Jump to content

Hafsat Idris

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Hafsat Idris
Rayuwa
Haihuwa Sagamu, 14 ga Yuli, 1989 (35 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a jarumi
Imani
Addini Musulunci

Hafsat Ahmad Idris ( An haife ta ne a ranar 14 ga watan yuli a shekara ta alif ɗari tara da tamanin da bakwai miladiyya 1987) wacce aka fi sani da Hafsat Idris ko Ku ma hafsat barauniya,[1][2] yar wasan kwaikwayo ce a Najeriya a masana'antar shirya fina finai [[Kannywood|fina].[3][4]Kuma maɗaukakiya a wasan ɓangaren ta na masana'antar ta kannywood dake kasar Najeriya anfi sanin ta da Hafsat Barauniya, sakamakon fitowa da tayi a cikin wani fim mai suna Barauniya.

Farkon rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Hafsat ita yar asalin jihar Kano ce, arewacin Najeriya . Amma an haife tane kuma ta girma a Shagamu, jihar Ogun, ma’ana kudu maso yammacin Najeriya .[5][6] An san Hafsat Idris a karon farko da kuma rawar da ta taka a fim ɗin Barauniya, wanda ya nuna canji a cikin aikinta. An zaɓe ta a matsayin jarumar Kannywood da ta fi fice a shekarar 2017 ta City People Movie Awards, ta kasance ɗaya daga cikin sanannun mata a kannywood.[7][8][9]

Hafsat Ahmad Idris ta fara fim ne a shekara ta 2016 a cikin fim mai suna Barauniya, tare da Ali Nuhu. Ta shiga masana'antar kannywood bayan da ta gwada hannun ta a harkar kasuwanci, ta yi tafiye-tafiye mafi yawan lokuta daga Oshogbo zuwa Kano saboda kasuwanci. Duk da haka, duk da yin kyakkyawan aiki a kasuwancin, sha'awar Hafsat ta karkata zuwa zama 'yar wasan kwaikwayo. Hafsat ta mallaki wani film da ta samarwa kamfanin da aka fi sani da Ramlat Investment, ta samu lambobin yabo na fina-finai a shekarar 2019, ciki har da blockbuster movie wanda ake akira Kawaye a cikin abin da gabatar da taurari, kamar Ali Nuhu, Sani Musa Danja da kuma kanta.[10]

Kyaututtuka

[gyara sashe | gyara masomin]
Shekara Kyauta Nau'i Sakamakon
2017 Kyaututtukan Nishadar City Mafi yawan 'yan wasan kwaikwayo Ayyanawa
2018 Kyaututtukan Nishaɗar City Mafi shahararren dan wasan kwaikwayo Lashewa
2019 Kyaututtukan Nishaɗar City Mafi kyawun actress Lashewa
2019 Kyaututtukan Nishaɗar City Fuskar Kannywood Lashewa

Hafsat tana cikin fina-finai da dama, ciki harda masu zuwa:

Take Shekara
Biki Buduri ba'a tantance lokacin ba.
Furuci ba'a tantance lokacin ba.
Labarina ba'a tantance lokacin ba.
Barauniya 2015
Makaryaci 2015
Abdallah 2016
Ta Faru Ta Kare 2016
Rumana 2016
Da Ban Ganshi Ba 2016
Dan Almajiri 2016
Haske Biyu 2016
Maimunatu 2016
Mace Mai Hannun Maza 2016
Wazir 2016
Gimbiya Sailuba 2016
Matar Mamman 2016
Risala 2016
Igiyar Zato 2016
Wata Ruga 2017
Rariya 2017
Wacece Sarauniya 2017
Zan Rayu Da Ke 2017
Namijin Kishi 2017
Rigar Aro 2017
Yar Fim 2017
Dan Kurma 2017
Kawayen Amarya 2017
Dr Surayya 2018
Alqibila 2018
Ana Dara Ga Dare Yayi 2018
Mata Da Miji 2019

.

  1. "Hafsa Idris [HausaFilms.TV - Kannywood, Fina-finai, Hausa Movies, TV and Celebrities]". hausafilms.tv. Retrieved 22 May 2019.
  2. Lere, Muhammad (17 December 2016). "Getting married is my priority – Kannywood actress, Hafsat Idris - Premium Times Nigeria". Premium Times. Retrieved 22 May 2019.
  3. Samfuri:Cite. web
  4. "Kannywood Winners Emerge @ 2019 City People Movie Awards". City People Magazine. City People Magazine. 14 October 2019. Retrieved 15 July 2020.
  5. "Hafsa Idris Biography - Age". MyBioHub. 2 June 2017. Retrieved 15 July 2020.
  6. Adamu, Muhammed (30 January 2017). "Hafsat Ahmad Idris: Epitome of hardwork, resilient actress". Blueprint. Retrieved 22 May 2019.
  7. https://www.premiumtimesng.com/entertainment/kannywood/218267-getting-married-priority-kannywood-actress-hafsat-idris.html
  8. "Ba zan iya fitowa karuwa a fim ba - Inji Hafsat Barauniya". Gidan Technology Da Media (in Larabci). Archived from the original on 2020-11-16. Retrieved 2020-09-24.
  9. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-07-15. Retrieved 2021-02-28.
  10. Muhammed, Isiyaku (24 September 2019). "Hafsat Idris hits one million followers on Instagram". Daily Trust. Archived from the original on 15 October 2019. Retrieved 15 October 2019.