Nwando Achebe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Nwando Achebe
Rayuwa
Haihuwa Enugu, 7 ga Maris, 1970 (53 shekaru)
ƙasa Najeriya
Tarayyar Amurka
Harshen uwa Harshen Ibo
Karatu
Harsuna Turanci
Harshen Ibo
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a historian (en) Fassara da Malami
Employers Michigan State University (en) Fassara

Nwando Achebe malama ce 'yar asalin Nijeriya da America, mai goyon bayan 'yancin mata (feminism) kuma mai koyarwa, kuma wacce taci kyautuka da dama kan tarihi.[1] Ita ake yiwa lakabi da Jack and Margaret Sweet Endowed Professor of History,[2] kuma Mataimakiyar Dean na Bambanci, Daidaituwa, da Hadawa a Kwalejin Kimiyyar Zamani a Jami'ar Michigan State University.[3] Haka kuma ita ce ta kafa Babban Edita na Jaridar Tarihin Afirka ta Yamma.[4]

Asali[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Nwando Achebe ne a Jihar Enugu, da ke gabashin Najeriya[5] ga marubucin Nijeriya, marubucin insha'i, kuma mawaki, Chinua Achebe, da Christie Chinwe Achebe, farfesa a Fannin Ilimantarwa.[6] Ita matar Folu Ogundimu, farfesan aikin jarida ne a Jami'ar "Michigan State University", kuma uwa ga 'yar ta, Chino.[7] Babban wanta, Chidi Chike Achebe babban likita ne.

Ilimi da Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Achebe ta karɓi digirin ta na digirgir a fannin ilimin Tarihin Afirka daga Jami'ar California, Los Angeles a shekara ta 2000. Masaniyar tarihin baka ta hanyar horo, bangarorin da ta kwarewa sune Tarihin Yaammacin Afirka, mata, jinsi da tarihin jima'i. A shekarar 1996 da shekarar 1998, ta yi aiki a matsayin Gidauniyar Ford da kuma Fulbright-Hays scholar-in-Residence a Cibiyar Nazarin Afirka da Sashen Tarihi da Nazarin Duniya a Jami'ar Nijeriya, Nsukka. Matsayinta na farko a harkkar ilimantarwa ya kasance a matsayin ta na Mataimakiyar Farfesa na Tarihi a Kwalejin William da Mary. Daga nan ta koma Jami'ar Michigan State University a shekarar 2005 a matsayin Mataimakiyar Furofesa, daga bisani Farfesa a shekara ta 2010, kuma a yanzu ita ce "Jack da Margaret Sweet Professor".

Malanta[gyara sashe | gyara masomin]

Ta wallafa littattafai guda shida, na farkon su shi ne, Farmers, Traders, Warriors, and Kings: Female Power and Authority in Northern Igboland, s tsakanin 1900–1960, wanda Heinemann ya wallafa acikin shekara ta 2005. Wannan littafi na Achebe ya taka rawa matuka a wajen nuna bayani akan jinsi da tarihin mata a nahiyar Afurka, da kuma canjin tsarin mulki da addinai a lokacin turawan mulkin mallaka. Littafin ya bada kafar muhawara akan 'yancin mata watau "feminism', wanda Achebe ta yi wa lakabi da “ka'idojin halayyar mata” wanda a yanzu matan inyamurai basu rayuwa akan wannan tsarin. Gabaki daya littafin ya kunshi bayanai da suka shafe ra'ayin cewa mata suna dogara ne da maza ta hanyar tambayoyi da kafa hujjoji daga fuskar tarihi akan kwarjini da kuma kima da mata suke dashi a tarihin kasashen inyamurai.

