Isiaka Adetunji Adeleke

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Isiaka Adetunji Adeleke
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

Mayu 2015 - ga Afirilu, 2017
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

ga Yuni, 2007 - Mayu 2011 - Mudasiru Oyetunde Hussein (en) Fassara
District: Osun West
Gwamnan Jihar Osun

ga Janairu, 1992 - Nuwamba, 1993
Leo Segun Ajiborisha - Anthony Udofia (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Enugu, 15 ga Janairu, 1955
ƙasa Najeriya
Ƙabila Yarbawa
Harshen uwa Yarbanci
Mutuwa 23 ga Afirilu, 2017
Yanayin mutuwa Sababi na ainihi (Ciwon zuciya)
Ƴan uwa
Mahaifi Raji Ayoola Adeleke
Karatu
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
Alliance for Democracy (en) Fassara

Isiaka Adetunji Adeleke ( 15 Janairu 1955 - 23 Afrilu 2017) ɗan siyasan Najeriya ne, ya kasance Sanata sau biyu da ya wakilci Osun ta Yamma daga 2007 zuwa 2011 a ƙarƙashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma an sake zaɓen sa a ƙarƙashin tutar jam'iyyar All Progressives Congress a shekarar 2015.[1] Ya sake tsayawa takara a watan Afrilun 2011 a jam’iyyar PDP, inda ya zo na biyu da ƙuri’u 77,090 bayan wanda ya lashe zaɓen Mudasiru Oyetunde Hussein na jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) wanda ya samu kuri’u 121,971.[2]

Farkon rayuwa da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Isiaka Adetunji Adeleke a ranar 15 ga Janairun 1955 ga iyalan Sanata Ayoola Adeleke da Esther Adeleke.[3] An haife shi a jihar Enugu kuma ya yi shekarunsa na farko a birnin har zuwa lokacin da aka fara yakin basasar Najeriya. Ya fara karatun firamare ne a makarantar Christ Church, Enugu, kafin ya koma Ibadan.[3] Ya kammala karatunsa na sakandare a makarantar Grammar Ogbomoso. Adeleke yana da digiri na farko na Arts, da kuma digiri na biyu a fannin gudanar da jama'a. Ya kasance shugaban Majalisar Gudanarwa, Majalisar Inganta Fitar da kayayyaki ta Najeriya, Pro-chancellor kuma Shugaban Majalisar Gudanarwa, Jami'ar Calabar, Najeriya.[1][4] Shi ne kawun mawaƙin Najeriya, Davido.[5]

Fagen siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Jihar Osun, Najeriya

A jamhuriya ta uku ta Najeriya Adeleke ya tsaya takarar gwamnan sabuwar jihar Osun wacce aka sassaka daga jihar Oyo. Ya kasance ɗan jam'iyyar SDP mai rinjaye a jihar. Wanda ya zo na gaba shi ne lauya, Oladipo Oladosu amma bayan kammala zaɓen fidda gwani da Adeleke ya zo na biyu, Adeleke ya samu nasara a zagaye na biyu. [6] Daga nan aka zaɓe shi gwamnan farar hula na farko a jihar Osun a shekarar 1992. Sanannen abun da Adeleke ya ya yi shine kafa kwalejin kimiyya da fasaha a Iree, kwalejin fasaha da ke Esa-Oke da kuma kammala aikin yaɗa labarai na jihar Osun. Sai dai a shekarar 1994, bayan rugujewar jamhuriyar, Adeleke ya kafa tantinsa ga ƙungiyar ƴan adawa, Afenifere, amma daga baya ya koma jam'iyyar Democratic Party of Nigeria, sabuwar jam'iyyar siyasa da ke samun goyon bayan wasu makusantan Abacha. [7] A 2007, Adeleke ya zama Sanata mai wakiltar Osun ta Yamma. Babban abokin takararsa shi ne Mudasiru Oyetunde Hussein, wanda ya tsaya takarar Action Congress. Hussein ya shafe wa'adi biyu a majalisar wakilai (1999-2007) a matsayin ɗan jam'iyyar Alliance for Democracy a wata mazaɓar jihar Legas, amma ya samo asali daga jihar Osun. Hussein ya ɗaukaka ƙara a zaɓen, amman bai yi nasara ba.[8] An naɗa Isiaka Adetunji Adeleke a kwamitoci akan Albarkatun Man Fetur, Haɗin kai, Gidaje da Sojojin Sama.[1]

A cikin watan Maris 2008, ya kafa lambar yabo ta tallafin karatu ga ɗalibai marasa galihu kusan 100 a manyan makarantu a faɗin ƙasar.[9]

A watan Yulin 2009, a matsayin shugaban kwamitin majalisar dattijai kan INEC, Sanata Isiaka Adetunji Adeleke ya yaba da ayyukan hukumar zabe mai zaman kanta, yana mai cewa "zuwa yanzu INEC ta taka rawar gani".[10] Ya goyi bayan ƴancin ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje su kaɗa kuri’a a zaɓen Najeriya.[11] Adeleke, kafin rasuwarsa, ana zarginsa da sa ido a kan kujerar gwamna a Osun gabanin zaɓen shekarar 2018 a jihar.[12]

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Afrilun 2017, Adeleke ya kamu da ciwon zuciya. Ya rasu ne a ranar 23 ga watan Afrilu, 2017 a Asibitin Biket da ke Osogbo, babban birnin Jihar Osun.[13]

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 "Sen. Isiaka Adetunji Adeleke". National Assembly of Nigeria. Archived from the original on 23 November 2009. Retrieved 2009-09-20.
  2. "Official result of OSUN Senatorial Elections". The Punch. April 10, 2011. Archived from the original on April 13, 2011. Retrieved May 5, 2011.
  3. 3.0 3.1 Lawal, Olumide. "Isiaka Adeleke: 60 years of service to humanity". sunnewsonline. Archived from the original on 5 January 2016. Retrieved 27 December 2015.
  4. "Timi of Ede, Oba Oyewusi Agbonran II". The Nation. 2009-08-22. Archived from the original on 2011-07-26. Retrieved 2009-09-20.
  5. "Davido mourns late Uncle, Senator Isiaka Adeleke". The Vanguard. 24 April 2017.
  6. Agbroko, G. (1996, Nov 18). From the editor. Theweek
  7. Olaniyonu, Y. (1996, Nov 18). A victim or a villain? Theweek
  8. "AC Senatorial Candidate boasts: I'll flush Adeleke out of Senate". The Daily Sun. 28 August 2008. Retrieved 2009-09-20.[permanent dead link]
  9. "Adeleke Scholarship Award for Indigent Students". This Day. 4 March 2008. Retrieved 2009-09-20.
  10. "INEC has done creditably well, Senate Committee!". INEC. 2009-07-31. Retrieved 2009-09-20. [dead link]
  11. "Nigerians abroad submit bill on voting right to National Assembly". Guardian Newspapers. 4 August 2009. Retrieved 2009-09-20. [dead link]
  12. "Osun: APC dares Adeleke to openly declare governorship ambition". Naija News. 4 December 2016. Archived from the original on 24 April 2017. Retrieved 2016-04-23.
  13. Template:Cite work