Nadine Ibrahim
Nadine Ibrahim | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Nadine Ibrahim |
Haihuwa | Jahar Kaduna, 20 century |
ƙasa | Najeriya |
Ƴan uwa | |
Mahaifiya | Amina J. Mohammed |
Karatu | |
Makaranta | University of Gloucestershire (en) |
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | darakta |
Imani | |
Addini | Musulunci |
IMDb | nm7495420 |
Nadine Ibrahim (an haife ta a tsakanin shekarun 1993/1994 ) ita daraktar fim ce 'yar Nijeriya.[1][2]
Tarihin rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Ibrahim Nadine haifaffiyar garin kaduna ce kuma ta tashi acikin musulunci. Mahaifiyarta, Amina J. Mohammed tsohuwar ministar muhalli ce ta Najeriya.[2] Tun tana ƙarama, ta ke da sha'awar shirya labari da shirya fim maimakon sauran darussa na ilimin karatun boko.[3] Ta koma zuwa kasar Burtaniya daga Najeriya a lokacin tana da shekara 14[4] kuma ta yi karatun aikin jarida da harkar fim a Jami'ar Gloucestershire. Daga cikin ayyukan ta sun hada da, ta yi aiki akan ayyukan Majalisar Dinkin Duniya da kuma fina-finai na labaran gaskiya. Ibrahim Nadine itace mataimakiyar furodusa na Hakkunde, shiri game da wani dan Kudancin Najeriya wanda ya fuskanci al'adun Arewacin Najeriya a karonsa na farko.[5]
An fitar da gajeren fim dinta na Through Her Eyes a cikin shekara ta 2017. Shirin ya kunshi labari akan wata yarinya Azeeza, 'yar shekara 12 da aka sace kuma ta zama 'yar kunar bakin wake. Fim din ya kai matakin kusa da na karshe a gasan na bikin Los Angeles Cinema Festival kuma an zaɓe shi a cikin jerin gajerun fina-finai na African International Film Festival. Ta yi amfani da kafar yada labarai na EbonyLife Films and Televison" don yin fina-finai da suke bada labarin kabilun arewacin Najeriya, irin su Hausa, Fulani, Igbira, Igala, Tiv da Gbagyi. Ita ce shugabar wani kamfani yada labarai da ke Najeriya, Nailamedia, wanda aka kafa a shekarar 2017.[6] Wani gajeren fim dinta mai suna ' Marked', wanda ta yi aiki a kansa na tsawon shekaru biyu, wanda ya fara fitowa a bikin Aké a Legas a shekarar 2019. Shirin na magana ne akan zanukan/tsaga na gargajiya, wanda ake iya samu a jikkunan mutane daban daban na yankunan kasar Najeriya, amma kuma yakan zama haramun, amma duk da haka ita Nadine tayi shirin ne akan kyawun tsagan na gargajiya.[7]
Ibrahim Nadine ta lissafo Tyler Perry, Alfred Hitchcock, Spike Lee da Ang Lee a matsayin wadanda take koyi da su. Wani muhimmin tasirin da ta ambata shi ne mahaifiyarta, wanda a cikin aikinta na gwamnati ta koya game da talauci da rashawa a Najeriya. An sanya ta cikin manyan matasa yan fim na Najeriya abun kalla.[8] Ibrahim ta auri Nasir a Abuja a shekarar 2014.[9]
Wasu fina-finai
[gyara sashe | gyara masomin]- 2015: Idéar (gajeren fim)
- 2017: Hakkunde (gajeren fim)
- 2017: Through Her Eyes (gajeren fim)
- 2018: Tolu (gajeren fim)
- 2019: I am not corrupt (gajeren fim)
- 2019: Marked (gajeren fim)
- 2019: Words cut deep (gajeren fim)
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "The Future Awards Africa Prize for Screen Producer". The Future Awards Africa. 2 December 2018. Retrieved 11 October 2020.
- ↑ 2.0 2.1 "Okoro, Enuma (4 March 2017). "Nadine Ibrahim: I want to tell stories that can change the world". Guardian Woman. Guardian Newspapers. Retrieved 11 October 2020.
- ↑ "Samanga, Rumaro (22 October 2019). "In Conversation with Nigerian Filmmaker Nadine Ibrahim: 'The local stories matter the most.'". OkayAfrica. Retrieved 11 October 2020.
- ↑ "Lessons on Breaking into the movie industry- Nadine Ibrahim Films to the world". MRSCEONAIJA. 25 February 2018. Retrieved 11 October 2020.
- ↑ Okoro, Enuma (4 March 2017). "Nadine Ibrahim: I want to tell stories that can change the world". Guardian Woman. Guardian Newspapers. Archived from the original on 16 September 2021. Retrieved 11 October 2020.
- ↑ "Udodiong, Inemesit (16 August 2019). "Nigerian filmmaker Nadine Ibrahim talks about the essence of being different". Pulse. Retrieved 11 October 2020.
- ↑ "Cadogan, Dominic (24 October 2019). "Immerse yourself in the taboo art of scarification via short film Marked". Dazed. Retrieved 11 October 2020.
- ↑ "Three Young Nigerian Filmmakers to Watch". Shadow and Act. 8 May 2017. Retrieved 11 October 2020.
- ↑ "Nadine Ibrahim: The Beautiful Daughter Of Amina J. Muhammad". Opera News. Retrieved 11 October 2020.