗa, saʼannan mai zanen hoto da ginin mutum-mutum.

Tarihin rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An kuma haifi Kenneth ranar 28 ga watan Satumba a shekarar 1963, a garin Paisley.[1][2] Ya yi ƙuruciyarsa a Helensburgh, wani gari a yammacin Scotland wanda ya yi kaurin suna wajen halartar ʼyan yawon shakatawa. Akwai masu sanaʼar zanen hoto da ginin mutum-mutum da yawa a cikin danginsa, ga misali, John McGhie. Bugu da ƙari, yana da dangantaka da Felix Burns, wani shahararren marubucin waƙar rawa a farkon rabin ƙarni na ashirin.[1][3] Tun yana ɗan shekara takwas, ya koyi kaɗa fiyano, saʼannan yana da shekara goma sha huɗu ya aiwatar da bikin wasan kaɗe-kaɗe na farko a bainin jamaʼa.

Bayan shekara biyu, ya kuma shiga makarantar koyon kiɗa da wasan kwaikwayo mai suna Royal Scottish Academy of Music and Drama wadda a yanzu ake kira Royal Conservatoire of Scotland. Shi ne ɗalibi mafi ƙanƙanta da makarantar ta taba ɗauka.[1][2][3][4]

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 1983, James Peace ya kammala karatun digiri na ɗaya kan fannin koyar da fiyano a jamiʼar Glasgow.[4][5] A shekara ta 1984, ya karɓi takardar shaidar karatun difiloma kan aiwatar da kiɗa, bayan ya yi kiɗa tare da ƙungiyar mawaƙa da makaɗa ta RSAMD a taron kaɗe-kaɗen fiyano na 1 na Mendelssohn.[1][6] Bayan ya bar karatu ta hanyar bin ƙaʼidar koyarwa, an yi ta buƙatarsa a matsayin mai kaɗa fiyano, Ya zauna a garin Edinburgh daga shekarar 1988 zuwa 1991.[1][2]

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Nazari[gyara sashe | gyara masomin]

James Peace ya zauna a garin Bad Nauheim a Jamus (Harshen Jamusanci: Tarayyar Jamus) daga shekara ta 1991 zuwa 2009.[6][7][8] Daga shekara ta 1998 ya yi nazarin waƙar rawar tango, har ya shirya faifayin waƙa wato sidi (CD) mai suna ʺTango Escocésʺ (Waƙar Tangon yaren Scottland) daga waƙoƙin tango na fiyano da ya rubuta.[8][9]

Memba[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta 2002, ya zama memba a Kolejin waƙe-waƙe da kaɗe-kaɗe da raye-raye na Victoria wato Victoria College of Music.[3][8] A wannan shekarar, wato 2002 ɗin ya zaga arewacin Jamus a watan Satumba da Oktoba, wuraren da ya kaddamar da taro na salon kiɗa da waƙa da rawa irin na mutum ɗai-ɗai.[10] A watan Nuwanba, ya zaga ƙasashen gabashin Asiya masu nisa, saʼannan a ƙasar Hong Kong, ya fara aiwatar da waƙarsa ta tango wadda ya mata lakani da ʺTango 17ʺ, wato ʺTango XVIIʺ.[8][9][10][11][12]

Tango Milonga op. 26
Tango XVIII by James Peace (James Peace, piano)

Daga bisani, ya zaɓi da ya aiwatar da waƙoƙinsa a Turai.

Waƙa[gyara sashe | gyara masomin]

A Turai, ya aiwatar da waƙokinsa na tango a hedikwatar ƙasashe kamar: Amsterdam da Athens[13] da Berlin[14] da Brussels da Helsinki[15] da Lisbon[16] da Landan da Madrid[17] da Oslo[18] da Reykjavik[19] da Vienna[20]. Don a shaida aikin da ya yi a kan tango, a shekara ta 2008, ya zama memba a Kolejin mawaƙa na Landan, wato London College of Music.[1] Bayan ya zauna na ɗan lokaci a Edinburgh, a watan Febrairun shekara ta 2010. ya koma da zama a garin Wiesbaden a Jamus.[1][3] Wannan ya kuma ƙara masa shaʼawa da azanci na ƙirƙira, har ya shirya gajerun finafinai na wasu waƙoƙin da ya rubuta. Fin irin na abin da ya faru a zahiri, wato dokumentari mai suna ʺK. James Peace a garin Wiesbadenʺ, wato ʺK. James Peace in Wiesbadenʺ na ɗaya daga cikin ayukansa na wannan nauʼi[21][22]

Muhimman waƙoƙin da ya rubuta[gyara sashe | gyara masomin]

• Magangarar Ruwa (Turanci: The Waterfall)[23]

• Waƙar Yabo Da Safe (Faransanci: Aubade)

• Kukan Zuci (Turanci: Silent Tears)

• Ganyaye Da Aka Manta (Turanci: Forgotten Leaves)

• Faretin Biki Lamba 1 (Turanci: Ceremonial March No.1)

• Faretin Biki Lamba 2 (Turanci: Ceremonial March No.2)

• Zinariyar Bazara (Turanci: Autumn Gold)[24]

• Madauwamiyar Waƙa (Turanci: Eternal Song)[1]

• ʺDon Georgiaʺ (Harshen Georgia: საქართველოსთვის)

  (Kalmomi: Tamar Chikvaidze, Zurab Chikvaidze da James Peace)

