Jump to content

Salvador Dalí

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Salvador Dalí
Murya
Rayuwa
Cikakken suna Salvador Domingo Felipe Jacinto Dalí i Domènech da Salvador Felipe Jacinto Dalí i Domènech
Haihuwa Figueres, 11 Mayu 1904
ƙasa Ispaniya
Mazauni Figueres
New York
Harshen uwa Catalan (en) Fassara
Mutuwa Figueres, 23 ga Janairu, 1989
Makwanci Dalí Theatre and Museum (en) Fassara
Yanayin mutuwa Sababi na ainihi (cardiac arrest (en) Fassara)
Ƴan uwa
Mahaifi Salvador Dalí i Cusí
Mahaifiya Felipa Domènech i Ferrés
Abokiyar zama Gala Dalí (en) Fassara  (8 ga Augusta, 1958 -  10 ga Yuni, 1982)
Ahali Anna Maria Dalí (en) Fassara
Karatu
Makaranta Royal Academy of Fine Arts of San Fernando (en) Fassara
(1922 - 1926)
Harsuna Turanci
Yaren Sifen
Faransanci
Catalan (en) Fassara
Ɗalibai
Sana'a
Sana'a painter (en) Fassara, Mai sassakawa, marubuci, Jarumi, darakta, marubin wasannin kwaykwayo, mai daukar hoto, ɗan wasan kwaikwayo, mai tsara bangarorin fim, illustrator (en) Fassara, jewelry designer (en) Fassara, mai zane-zanen hoto da holographer (en) Fassara
Wurin aiki Madrid, Faris, Mauritshuis (en) Fassara, Prinsenhof (en) Fassara, Faransa, Tarayyar Amurka, Ispaniya, Tel Abib, Singapore, Manhattan (en) Fassara, Delft (en) Fassara da The Hague (en) Fassara
Muhimman ayyuka The Persistence of Memory (en) Fassara
Christ of Saint John of the Cross (en) Fassara
The Sacrament of the Last Supper (en) Fassara
The Great Masturbator (en) Fassara
Soft Construction with Boiled Beans (en) Fassara
The Face of War (en) Fassara
Kyaututtuka
Wanda ya ja hankalinsa Friedrich Nietzsche, Pablo Picasso da Hieronymus Bosch (en) Fassara
Mamba Académie des beaux-arts (en) Fassara
Royal Academy of Science, Letters and Fine Arts of Belgium (en) Fassara
Fafutuka surrealism (en) Fassara
Sunan mahaifi Dali, Salvador da Dalí Domènech, Salvador
Artistic movement still life (en) Fassara
genre painting (en) Fassara
Hoto (Portrait)
landscape painting (en) Fassara
allegory (en) Fassara
religious art (en) Fassara
IMDb nm0198557
salvador-dali.org

alvador Domingo Felipe Jacinto Dalí i Domènech, Marquess din Dalí na Púbol (11 May 1904 – 23 Junairun 1989), wanda akafi sanii da Salvador Dalí, Mai zane ne dan kasar Sipnaiya wanda yayi fice da baiwarsa na zane, kwarewa a zana mutane, da zanukansa na musamman masu ban al'ajabi.

An haife shi a Figueres, Katalunya, Hispania a shekara ta 1904, ya mutu a Figueras a shekara ta 1989. Dani ya samu iliminsa na zane a Madrid. A dalilin horn da ya samu daga malaman Impressionist da Renaissance tun yana karami, ya zamo mabiyin tafarkin zane na cubism da kuma avant-garde.[1]

Ya samu kusanci da kungiyar Surrealism a shekarun 1920s sannan ya koma kungiyar a shekarar 1929, nan da nan ya zamo daya daga cikin muhimman jagororin kungiyar. Aikinsa da yafi kowanne shahara The Persistence of Memory, ya kammala shi ne a watan Agustan 1931. Kuma yana daya daga cikin ayyukan Surrealist mafi shahara. Dali ya kwashe daukakin rayuwarsa a lokacin Yakin Basasar Hispaniya (1936 to 1939), kafin ya koma Amurka a 1940, inda ya samu nasarori da dama na kasuwanci. Ya dawo kasar Sipaniya a shekarar 1948 inda ya sanar da dawowarsa zuwa addinin Katolika inda ya fara habaka salonsa na “nuclear mysticism".[2]

Tarihin Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Kuruciya[gyara sashe | gyara masomin]

Salvador Dalí
Salvador Dalí

An haifi Salvador Dali a ranar 11 ga watan Mayun 1904, da misalin karfe 8:45 na safe, a hawa na farko na ginin Carrer Monturiol a birnin Figueres, na yankin Empordà, kusa da iyakar Faransa dake Kataloniya, kasar Sipaniya.[3] Babban wan Dali mai suna Salvador (wanda aka haifa a ranar 12 ga watan Oktoban 1901) ya rasu a sanadiyyar cutar gastroenteritis watanni tara kafin haihuwar Dali, a ranar 1 ga watan Augustan 1903. Mahaifinsa, Salvador Luca Rafael Aniceto Dalí Cusí (1872–1950), lauya ne kuma magatakarda mai matsakaicin karfi,[4] tsatsauran mabiyin addinin gargajiya dan Katalan, wanda matarsa,[5] Felipa Domènech Ferrés (1874–1921) ta saba duk wani ka'idojinsa,[6] inda ta karfafawa danta gwiwa da ya cigaba da bibiyar sana'ar zane. A lokacin rani na shekara ta 1912, iyalin sun koma bene na sama acikin ginin Carrer Monturiol 24 (hawa na 10 a yanzu)[7][8]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Gibson, Ian, The Shameful Life of Salvador Dalí, London, Faber and Faber, 1997, Chs 2, 3
  2. Gibson, Ian, The Shameful Life of Salvador Dali(1997)
  3. "Dalí recupera su casa natal, que será un museo en 2010". El País. 14 February 2008. Archived from the original on 2 July 2017. Retrieved 26 June 2017.
  4. Llongueras, Lluís. (2004) Dalí, Ediciones B – Mexico. ISBN 84-666-1343-9.
  5. Gibson, Ian (1997) pp. 16, 82, 634, 644
  6. Rojas, Carlos. Salvador Dalí, Or the Art of Spitting on Your Mother's Portrait Archived 19 April 2016 at the Wayback Machine, Penn State Press (1993). ISBN 0-271-00842-3.
  7. Gibson, Ian (1997)
  8. Dalí, The Secret Life of Salvador Dalí, 1948, London: Vision Press, p. 33
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.