Jump to content

Mohammed Kaliel

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mohammed Kaliel
Minister of Water Resources (en) Fassara

1999 - 13 ga Yuni, 2001 - Muktar Shagari
Gwamnan Jihar Bauchi

ga Maris, 1976 - ga Yuli, 1978 - Garba Duba
Rayuwa
Haihuwa 1942
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Mutuwa 10 ga Maris, 2015
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Mohammed Bello Kaliel (ya rasu a ranar 10 ga Maris din Shekarar 2015) ya kasance Sojan Najeriya matakin kanel kuma Gwamnan Jihar Bauchi na farko a Najeriya bayan an kafa ta a ranar 3 ga watan Fabrairun shekarar 1976 lokacin da aka raba Jihar Arewa maso Gabas zuwa jihohin Bauchi, Borno, da Gongola, a lokacin mulkin soja na Janar Olusegun Obasanjo. Ya rike mukamin har zuwa watan Yulin shekarar 1978.[1]

Mohammed Bello Kaliel ya shiga aikin soja a shekarar 1967. Daga shekarar 1972-1974, ya kasance malami a Kwalejin Tsaro ta Najeriya.[2] A watan Fabrairun 1976, Mohammed Kaliel ya zama gwamnan jihar Bauchi ta hannun shugaban kasa, Janar Murtala Muhammed, jim kadan kafin a kashe shi a wani yunkurin juyin mulki. Ya hau mulki a watan Maris 1976, ya kawo tawagar gogaggun ma’aikatan gwamnati daga Maiduguri domin kafa sabuwar gwamnati. Ya samu jihar ba ta da wutar lantarki da karancin ruwan sha daga rijiyoyin burtsatse, kuma ya sanya a inganta wannan muhimman ababen more rayuwa da fara mulkinsa.[3]

Kaliel ya kasance Kwamanda a Cibiyar Resettlement ta Legas, Najeriya daga shekarar 1978 – 1980, Darakta na dabaru da tsaro (1980 – 1981) da kwamandan Brigade of Guards, Legas (1981 – 1984). A watan Disambar 1983, a lokacin da Kaliel ke hutu daga Brigade of Guards, anyi wani juyin mulki da ya yi sanadiyyar Muhammadu Buhari zama shugaban kasa.[4]

Bayan kammala aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

Kaliel ya yi ritaya jim kadan bayan juyin mulkin a shekarar 1984. Bayan dawo da mulkin dimokradiyya a watan Mayu shekara ta 1999, an nada shi ministan albarkatun ruwa na tarayya tsakanin 1999 zuwa 2001. A watan Janairun 2001, ya gana da Gwamnan Jihar Zamfara, Ahmed Sani Yerima, wanda ya shaida masa cewa Dam din Gusau zai iya kafewa nan ba da dadewa ba, kuma ya roki Gwamnatin Tarayya ta mika ruwa daga Dam din Bakolori zuwa babban birnin Jihar, Gusau. Kaliel ya ce gwamnatin tarayya ta dukufa wajen samar da ingantaccen ruwa ga daukacin ‘yan Najeriya, kuma nan ba da dadewa ba za ta samar da tallafi ga jihohin, tare da baiwa Gusau fifiko.[5] An maye gurbinsa a cikin majalisar ministoci a ranar 13 ga Yuni 2001.[6]

A watan Mayun shekarar 2005, an nada shi a matsayin shugaban bankin All States Trust Bank Plc.[7]

A ranar 10 ga Maris, 2015, Bello Kaliel ya rasu a wani asibiti a kasar Turkiyya.

  1. "Nigerian States". WorldStatesmen. Retrieved 2010-01-12.
  2. "Arah, Two Others Join All States Board". ThisDay. 2004-05-21. Archived from the originalon 2009-08-17. Retrieved 2010-01-12.
  3. "Past Executive Council: Lt. Col Mohammed Bello Kaliel 1976 – 1978". Bauchi State Government. Archived from the original on 2011-07-25. Retrieved 2010-01-12.
  4. Shehu Shagari (2004-03-21). "How Buhari & Co Toppled Second Republic". ThisDay. Archived from the original on 2005-11-30. Retrieved 2010-01-12.
  5. "Iyefu Adoba (2001-01-12). "Gusau Dam Drying Up, Says Zamfara Governor". ThisDay. Archived from the original on 2004-12-06. Retrieved 2010-01-12.
  6. "Obasanjo soumet au Sénat les noms de nouveaux ministres" (in French). Panapress. 2001-06-14. Retrieved 2010-01-12.
  7. "The Late Brigadier Kaliel, One of Nigeria's Finest Officers – Buhari". 13 March 2015.

Samfuri:BauchiStateGovernorsGwamnan Jihar BauchiSamfuri:Nigeria Obasanjo GovernorsGwamna a gwamnatin obasanjoSamfuri:Cabinet of President Olusegun Obasanjo 1999-2003Kusa a gwamnatin Obasanjo