Littafin ta na biyu shine, The Female King of Colonial Nigeria: Ahebi Ugbabe, wanda Indiana University Press suka wallafa a cikin shekara ta 2011. Cikakken tarihi ne game da mace daya tak da ta rike matsayi da sarauta a lokacin mulkin turawa a Afurka, littafin da ya lashe lambobin yabo guda uku, kyautar Aidoo-Snyder Book Prize, da kyautar The Barbara "Penny" Kanner Book Prize da kuma kyautar Gita Chaudhuri Book Prize.[8]Wani kafar binciken littattafai yayi nuni da cewa wannan ittafin a matsayin jayayya mai karfi akan nazarin karatun academiya na tarihin matan kasashen Inyamurai da Najeriya da kuma Afurka gaba daya. Littafin ya kunshi labarin Ahebi Ugbabe (c. 1885–1948), wacce a lokacinta ta nada kanta matsayin sarki kuma ya bada bayanai akan yadda tsarin mulki ya canza bayan mulkin turawan mulkin mallaka a fakaice. Har wayau binciken da littafin yayi ya nuna bambamci akan tsarin mulki na maza da kuma shuwagabancin maza kawai, zuwa mace mai matsayi, mace mai doka, mace mai sarauta, kuma mace miji. Har ila yau, wannan labari ya iyakance iyakokin matsayin jinsi. A takaice dai, wannan littafi na The Female King of Colonial Nigeria yana wayar da kan al'umma akan fahimtar su na gargajiya da kuma lokacin turawa akan tsarin mulki da siyasa a yankin ta.

Littafin da Achebe ta taimaka wajen rubutawa a cikin shekara ta 2018 mai suna History of West Africa E-Course Book (British Arts and Humanities Research Council, 2018), litttafin karatun aji wanda aka rubuta don dalibai masu fuskantar jarabawar karshe a matakin makarantun sakandare na Yammacin Afurka wato (WASSCE). Har ila yau ta tallafa wajen rubuta littafin A Companion to African History (Wiley Blackwell, 2019) ita da William Worger da kuma Charles Ambler sannan kuma sun rubuta littafin Holding the World Together: African Women in Changing Perspective (University of Wisconsin Press, 2019), ita da Claire Robertson. Ohio University Press suka wallafa littafin Achebe na shekara ta 2020 mai suna Female Monarchs and Merchants Queens in Africa.[9]Laura Seay daga gidan jarifdar The Washington Post, ta rubuta game da littafin Female Monarchs and Merchant Queens in Africa a matsayin "cikakken littafin wanda ya kunshi komai kuma mai saukin fahimta".

Tallafi da Kyaututtuka[gyara sashe | gyara masomin]

Nwando Achebe ta samu tallafi daga Gidauniyar Wenner Gren, Gidauniyar Rockefeller, Woodrow Wilson, Fulbright-Hays, Gidauniyar Ford, Hukumar Lafiya ta Duniya da kuma Hukumar bayar da tallafi ta Dan Adam. Ita ce kuma wacce ta samu lambar yabo ta littafi har sau uku.[10]

Littattafai[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Woodrow Wilson National Fellowship Foundation. "Seeing The Whole Dance: Nwando Achebe WS '00 Brings New Perspective to African Women's Power". Retrieved 11 May 2017.
  2. "Nwando Achebe, Department of History". Retrieved 13 May 2017.
  3. "Associate Dean of Diversity, Equity, and Inclusion". Retrieved 15 August 2020.
  4. http://woodrow.org/about/fellows/achebe-nwando/
  5. "Daily Trust Newspaper. "Nigeria: Nwando Achebe--The Woman and Her Works". All Africa. Retrieved 13 May 2017.
  6. "Offiong, Vanessa. "Nigeria: Nwando Achebe--The Woman and Her Works". AllAfrica. Retrieved 11 May 2017
  7. "Meet the Winner of the 2013 Aidoo-Snyder Prize--Dr. Nwando Achebe". African Studies Association. Archived from the original on 31 March 2017. Retrieved 13 May 2017.
  8. "African Studies Association. "Meet the Winner of the 2013 Aidoo-Snyder Book Prize--Dr. Nwando Achebe". Archived from the original on 31 March 2017. Retrieved 11 May 2017.
  9. "Nwando Achebe | College of Social Science | Michigan State University". socialscience.msu.edu. Retrieved 27 May 2020.
  10. ""The Politics of Knowledge Production—A Reflective Journey and Dance about the Epistemology and Practice of African Gender History"". www.international.ucla.edu. Retrieved 27 May 2020.