Al'adun Arewacin Najeriya
Al'adun Arewacin Najeriya | ||||
---|---|---|---|---|
culture of an area (en) | ||||
Bayanai | ||||
Ƙaramin ɓangare na | Al'adun Najeriya na gargajiya | |||
Facet of (en) | Arewacin Najeriya | |||
Ƙasa | Najeriya | |||
Wuri | ||||
|
Al’adun Arewacin Najeriya, galibi sun mamaye al’adun masarautu goma sha hudu da suka mamaye yankin a zamanin kafin tarihi, amma kuma waɗannan al’adu suna da tasiri matuƙa a kan al’adun ƙabilu sama da ɗari da ke zaune a mabanbanta yankin.
Adabi
[gyara sashe | gyara masomin]Arewacin Najeriya ya gaji da yawa daga cikin abubuwan adabi na tsohuwar jihohin Sudan. Sarakunan Hausawa daga ƙarni na 9 zuwa na 18 sun samar da ayyukan adabi da dama.[1] Dubban irin waɗannan ayyuka galibi a cikin harsunan Ajami, Hausa da Larabci har yanzu ba a lissafta su a duk Arewacin Najeriya.[2] Tun lokacin da daular Birtaniyya ta yi wa mulkin mallaka, Ingilishi da rubutun Latin sun maye gurbin rubutun Ajami. Ana kallon Abubakr Imam Kagara a matsayin ɗaya daga cikin uban adabin Arewacin Najeriya na zamani,[1] Ayyukansa irin su Ruwan Bagaja da Magana Jari Ce, wanda aka buga a shekarun 1930, sun kasance wata gada tsakanin tsohuwar al'adar adabin Sudan da hanyoyin yamma.
Sauran irin su Yabo Lari da Muhammed Sule – marubucin The Undesirable Element – sun ba da gudummawa daidai gwargwado a cikin shekarun 1960. A shekarun 1980 fitattun marubutan da suka haɗa da Abubakar Gimba da Zaynab Alkali sun yi aiki don raya al’adun adabin Arewa da kuma bambanta da kudancin Najeriya.[1] A shekarun 1990 ne aka samu fitowar marubuta daga Abubakar Othman, Ismail Bala da Ahmed Maiwada a cikin waƙoƙi ga Maria Ajima da Victor Dugga a wasan kwaikwayo. Adabin Arewacin Najeriya na zamani ana yin su ne a Kano, Kaduna, Jos da Minna. Marubuta irin su BM Dzukogi, Ismail Bala, Yusuf Adamu, Musa Okapnachi, Razinat Mohammed da E.E. Sule suna nan suna aiki.[1]
Kiɗa
[gyara sashe | gyara masomin]Yayin da tsohuwar al’adar Sudan ta fi mayar da hankali kan waƙa ko waƙe-waƙe, tun daga shekarun 1950 shigowar tasirin Birtaniya ya yi haɓɓaka kiɗan Arewacin Najeriya.[3] Dan Maraya Jos, Mamman Shata, Barmani Choge, Aliyu Dan Kwairo da wasu da dama ana ɗaukar su a matsayin waɗanda suka kafa irin salon waka na musamman a Arewacin Najeriya.[3] Wasu irin su Fatima Uji sun ci gaba da shahara. Tun a shekarun 1990 tasirin al'adun salon wakar pop ya haifar da ƙaruwar mawakan R&B na Arewacin Najeriya. Mawaƙan Arewacin Najeriya da suka haɗa da Adam Zango, Ice Prince Zamani, Idris Abdulkareem da Sarki Bawa sun shahara a duk faɗin Afirka.
Cinema
[gyara sashe | gyara masomin]Masana'antar fina-finai ta Arewacin Najeriya, wacce aka fi sani da Cinema ta Hausa, ta kasance ɗaya daga cikin masana'antar fina-finai ta farko ta kasuwanci a yankin kudu da hamadar Sahara. Manyan ‘yan jarida da ‘yan wasan kwaikwayo daga Rediyo Kaduna da RTV Kaduna ne suka ƙirƙiro masana’antar a shekarun 1950. A yau jarumai irin su Ali Nuhu, Adam A Zango, Sani Danja, da Ibrahim Maishukku sun shahara a yankin. Tun daga shekarun 1990 da kuma tafiyar hawainiya na dalilin ra'ayin addinin Musulunci ta hanyar yaƙin neman zaɓe na kungiyar Izala, fina-finan Arewacin Najeriya ya gamu da koma baya sosai, kuma yanzu takwarorinsu na Kudancin Najeriya sun musu nisan kiwo.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 Ali, Richard Ugbede. "On Northern Nigerian Literature And Related Issues". Archived from the original on 2015-01-02. Retrieved 2014-11-11.
- ↑ Auyo, Musa; Mohammed, Ahmed (2009). "The Prevalence of Arabic and Ajami Manuscripts in Northern Nigeria, Implications for Access, Use, and Enduring Management: A Framework For Research". National Conference on Exploring Nigeria's Arabic/Ajami Manuscript Resources for Development of New Knowledge.
- ↑ 3.0 3.1 Adah, Abah; Chiama, Paul. "Northern Nigeria's Music Legends". leadership.ng. Retrieved 2014-11-11.