Komadugu Yobe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Dauka yankin na kogin Yobe
Kogin Yobe a cikin shekarar 1900

Kogin Yobe, wanda kuma aka san shi da Komadougou Yobe ko Komadougou-Yobe a harshen Faransa, wani kogi ne a Yammacin Afirka wanda ke kwarara zuwa tafkin Chadi ta hanyar Najeriya da Nijar . Ma hadar wannan kogin ya hada da Kogin Hadejia, da Kogin Jama'are. [1] da Kogin Komadugu Gana . Kogin ya zama wani sashi na iyakar ƙasa tsakanin Nijar da Najeriya.[2]

Akwai damuwa game da sauye-sauye akan gudanar ruwan kogin, dangane da tattalin arziki da kuma tsabtace muhallin kogin, a halin yanzu shine Dam din Tiga a cikin jihar Kano, tare da shirin tattaunawa game da Dam din Kafin Zaki a cikin jihar Bauchi. [3]

Manyan biranen dake kusa da kogin sun hada da Gashua, Geidam, da Damasak a Najeriya, da Diffa a Nijar.

Dubi kuma[gyara sashe | Gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

Mahadan kasa: 12°39′06″N 10°38′50″E / 12.65167°N 10.64722°E / 12.65167; 10.64722