Saratu Gidado
Saratu Gidado | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Saratu Gidado |
Haihuwa | Jihar Gombe, 17 ga Janairu, 1968 |
ƙasa | Najeriya |
Mutuwa | jihar Kano, 9 ga Afirilu, 2024 |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | Jarumi |
IMDb | nm3885616 |
Saratu Gidado (17 Janairu 1968 – 9 Afrilu 2024), wacce aka fi sani da Daso, ‘yar wasan fina-finan Najeriya ce, a masana’antar fina-finan Kannywood. Daso ta fi fitowa a matsayin muguwa a fina-finan ta. Ta fara fitowa a fim a shekarar 2000 a fim ɗin Linzami Da Wuta, wanda kamfanin shirya fina-finai na Sarauniya Movies ta shirya.[1][2] Dagana kuma ta fito a sauran finafinai kamar Nagari, Gidauniya, Mashi, da Sansani.[3] Ta tabbatar da cewa tana son taka rawar muguwar mace.[4]
Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]
An haifi Saratu Gidado a Jihar Gombe dake Arewacin Najeriya. Ta yi makarantar firamare a Jihar Kano. Ita ce matar aure ta farko a masana'antar Kannywood.
Baya ga riko, an nada Gidado a matsayin jami’ar hulda da jama’a (Jakadiya) ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a shekarar 2016.
Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]
Gidado ta rasu ne a ranar 9 ga watan Afrilu, 2024, wanda ye daidai da watan Ramadan Ashirin da tara ga watan,ta yi sahur kafin ta kwanta barci, ta rasu tana barci tana da shekara 56, an yi jana’izarta bayan Sallah La'sar kamar yadda addinin Musulunci ya koyar.[5] Sarkin Kano Malam Aminu Ado Bayero ya samu damar Zuwa jana'izar nata da wasu sauran manyan gari da yan film.
Finafinai[gyara sashe | gyara masomin]
Saratu Gidado ta shiga masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood a shekarar 2000, kuma ta fito cikin fina-finai sama da 100.[6]
Take | Shekara |
---|---|
Yar Mai Ganye | |
Cudanya | |
Nagari | |
Sansani | |
Mashi | |
Fil'azal | |
Gidauniya | |
Gidan Iko | |
Jakar Magori | |
Mazan Baci | |
Mazan Fama | |
Rintsin Kauna | |
Shelah | |
Uwar Kudi | |
Yammaci | |
Daham | 2005 |
Sammeha | 2012 |
Gani Gaka | 2013 |
Ibro Ba Sulhu | 2014 |
Akwai Hanya | 2016 |
Ba Tabbas | 2017 |
Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]
- ↑ Matazu, Hafsah Abubakar (23 March 2019). "5 Kannywood veterans still on screen". Daily Trust. Archived from the original on 9 October 2019. Retrieved 9 October 2019.
- ↑ "I'm the only married woman that is still into acting – Daso". Blueprint. Retrieved 9 October 2019. Unknown parameter
|hidate=
ignored (help) - ↑ "TOP 10 NORTHERN ACTRESSES". Modern Ghana (in Turanci). Retrieved 9 October 2019.
- ↑ Blueprint (2021-08-27). "Why I like playing role of wicked women – Daso". Blueprint Newspapers (in Turanci). Retrieved 2022-07-23.
- ↑ Bahara, Hafsat Bello (2024-04-09). "JUST-IN: Veteran Kannywood Actress Saratu Daso Is Dead" (in Turanci). Retrieved 2024-04-09.
- ↑ "Saratu Gidado [HausaFilms.TV - Kannywood, Fina-finai, Hausa Movies, TV and Celebrities]". hausafilms.tv. Hausa Tv. Retrieved 9 October 2019.