Harshen Hausa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Yaren Hausa)
Jump to navigation Jump to search
Hausa
language
subclass ofWest Chadic languages Gyara
native labelHausa Gyara
coordinate location12°0′0″N 7°0′0″E Gyara
linguistic typologysubject–verb–object Gyara
writing systemLatin script, Arabic alphabet Gyara
Ethnologue language status2 Provincial Gyara
Wikimedia language codeha Gyara
indigenous toNijar, Nijeriya Gyara

Harshen Hausa na daya daga cikin rukubin Harsunan Chadic, kuma a k'ungiyar Harsunan Chadic kan, wanda ke cikin iyalin harshen Afroasiatic.

Hausa dayane daga cikin yarukan najeriya, hausa shine yare mafi girma a nijiriya, masu magana da yaren hausa a nijiriya sunkai kashi hamsin da biyar (55%). harshen hausa yana yaduwa ne ta hanyar 'yan-kasuwa. yan kasuwar da suke tafiya daga kasar hausa zuwa wasu kasashe da zummar kasuwanci, hakan yakara daukaka harshen hausa da hausawa a fadin duniya. idan aka ce Hausa ana nufin duk wani abu dayake da alaka da Hausawa ko kasashensu, da Harshen su, Hausawa nada asali a Najeriya da kasar habasha wato (Etophia), wanda ya yadu a duk fadin duniya. Ana kiran masu amfani da harshen da suna Hausawa, kasar hausa tana da tarihi mai yawa, tun kafin zuwan turarawa da larabarawa kasar hausa, hausawa suke da sarakuna da suttura da sana'oi masu tarin yawa.