Dangote Group

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Template:Infobox company


Rukunin kamfanoni na Dangote ko Dangote Group kamfanine na hadaka a Najeriya mallakin Alhaji Aliko Dangote. Shine babban kamfani a Afrika ta yamma kuma daya daga cikin manya a nahiya Afrika. Kamfanin ya samawa mutane sama da 300,000 aikin yi.

An samar da kamfanin ne a 1981 da farko domin kasuwanci inda ya fara da shigo da sikari da siminti da shinkafa da kifi da sauran kayayyakin masarufi na bukatun yau da kullum don rarabawa a kasuwannin Najeriya. Kamfanin ya cigaba zama babbban kamfanin dake sarrafawa tare da samar da kayayyaki a shekarun 1991, ya fara da sakar tufafi, sai kuma sarrafa fulawa sai sarrafa gishiri sai sarrafa sikiri. Daganan kamfanin ya bunkasa zuwa samar da kamfanin sarrafa siminti. Kamfanin ya bunkasa zuwa sauran sassa na nahiyar Afrika.

A yanzu rukunin yana tafiyar da kamfanoni sama da 18 a kasahen Afrika guda goma. Babbar cibiyar rukunun kamfanonin Dangote tana Legas a Najeriya.

Tarihin kamfanin[gyara sashe | Gyara masomin]

Aliko dangote ne ya kafa kamfanin bayan samun rance na dalar Amurika $3,000 daga hannun kawun sa. Ya fara ne da sayar da kayan abinci daga bisani kuma yacigaba zuwa shigo da kayayyaki ta jirgin ruwa kamar siminti.

A yau kamfanin ya bunkasa sosai a Nahiyar Afrika. Kamfanin na samarwa tare da kasuwancin Shinkafa, Sikari, Fulawa, taliya, kayan ruwa, man fetur da iskar gas, samar da rukunun gidaje, harkar sadarwa, takin zamani da tama da karafa.

Rarrabuwar Kamfani[gyara sashe | Gyara masomin]

Kamfanin wanda ya shahara a huldar kasuwar duniya ta Stock Exchange ya rarabu zuwa kasashen Benin, [[Kamaru, Ghana, Najeriya, Afrika ta kudu da Zambiya

Kamfanin sikari na Dangote shine babban kamfanin sikari a yankin Afrika makusantan Sahara.