Tsarin Zaizayar Najeriya da Gudanar Ruwa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Tsarin Zaizayar Najeriya da Gudanar Ruwa

Tsarin Kula da Zaizayar Ruwa a Najeriya (NEWMAP) wani shiri ne da Bankin Duniya ya taimaka da nufin magance matsalar zaizayar kasa a Nijeriya a yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya da lalata kasa a Arewacin Najeriya ta fuskoki da yawa. Wannan aikin ya samo asali ne daga neman taimako da Shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya yi wa Bankin Duniya a shekara ta 2010. Ya kuma nemi taimako don magance mummunar zaizayar kasa a Kudancin Najeriya da lalacewar kasa a Arewacin Najeriya da rashin tsaro na muhalli.[1][2]

Bayan Fage[gyara sashe | gyara masomin]

Kwamitin ya amince da aikin ne a ranar 8 ga Mayun, shekara ta 2012, ya fara aiki a ranar 16 ga Satumbar, shekara ta 2013 tare da nada Amos Abu, Ruth Jane Kennedy-Walker, Grant Milne a matsayin shugabannin kungiyar, ma’aikatar muhalli ta tarayya a matsayin hukumar da ke aiwatar da shi jimlar aikin aikin dalar Amurka miliyan 650 ne, kuma adadin da Bankin Duniya ya yi na dala miliyan 500 ne. aiki ne na shekaru 8, ana sa ran zai ƙare a ranar 30 ga Yuni, 2020.[3]

Aikin ya fara aiki a shekara ta 2013 tare da jihohi matuka bakwai wadanda sune; Abia, Anambara, Kuros Riba, Ebonyi, Edo, Enugu da jihar Imo wadanda suka gamu da barazana ta mummunar zaizayar kasa su zuwa abubuwan more rayuwa. A shekara ta 2015, aikin ya fadada don biyan bukatun muhalli na karin wasu Jihohi goma sha biyu wato; Delta, Oyo, Sokoto, Gombe, Plateau, Kogi, Kano, Akwa Ibom, Borno, Nasarrawa, Katsina da Neja .

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

External links[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "About Us – NEWMAP". newmap.gov.ng (in Turanci). Archived from the original on 2020-04-08. Retrieved 2018-03-08.
  2. User, Super. "Federal Ministry of Environment - NEWMAP". environment.gov.ng (in Turanci). Archived from the original on 2021-06-08. Retrieved 2018-03-08.
  3. "Projects  : Nigeria Erosion and Watershed Management Project | The World Bank". projects.worldbank.org. Retrieved 2018-03-08.