Maher Zain

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Maher Zain
Maher Zain at Tuisa charity concert Essen Germany 2012.jpg
Rayuwa
Haihuwa Tripoli (en) Fassara, 16 ga Yuli, 1981 (39 shekaru)
ƙasa Sweden
Sana'a
Sana'a mawaƙi, mawaƙi, mai rubuta waka da injiniya
Wanda ya ja hankalinsa Sami Yusuf (en) Fassara
Artistic movement rhythm and blues (en) Fassara
Kayan kida guitar (en) Fassara
voice (en) Fassara
Jadawalin Kiɗa Awakening Records (en) Fassara
Imani
Addini Mabiya Sunnah
maherzain.com

Maher Zain da Larabci ما هرزين ; (an haife shi a ranar 16 ga watan Juli 1981). Mawaki ne na Salon wakokin zamani wato R&B ne, kuma marabucin wakokin ne sannan kuma yana samar da kade-kade shi dan asalin Lebanon ne. Ya saki kundin wakokin sa na farko mai suna Thank you Allah a shekarar 2009, daga kamfanin wakokin su mai suna Awakening Records. Daganan kuma ya kara sakin Kundin sa na biyu mai suna Forgive mea watan Afrilu 2012 ta karkashin shi kamfanin wakokin nasa.

Daukaka[gyara sashe | Gyara masomin]

Farko daga tushe[gyara sashe | Gyara masomin]

Dangin Maher zain yan gudun hijira ne daga kasar Labanon zuwa Sweden tun yana dan shekara takwas. A kasar Sweden ya kammala dukkan karatun sa inda ya kammala digirin sa na farko akan ilimin gyaran jirgin sama. Daganan sai ya shiga masana'antar wakoki ta kasar Suwidin, a shekara 2005 kuma ya hadu da mawaki dan asalin Maroko haifaffen Suwidin RedOne. Lokacin da RedOne ya koma Amurika ne shima Zain ya bishi dan yaci gaba da wakokin sa a shekarar 2006. Bayan dawowar sa daga kasae Amurika ne kuma a Suwidin ya yanke hukuncin zama cikakken mawakin wakoki irinna addinin Musulunci

Nasarorin da ya samu[gyara sashe | Gyara masomin]

A shekarar 2009 MAHER ZAIN ya fara aikin kundinsa tare da kamfanin wakokin sa Awakening Records . Kundin nasa na farko maisuna Thank you Allah ya fitar dashi ne a 1 ga watan Nuwamba 2009, Kundin mai wakoki 13 da kuma garabasar wakoki 2 an fitar da shi ma acikin harahen Faransanci.

Zain da kamfanin sa na Awakenin Records sunayin amfani da kafafen sada zumunta kamar au Faceboo, YouTube da iTunes wajen yada wakokin sa a sassan Duniya. A farkon shekarar 2010 wakokin sa suka zagaye kasashen Larabawa dama aauran kasashen Musulmi dama tsakanin matasan Musulmai a kasaahenNahiyar Turai da yankunan Amurika. Zuwa karshen shekarar 2010 Sunan sa ne gagara badau wajen bincike a kasar Maleshiya da Indonisiya a shafin Google. Kuma wadannan kasashen ne suka zama mafiya hulda daahi wajen kasuwancin wakokin sa. Thank you Allah shine kundin sa wanda akafi saye akasashen Maleshiya da Indonesiya 2010.

Zain Ya fi yin mafi yawan wakokin sa cikin harahen Turanci amma kuma yakan yi wadansu wakokin da wani yaren na daban, kuma yakan yi kwaikwayon wakokinsa zuwa yarurruka da dama, Misali wakar Insha Allah akwaita a haraunan Turanci, Faransanci, Larabci, Turkanci, Malesiyanci da Indonesiyanci.Wakar Zain ta Allahi Allah Kiya Karoan reratane da yare Urdutare da hadin gwiwar ba fakiste kuma mawaki a kasar Kanada Irfan Makki. Zain ya shirya taron wakokin sa a kasashen Duniya da dama ciki har da Nahiyar Turai da Amurika, saurn sun hada da Maleshiya, Indonesiya, Saudiyya, da Misra. Yanada kungiyoyin masoya a dukkan wadannan kasashe, ciki harda Najeriya da Aljeriya dama wadansu kasashen da dama.

Maher Zain a wani wajen gabatar da wakokin sa shekarar 2012

Wakokin sa na Bidiyo[gyara sashe | Gyara masomin]

 • 2009: "Palestine Will Be Free"
 • 2009: "Subhan Allah"
 • 2010: "Insha Allah"
 • 2010: "The Chosen One"
 • 2011: "Freedom"
 • 2011: "Ya Nabi Salam Alayka"
 • 2011: "For the Rest of My Life"
 • 2012: "Number One For Me"
 • 2012: "So Soon"
 • 2012: "Guide Me All the Way"
 • 2013: "Love Will Prevail"
 • 2013: "Ramadan"
 • 2014: "Muhammad (P.B.U.H)"
 • 2014: "Nas Teshbehlana" (a Larabci ناس تشبهلنا)
 • 2014: "One Day"
 • 2015: "A'maroona A'maloona" (a Larabci أعمارنا أعمالنا)
 • 2016: "I am Alive" (da Atif Aslam)
 • 2016: "By my Side"
 • 2016: "Paradise"
 • 2016: "Peace Be Upon You"
 • 2016: "The Way of Love" (da Mustafa Ceceli)
 • 2017: "Close to You"
 • 2017: "As-subhu Bada" (a larabci الصبح بدا)
 • 2017: "Kun Rahma" (a larabci كن رحمة)
 • 2017: "Medina"
 • 2018: "Gülmek Sadaka"
 • 2018: "Huwa Alqur'an"
 • 2018: " Qur'an
 • 2019: "Ala Nahjik Mashayt2019"
 • 2019: "Ummi (Mother)"
 • 2019: "Ya Khuda"
 • 2019: "Live It Up"
 • 2019: "Lawlaka"
 • 2020: "Srebrenica"
 • 2020: "Asma Allah Alhusna (The 99 Names of Allah)"
 • 2020: "Antassalam"
Fitowa ta musamman a
 • 2011: "I Believe" (Irfan Makki tare da. Maher Zain) (a kundin Irfan Makki I Believe)
 • 2009 : "Never Forget" (Mesut Kurtis tare da. Maher Zain) (a kundin Mesut KurtisBeloved)
 • 2014: "So Real" (Raef tare da. Maher Zain) (a kundin Raef The Path)
 • 2014: "Eidun Saeed" (Mesut Kurtis tare da. Maher Zain) (a kundin Mesut Kurtis Tabassam)