Joseph Edet Akinwale Wey

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Joseph Edet Akinwale Wey
mataimakin shugaban ƙasar Najeriya

ga Yuli, 29, 1966 - ga Yuli, 29, 1975
Babafemi Ogundipe (en) Fassara - Olusegun Obasanjo
Rayuwa
Haihuwa ga Maris, 1918
ƙasa Najeriya
ƙungiyar ƙabila Yarbawa
Mutuwa Disamba 12, 1990
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Digiri admiral (en) Fassara

Vice Admiral Joseph Edet Akinwale Wey (yarayu daga March 6, 1918 zuwa December 12, 1991)[1] yakasance hafsan sojin Ruwa ne a Nijeriya, yayi aiki a lokuta daban-daban, amatsayin sa na shugaban Nigerian Navy (wato Chief of Naval Staff),[2] da kuma Ministan Harkokin waje na wucin gadi,[3] sannan kuma yazama Chief of Staff na Supreme Headquarters,[4] haka yasa yazama de facto Mataimakin Shugaban Nijeriya lokacin janar Yakubu Gowon.

An haife shi a birnin Calabar a watan Maris shekarar 1918 a gidan Yarbawa da Ibibiyo/Efik wato mahaifinsa da mahaifiyar sa, Admiral Wey yayi karatunsa na farko a Calabar, Cross River State makarantar firamare na Methodist, Ikot Ekpene a Jihar Akwa Ibom ayanzu; sannan yacigaba da karatunsa a Jihar Lagos. Yafara aikin sa na farko a Marine Department amatsayin cadet kuma mai koyon zama injiya a 1940. A karshen koyon aikin sa a 1945, yayi aiki a dukkanin sea-going vessels dake a Marine Department. Lokacin da aka kirkiri Nigerian Navy a shekarar 1956, an maida shi bangaren Navy amatsayin sub-lieutenant. A 1962, an nada shi hafsa mai bada umurni na base da naval officer da rike da yankin Apapa, Lagos. A 1966, an nada shi Federal Commissioner na Establishment kuma yazama mamba a federal Executive Council. An masa Karin girma da dama inda yakai har zuwa matsayin vice-admiral.

Matsayoyin da ya rike a soja sune:

 • Marine engineer, 1950
 • Sub-lieutenant and engineer, 1956
 • Lieutenant, 1958
 • Lieutenant commander, 1960
 • Captain, 1963
 • Commodore, 1964
 • Rear-admiral, 1967
 • Vice-admiral, 1971

Yayi ritaya a 1975 bayan samun juyin mulki data kawo Murtala Mohammed a shugaban cin kasa [4], wacce ta mate gurbin mulkin gwamnatin janar Yakubu Gowon. Ya rasu a 12 December 1991.[1]

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

 1. 1.0 1.1 Cite news|last1=Aginam|first1=Arthur-Martins|title=For Whom The Bell Tolls - Nigeria's first naval chief dies at 73|publisher=African Concord|date=December 1991
 2. Cite web |url= http://www.gamji.com/article6000/NEWS7030.htm%7Ctitle=Aburi: The "Sovereign National Conference" That Got Away |accessdate=2007-06-16 |work= Gamji|last=Siollun|first=Max|publisher=
 3. Cite web |url= http://www.time.com/time/magazine/article/0,9171,904219,00.html%7Ctitle=An Attentive Listener|accessdate=2007-06-16 |date=1970-03-02 |work= Time|publisher=Time Warner
 4. 4.0 4.1 Cite web |url= http://www.nigeriavillagesquare1.com/Records/2004/08/murtala-muhammeds-first-address-to.html%7Clast=Mohammed%7Cfirst=Murtala |title=Murtala Muhammed's First Address to Nigeria |accessdate=2007-06-16 |work=Nigeriavillagesquare.com |publisher=Nigerian Village Square