Template:Kanun labarai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
  • A ranar 8 ga watan Afrilu miliyoyin mutane suka kalli Husufin Rana a yankin Amurka.
  • A ranar 7 ga Afrilu 2024, Kasar Rwanda ta cika shekaru 30 da kisan kare dangi wanda yayi sanadiyar mutuwar dubban mutane.
  • Ƙasar Indonesiya ta bi sahun ƙasar Afirka ta Kudu wajen shigar da ƙasar Isra'ila ƙara a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya dake birnin Hague, bisa ga mamata da kisan gillar da ƙasar Isra'ila take yima Falasdinawa.
  • Tsohon Firaministan ƙasar Asturaliya Scott Morrison, ya fitar da sanarwar barin dukkanin harkokin siyasa.
  • Ƙungiyar Tarayyar Turai ta sake jadadda matsayar ta na samar da kasar Falasdinu mai cikakken iko kusa da Isra’ila, tana mai cewa wannan ita kadai ce hanyar da za’a kawo karshen rikicin da aka shafe shekaru ana gwabzawa.
  • Najeriya ta lallasa Guinea-Bissau da ci 1-0, a fafatawar da suka yi a gasar lashe kofin Afirka a filin wasa na Félix Houphouet-Boigny da ke Abidjan na kasar Ivory Coast, yayin da Gini Ikwatoriya ta lallasa mai masaukin baki Ivory Coast da ci 4-0.