Jump to content

Kofa:Kimiyya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kofa:Kimiyya
Wikimedia portal (en) Fassara
Dr. Wendy Bohon a cikin ɗakin gwajin kimiyya
Ma auni
ma auni ne na ilimin kimiyya
Masana kimiyya suke kir kira sababbin abubuwa

Kimiyya na nufin ilimin zahiri da ake iya ganin sa, ko taɓa shi, ko ɗanɗanonshi, da kimiyya ne ake samar da Fasaha. [1]kimiyya dabaru ne a fannin ilimin lissafi, ilimin ƙwayar halitta da ilimin na'ura wajen samar da rayuwa mai sauƙi a fannin Sifiri, Lafiya, Makamai, Noma, Lantarki, Na'ura da Gini. Kimiyya ce take samar da Fasaha a ƙwa-ƙwalwan Mutane har su ƙirƙiri sa babbin abubuwa. Duk ci gaban da aka samu a Duniya to a dalilin Kimiyya ne, kuma kimiyya ce ta ke dunƙule ilimi dayawa waje guda kuma ta raba su a matsayin ilimi mai zaman kanshi.[2] Asalin ilimin Kimiyya ya samo asali ne a ƙasar Misra wato Egypt da kuma Mesopotamia a shekaru 3500, zuwa shekara ta 3000, BCE kafin zuwan Annabi Isah. Sun bayar da gudummawa a fannoni daban-daban kamar su ilimin Lissafi, Ilimin Taurari da Ilimin Magunguna. wannan kimiyyar ya shiga har izuwa girka wato (Greek) da daular Rumawa, ya wayar musu da kai. Ilimin Kimiyya na girkawa ya ƙarfafa ma 'yan gabashin Turai kuma ya wayar musu da ido a shekara ta (400 zuwa 1000 CE) amman a lokacin ba ai amfani da shi a Duniyar Musulmi ba, sai daga baya a lokacin Islamic Golden Age. A lokacin ne Musulmai sukayi bincike a gabashin nahiyar Turai daga ƙarni na 10th zuwa ƙarni na 13th. Kimiyya ta ratsa ko inane a Ƙarni na 19, wanda a lokacin ne aka samar da gwanaye a fannin Kimiyya har suka canza mata suna daga "natural philosophy" zuwa "natural science."[3]

Fannonin kimiyya.

[gyara sashe | gyara masomin]

Kimiyya ta zamani ta kasu zuwa kaso uku ne, sune kamar haka:-

A daa can ana samun ilimin kimiyya ne a gun sanannun masu ilimi da kuma bincike dan ƙirƙirar sabuwar Kimiyya ko gano ta. Amman a wannan zamanin ana samun ilimin Kimiyya ne kaɗai a Jami’o’i da ƙananan cibiyoyin Ilimi kuma ana sayar da kimiyyar ne zuwa ga kamfanoni da masana’anta domin ci gaba da samun arziƙi.

Koyon Wikipedia
Ajin karatu | Manufofin Wikipedia | Saka Fayal | Editin | Editocin Hausa Wikipedia | Tambaya | Bidiyon koyo
  1. https://www.britannica.com/science/science
  2. https://www.dictionary.com/browse/science
  3. https://hausa.legit.ng/1086886-kimiya-ta-bayyana-hanyoyin-3-da-iya-kawo-karshen-duniya.html