Nazifi Asnanic
![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | jihar Kano, 8 ga Janairu, 1985 (38 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Hausa |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Hausa Larabci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a |
Jarumi, mawaƙi da producer (en) ![]() |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Nazifi Abdulsalam YusufNazifi Abdulsalam (Taimako·bayani) (An haife shi a ranar 2 ga watan Fabrairun shekara ta dubu daya da Dari Tara da tamanin da biyu 1982) wanda aka fi sani da suna Nazifi Asnanic[1] mawaƙi ne a Najeriya, marubucin waƙa, darakta, kuma furodusa.[2] An haifeshi a Garmin kano kuma ya girma a garin Kano . Nazifi Asnanic galibi ana kiran sa da sunan Nazifi Asnanic,[3] an san shi a matsayin ɗaya daga cikin hazikan mawakan Hausa a kowane lokaci a tarihin Kannywood.Ya sami lambobin yabo da gabatarwa ciki har da City People Entertainment Awards a matsayin fitaccen mawaƙi a shekara ta dubu biyu da sha hudu 2014.[4] Yana kuma daga cikin jaruman Kannywood da suka samu lambar yabo daga gwamnatin jihar Zamfara ta Nijeriya saboda gagarumin kokarinsu da gudummawar da suka bayar wajen hada kan al'adun Hausawa. Nazifi Asnanic ya fito, ya shirya, kuma ya bada umarni yawan lambobin fim a Kannywood.[5] [6].
Aiki[gyara sashe | gyara masomin]
Nazifi Abdulsalam Yusuf (Nazifi Asnanic) ya fara harkar waka ne a farkon shekara ta 2000. A shekara ta 2002, ya bar faifan sa na farko da wakoki 10 ciki har da Dawo Dawo . Ya dauki hankalin darakta, kuma Furodusa kamar Ali Nuhu da Aminu Saira inda ya yi waka don shirya FKD da Saira Fina-Finan a cikin Ga Duhu Ga Haske da Sai Wata Rana . Nazifi Asnanic ya sake fitar da faya-fayai 10, kuma ya sayar da kwayoyi miliyan a Najeriya da ma duniya baki daya wanda hakan ya sa ya zama daya daga cikin mafiya nasara a Kannywood. Ban da rera waka da kida, Nazifi ya shirya finafinai da yawa kamar Rai da Buri, Shu'uma, Ba'asi da sauransu.[7][8]
Wakoki[gyara sashe | gyara masomin]
- Labarina (2009)[9]
- Daga Ni Sai Ke (2010)
- Bunjuma (2011)
- Dan Marayan Zaki (2012)
- Dakin Amarya (2013)
- Rayuwa (2014)
- Kambu
- Ruwan Zuma '' (2013) ''
- Abu uku
Fina finai[gyara sashe | gyara masomin]
Fim | Shekara |
---|---|
Bilkisu Mai Gadon Zinari | ND |
Dare Da Yawa | ND |
Ga Fili Ga Mai Doki | ND |
Indai Rai | ND |
Kallo Daya | ND |
Makauniyar Yarinya | ND |
Miyatti. . . Miyatti | ND |
Almajira | 2008 |
Jamila Da Jamilu | 2009 |
Mata Da Miji | 2010 |
Ga Duhu Da Haske | 2010 |
Muradi | 2011 |
Rai Da Buri | 2011 |
Toron Giwa | 2011 |
Dan Marayan Zaki | 2012 |
Dare Daya | 2012 |
Gaba Da Gabanta | 2013 |
Lamiraj | 2013 |
Rayuwa Bayan Mutuwa | 2013 |
Shu'uma | 2013 |
Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]
- ↑ "Artist – Nazifi Asnanic || Kano, Nigeria". asnanic.com. Asnanic. Retrieved 26 May 2019.
- ↑ "Nazifi Asnanic [HausaFilms.TV – Kannywood, Fina-finai, Hausa Movies, TV and Celebrities]". hausafilms.tv. Retrieved 26 May 2019.
- ↑ "Kannywood: Taƙaitaccen Tarihin Mawaki Mai Muryar Zinare Wato Nazifi Asnanic". NaijaDrop.Com. 15 July 2017. Retrieved 26 May 2019.
- ↑ Lere, Muhammad (1 January 2015). "Kannywood's finest, worst moments of 2014". Premium Times Nigeria. Premium Time. Retrieved 26 May 2019.
- ↑ Ngbokai, Richard P. (12 July 2017). "Zamfara govt. honours Kannywood stars". Daily Trust. Archived from the original on 26 May 2019. Retrieved 26 May 2019.
- ↑ Wasu Kadan Daga Cikin Wakokin Nazifi Asnanic
- ↑ "NAZIFI ASNANIC YA SAKI SABUWAR WAKA MAI ZAFI AKAN RIKICIN AREWACIN NIGERIA – DOWNLOAD MUSIC HERE". Muryarhausa. Retrieved 26 May 2019.
- ↑ "Nazifi Asnanic Zai Fito Da Shu'uma". VOA. Retrieved 26 May 2019.
- ↑ "Nazifi Asnanic – Boomplay music". theboomplayer.com. Boomplayer. Retrieved 26 May 2019.[permanent dead link]