• Waƙoƙi 24 don makaɗin fiyano[1][9][21][22]

Lambobin girma da lambobin yabo[gyara sashe | gyara masomin]

• Lambar Girma ta Farko, Gasar Agnes Millar. Glasgow, 1983[4]

• Lambar Girma ta Karko, Gasar Dunbartonshire EIS. Glasgow, 1984[4]

• Lambar Girma na Inshaʼin Sibelius, Glasgow, 1985[4]

• Difilomar Girmamawa, Gasar Tsara Waƙa ta Kasa da Kasa ta TIM. Rum, 2000[1][2][5]

• Difilomar Girmamawa, Giɗauniyar IBLA. New York, 2002[1][2][5]

• Lambar Tunawa, Kungiyar Kaɗa Fiyano Mutum Biyu ta Kasa da Kasa. Tokyo, 2002[1][2][5][25]

• Lambar Gwal, Kungiyar Masana ta ƙasa da ƙasa a Garin ʺLutèceʺ. Faris, 2005[1][2]

Hulda da Kasashen waje[gyara sashe | gyara masomin]

James Peace - Idylls Op.4b

Souvenir de Buenos Aires (don makaɗin fiyano) - youtube

Autumn Gold - youtube

Lento Lacrimoso - youtube

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.00 1.01 1.02 1.03 1.04 1.05 1.06 1.07 1.08 1.09 1.10 1.11 1.12 Birgitta Lamperth. ʺBabu ʹMuryoyiʹ Marasa Armashiʺ. Wiesbadener Tagblatt (Jaridar Jamusanci), 10 Fabrairu 2011
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 2.4 2.5 2.6 Julia Anderton. ʺ ʹRawar Tangoʹ Tamkar Labari Na Jin Daɗi Da Rashin Jin Daɗiʺ. Wiesbadener Kurier (Jaridar Jamusanci), 24 Maris 2012
  3. 3.0 3.1 3.2 3.3 Sabine Klein. ʺWaƙata Tanaa Kama Da Ni-Mai Bayyana Soyayya Kararaʺ. Frankfurter Rundschau (Jaridar Jamusanci), a shekara 1992, bazawa lamba  264, p.2
  4. 4.0 4.1 4.2 4.3 4.4 G. Müller. ʺRuhin Fiyano Ya Yi Rawar Tangoʺ. Kulturspiegel Wetterau (Jaridar Jamusanci), 17 Mayu 2001, p.5
  5. 5.0 5.1 5.2 5.3 Deutsche Nationalbibliothek. “James Peace”
  6. 6.0 6.1 ʺJames Peaceʺ. FRIZZ (Mujallar Jamusanci), a watan Janairun shekarar 2004, p.5
  7. Manfred Merz. ʺDuniyar Fasaha Da Sanin Soyayyaʺ. Wetterauer Zeitung (Jaridar Jamusanci), 12 Nuwamba 1992, p.19
  8. 8.0 8.1 8.2 8.3 ʺJames Peaceʺ. The Tango Times (Mujalla a New York), lokacin hunturu 2002-2003, bazawa lamba 39, pp.1-5
  9. 9.0 9.1 9.2 National Library of Scotland. ʺTango estudioʺ
  10. 10.0 10.1 ʺJames Peaceʺ. La Cadena (Mujalla Harshen Dutch), a watan Satumba 2002, p.26
  11. TangoTang (Jaridar Taiƙaitattun Labarai Na Wata-Wata), Hong Kong, 8 Oktoba 2002
  12. ”James Peace“. South China Post (Jarida a Hong Kong), 9 Oktoba 2002
  13. Takardar Jerin Abubuwan Da Aka Aiwatar a Bikin Mawaƙa Da Makaɗa, {Για σένα Αγγελική}, 27 Oktoban shekarar 2016
  14. Tangodanza (Mujallar Jamusanci), bazawa lamba 1/2002, p.9
  15. Hoton Tallar Bikin Mawaƙa Da Makaɗa (Finlan), 2014
  16. Hoton Tallar Bikin Mawaƙa Da Makaɗa (Portugal), 2016
  17. Hoton Tallar Bikin Mawaƙa Da Makaɗa (Ispaniya) «¡Feliz cincuenta cumpleaños, 2013!»
  18. Listen.no: James Peace (Flygel), Munch Museum, Oslo 16 Oktoba 2004
  19. Ríkarður Ö. Pálsson. ʺSkozkir Slaghörputangoárʺ. Morgunblaðið (Jaridar a Ayislan), 14 Oktoba 2004
  20. Takardar Jerin Abubuwan Da Aka Aiwatar a Bikin Mawaƙa Da Makaɗa, Fiyena 23 Janairu 2005
  21. 21.0 21.1 National Library of Scotland. ʺK. James Peace in Wiesbadenʺ
  22. 22.0 22.1 Deutsche Nationalbibliothek. ʺK. James Peace in Wiesbadenʺ
  23. Wiesbadener Staatstheater, Takardar Jerin Abubuwan Da Aka Aiwatar a Bikin Mawaƙa Da Maƙada, 12 da 19 Satumba 2021
  24. Schwäbische Post (Jamus). ʺSautin Amon Goge Ya Tashi Bisa Kan Makaɗaʺ. 4 Yuni 1994
  25. Kungiyar Kaɗa Fiyano Mutum Biyu ta Kasa da Kasa (Tokiyo). Jerin Sunayen Waɗanda Suka Sami Lambar Girma, 2002