Juyin Mulki a Najeriya, 1966
Iri |
coup d'état (en) Counter-coup (en) |
---|---|
Kwanan watan | 28 ga Yuli, 1966 |
Ƙasa | Najeriya |
Adadin waɗanda suka rasu | 300 |
Juyin mulkin Najeriya na 1966, ko kuma abin da ake kira "July Rematch", shi ne juyin mulki karo na biyu na juyin mulkin da sojoji suka yi a Najeriya. Laftanar Kanar Murtala Muhammed[1] da wasu da yawa daga cikin hafsoshin sojan Arewa ne suka shirya shi. Juyin mulkin ya fara ne da misalin tsakar dare a ranar 28 ga watan Yuli, 1966[2] kuma wani martani ne ga kashe-kashen da wasu sojoji suka yi wa ƴan siyasa da Jami'an Arewa a ranar 15 ga wtan Janairun shekara ta alif1966 (duba Juyin mulki a Najeriya, (15 ga watan Janairu 1966)). Juyin mulkin da aka yi a watan Yuli ya yi sanadin kashe shugaban mulkin soja na farko a Najeriya, Janar Johnson Aguiyi-Ironsi da Laftanar Kanar Adekunle Fajuyi (wanda ke karɓar baƙuncin Aguiyi-Ironsi) a Ibadan da wasu ɓangarorin Arewa da ba sa so.[3] Bayan kawo ƙarshen gwamnatin shugaba Ironsi ne aka naɗa Laftanar Kanar Yakubu Gowon a matsayin shugaban ƙasa a watan Yuli na shekarar 1966.
Dalilan da suka sa aka yi juyin mulki
[gyara sashe | gyara masomin]A cewar masanin tarihi Max Siollun sojojin arewa suna da jerin ƙorafe-ƙorafe[4] biyo bayan wata dakatarwa a ranar 15 ga watan Janairun 1966, juyin mulkin da ya kai ga shirya wani juyin mulkin. Jerin korafe-korafensu sune:
- Kisan shugabannin farar hula na arewa da hafsoshin soji a ranar 15 ga Janairun 1966, juyin mulki.
- Ranar 15 ga Janairun 1966, masu yunƙurin juyin mulki (mafi yawa manyan jami'an soji) ba a yi musu shari'ar cin amanar ƙasa ba, haka-zalika, ana biya su-(albashi) yayin da suke tsare.
- Ƙaddamar da Dokar Haɗin Kai.
- Jita-jitar "Juyin Mulkin Ibo" don kawar da sojojin Arewa.
- Kara girma da wasu Manyan Ibo suka yiwa Laftanar Kanal .
- Jita-jita cewa Janar Aguiyi-Ironsi ya nuna fifiko ga ƙabilar Igbo.
- Ana shirin yin musanya da bataliya ta 1 da ta 4 da kuma shirin karban gwamnonin sojoji na yankuna daban-daban.
Mahalarta juyin mulkin
[gyara sashe | gyara masomin]Ga jera sunayen manyan waɗanda suka yi yunƙurin juyin mulkin a ƙasar, kamar haka:[5]
- Laftanar Kanar Joseph Akahan (Kwamandan Bataliya ta 4 Kaduna)
- Laftanar Kanar Murtala Muhammed (Inspector of Signals, Lagos)
- Major Theophilus Danjuma (Principal Staff Officer, Army HQ, Lagos)
- Major Abba Kyari (Artillery, Kaduna)
- Manjo Martin Adamu (Bataliya ta biyu Legas)
- Manjo Shittu Alao (HQ, Legas)
- Manjo Musa Usman (Rundunar Sojojin Najeriya, Legas)
- Captain Joseph Garba (Federal Guards Lagos)
- Captain Isa Bukar (Federal Guards Lagos)
- Captain Ibrahim Taiwo (Lagos Garrison Yaba)
- Captain Baba Usman GSO (Grade II, Army HQ, Lagos)
- Captain Abdul DS Wya (Bataliya ta uku, Kaduna)
- Laftanar Muhammadu Buhari (2 Brigade Lagos)
- Laftanar Ibrahim Babangida (1st Reconnaissance Squadron, Kaduna)
- Laftanar Ibrahim Bako (Bataliya ta hudu, Ibadan)
- Laftanar William Walbe (Bataliya ta biyu, Legas)
- Laftanar Mamman Vatsa (Bataliya ta hudu, Ibadan)
- Laftanar Buka Suka Dimka (Nigerian Military Training College Kaduna)
- Laftanar Yakubu Dambo (Bataliya ta uku Kaduna)
- Laftanar Garba A. Dada (Adjutant 4th Battalion Ibadan)
- Laftanar Garba Duba (1 Reconnaissance Squadron Kaduna)
- Laftanar Mohammed Balarabe Haladu (Bataliya ta hudu, Ibadan)
- Laftanar Malami Mahe Nassarawa (2nd Battalion, Lagos)
- Laftanar James Onoja (Bataliya ta hudu, Ibadan)
- Laftanar Abdullahi Shelleng (Kwamandan Kamfanin, Bataliya ta 4, Ibadan)
- Laftanar Paul Chabri Tarfa (Federal Guards, Lagos)
- Laftanar DS Abubakar (Abeokuta Garrison)
- Laftanar Na Biyu Sani Abacha (Bataliya ta Uku Kaduna)
- Laftanar Muhammadu Gado Nasko (Artillery, Kaduna)
- Sajan Paul Dickson
- Sabo Kwale (Abeokuta Garrison)
- Kofur John Shagaya (2nd Reconnaissance Squadron, Abeokuta)
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- 1966 anti-Igbo pogrom
- Tarihin Sojan Najeriya
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Siollun, Max (2009). Oil, Politics and Violence: Nigeria's Military Coup Culture (1966-1976). Algora. pp. 98–102. ISBN 9780875867090.
- ↑ Joe Garba- A Revolution in Nigeria, another view
- ↑ Siollun, Max (2009). Oil, Politics and Violence: Nigeria's Military Coup Culture (1966-1976). Algora. p. 110. ISBN 9780875867090.
- ↑ Siollun, Max (2009). Oil, Politics and Violence: Nigeria's Military Coup Culture (1966 - 1976). Algora. p. 97. ISBN 9780875867090.
- ↑ Siollun, Max (2009). Oil, Politics and Violence: Nigeria's Military Coup Culture (1966 - 1976). Algora. pp. 245–248. ISBN 9780875867090.