Salvador Dalí
Salvador Domingo Felipe Jacinto Dalí i Domènech, Marquess din Dalí na Púbol (11 May 1904 – 23 Junairun 1989), wanda akafi sanii da Salvador Dalí, Mai zane ne dan kasar Sipnaiya wanda yayi fice da baiwarsa na zane, kwarewa a zana mutane, da zanukansa na musamman masu ban al'ajabi.
An haife shi a Figueres, Katalunya, Hispania a shekara ta 1904, ya mutu a Figueras a shekara ta 1989. Dani ya samu iliminsa na zane a Madrid. A dalilin horn da ya samu daga malaman Impressionist da Renaissance tun yana karami, ya zamo mabiyin tafarkin zane na cubism da kuma avant-garde.[1]
Ya samu kusanci da kungiyar Surrealism a shekarun 1920s sannan ya koma kungiyar a shekarar 1929, nan da nan ya zamo daya daga cikin muhimman jagororin kungiyar. Aikinsa da yafi kowanne shahara The Persistence of Memory, ya kammala shi ne a watan Agustan 1931. Kuma yana daya daga cikin ayyukan Surrealist mafi shahara. Dali ya kwashe daukakin rayuwarsa a lokacin Yakin Basasar Hispaniya (1936 to 1939), kafin ya koma Amurka a 1940, inda ya samu nasarori da dama na kasuwanci. Ya dawo kasar Sipaniya a shekarar 1948 inda ya sanar da dawowarsa zuwa addinin Katolika inda ya fara habaka salonsa na “nuclear mysticism".[2]
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Kuruciya
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Salvador Dali a ranar 11 ga watan Mayun 1904, da misalin karfe 8:45 na safe, a hawa na farko na ginin Carrer Monturiol a birnin Figueres, na yankin Empordà, kusa da iyakar Faransa dake Kataloniya, kasar Sipaniya.[3] Babban wan Dali mai suna Salvador (wanda aka haifa a ranar 12 ga watan Oktoban 1901) ya rasu a sanadiyyar cutar gastroenteritis watanni tara kafin haihuwar Dali, a ranar 1 ga watan Augustan 1903. Mahaifinsa, Salvador Luca Rafael Aniceto Dalí Cusí (1872–1950), lauya ne kuma magatakarda mai matsakaicin karfi,[4] tsatsauran mabiyin addinin gargajiya dan Katalan, wanda matarsa,[5] Felipa Domènech Ferrés (1874–1921) ta saba duk wani ka'idojinsa,[6] inda ta karfafawa danta gwiwa da ya cigaba da bibiyar sana'ar zane. A lokacin rani na shekara ta 1912, iyalin sun koma bene na sama acikin ginin Carrer Monturiol 24 (hawa na 10 a yanzu)[7][8]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Gibson, Ian, The Shameful Life of Salvador Dalí, London, Faber and Faber, 1997, Chs 2, 3
- ↑ Gibson, Ian, The Shameful Life of Salvador Dali(1997)
- ↑ "Dalí recupera su casa natal, que será un museo en 2010". El País. 14 February 2008. Archived from the original on 2 July 2017. Retrieved 26 June 2017.
- ↑ Llongueras, Lluís. (2004) Dalí, Ediciones B – Mexico. ISBN 84-666-1343-9.
- ↑ Gibson, Ian (1997) pp. 16, 82, 634, 644
- ↑ Rojas, Carlos. Salvador Dalí, Or the Art of Spitting on Your Mother's Portrait Archived 19 April 2016 at the Wayback Machine, Penn State Press (1993). ISBN 0-271-00842-3.
- ↑ Gibson, Ian (1997)
- ↑ Dalí, The Secret Life of Salvador Dalí, 1948, London: Vision Press, p. 33