Jump to content

Ali Jita

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mukala mai kyau
Ali Jita
Rayuwa
Cikakken suna Ali Isah Jibrin
Haihuwa jahar Kano, 15 ga Yuli, 1983 (41 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a mawaƙi, mai rubuta waka, darakta, producer (en) Fassara da mawaƙi
Imani
Addini Musulunci
Mawakin hausa

Ali Isah Jibrin (Haihuwa: A ranar 5, ga watan Yulin shekara ta alif 1983) Ana masa laƙabi da Ali Jita a fannin waƙa, ana kuma kiran shi da Mai jita ko Ali Isah Jita sunan shi na yanka shine 'Ali Isah Jibrin. Ya kasance mawakin Hausa na zamani, marubucin waƙa kuma mai rerawa.[1][2][3] An haife shi a cikin jihar Kano a wani gari mai suna Gyadi gyadi, Ali jita ya tashi a Shagari quarters a karamar hukumar Kumbotso. Daga bisani kuma aiki ya mai da mahafinsu da su garin Lagos daga baya suka kara komawa Abuja. Sunan mahaifinsa Alhaji Sallau Jibrin Kibiya ya kasance mahauci ne, Mahaifiyarsa kuma Hajiya Ummul-Khairi.[4].

Ali jita ya fara karatun noziri a shagari quaters, yayi karatun firamari da sakandari a Victoria ireland dake Lagos a cikin wani barikin sojoji mai suna Bonikam Barrack, ya karasa karatun sa na sakandiri ne a Abuja. Sannan ya zurfafa karatunsa a Federal College of Education Kano inda ya karanta Public Administraion, inda aka bashi darajan shaidawa ta National Diploma, sannan kuma ya karanta ilimin kwamputa a Intersystem ICT School inda ya ƙara samun shaida na Diploma.[5]

Waka da fim.

[gyara sashe | gyara masomin]

Yawancin wakokin Ali jita an saka su a masana'antar fim ta Kannywood, amman wasu daga cikin Albom ɗin shi kuma an sayar dasu ne a wajen Kannywood, Yana waka ne tare da shahararren mawaki Nazifi Asnanic da kuma Fati Nijar a matsayin abokan arziki. Harwa yau, shahararren mawakin yayi waka tare da Nazir M Ahmad mai suna Mama, sannan yayi waka tare da Umar M Shareef mai suna Kano. A shekara ta 2018, Ali jita yayi wata waka mai suna Love, wakar ta lashe lambar girma na jadawalin wakokin da suka fi kowanne a shekaran, a inda wakan tazo na biyu, kamar yanda BBC Hausa suka dauko rahoto.[6][7] Ali jita yayi amfani da salan Ingausa wajen rubuta wakan da kuma rerawa. A shekara ta 2019, yayi bidiyon wakan sa mai suna Arewa angel tare da tsohuwar jaruman Kannywood mai suna Rahama Sadau. Sannan yayi bidiyon waka mai suna Love tare da Hadiza Gabon.[8]

Ali jita ya fara harkan waka tin yana ɗan shekara 16, a lokacin yana makarantan islamiyya a Lagos[4] tin lokacin da yake zurfafa karatun sa a Federal college of education kano ya kasance yana ɗan taɓa waka kadan-kadan. haka ya cigaba da taɓa waka har girman sa. ya kasance mutum ne mai saukin kai, yana da sanyayyar murya. Mutum ne kuma mai yawan murmushi. Yana san Nazifi Asnanic a matsayin abokin kirki a wajen waka da kuma cikinta. Kuma su biyun makusantan juna ne a harkan waka, sunyi wakoki dayawa tare irinsu Aboki da Ruwan zuma. An kira shi da Ali jita ne saboda san jita da yakeyi, kuma yana yawan rike Jita a wakokinsa da kuma ambatan sunanta. Ali jita yana da aure harda yara biyar, Usman suna kiranshi da Affan, da Aliyu inkiya Ramadan, Ahmad farid, zainab hidda sai Aisha ana kiranta da Afra.

Kundin Wakoki.

[gyara sashe | gyara masomin]
Albom Wakoki Shekara Adadin wakoki
Labarin duniya * wacece nake so
  • Labarin duniya
  • Bakandamiya 3
  • Murmushin alkawari
  • Zaman gida
  • Buje Remix
  • Uwar gida
  • Labarin jita remix
  • Rayuwa
  • Chan changi
  • Ga amarya ga ango remix
  • So sinadari remix
12
Zakin maza *Rabbana

*Duniya

*watan Azumi

*Farar diya

2016
Mata *Mata 2018
Arewa Angel

Mamana

Tarkon kauna

Gimbiyar mata

Buri uku

Yar lele

Duniya

Halimatu sadiya

Asha ruwa

Jawabi

Yara yara

Kece

Love

Indo

Aure

Zaman aure

Farar diya

Zakka

Mai jita

Fati fati

Kano

Ba'a san shekaran ba

[9]

Kambu da Lambar girma.

[gyara sashe | gyara masomin]

Ali jita ya samu lamban girmamawa a fannin waka daban daban akalla guda goma sha biyar 15 kamar haka:

Sunan awad Lamban girma shekara
Ama award
Tozali award
MTN award

Diddigin bayanai na waje.

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. https://www.bbc.com/hausa/news/2016/07/160711_kannywood_kalankuwa_sallah
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2019-02-15. Retrieved 2020-01-08.
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-05-28. Retrieved 2020-01-08.
  4. 4.0 4.1 https://allafrica.com/stories/200809220641.html
  5. http://hausafilms.tv/musician/ali_jita
  6. https://www.bbc.com/hausa/amp/labarai-46693772
  7. https://www.bbc.co.uk/hausa/labarai-46701664
  8. https://afrobitz.com/ali-jita-feat-hadiza-gabon-love-new-2018/amp/[permanent dead link]
  9. https://www.dailytrust.com.ng/author/belloabdulazeez/page/2117[permanent dead link]