Jump to content

Falasdinu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Falasɗinu)
Falasdinu


Wuri
Map
 31°37′31″N 35°08′43″E / 31.625321°N 35.145264°E / 31.625321; 35.145264
Labarin ƙasa
Bangare na Southern Levant (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
UTC+02:00 (en) Fassara
UTC+03:00 (en) Fassara
Allenby delivering speech, Jerusalem, May 1918
Masu zanga zangar neman yancin palastin

Falasdinu (Turanci Palestine), (Larabci فلسطين) دولةفلسطين Daular Falastin kasa ce da ake rigima a kanta a nahiyar Asiya. Kasar na ikirarin mallakar yankin gabar tekun yammacin ta kwato (iyaka da kasar Isra'ila da Jordan) sai kuma yankin Gaza (iyaka da Israila da Masar) da kuma gabashin birnin Jerusalem wanda shi ne kasar take dauka a matsayin babban birnin ta, duk da yake kuma a birnin Ramallah ne ake tafiyar da mafi yawan aiyukan gwamnati. Mafi yawancin yankunan kasar Falasdinu na karkashin Yahudawan Israila 'yan kama guri zauna da suka kwace tun daga shekarar 1967. Yawan mutanen kasar ya kai 4,560,368 kidayar 2014, ita ce kasa ta 123 a yawan jama'a a duniya.

Bayan kammala yakin duniya na biyu a 1947, Majalisar dinkin duniya ta yi kokarin kafa kasar ta Falasdinu wadda ta kumshi Larabawa Musulmai, da kuma Yahudawa da kasar su ta Israila a shekara ta 1948. Bayan kafa kasar ta Falasdinu ne sai larabawa Musulmai suka dauki makamai domin nuna adawa da yin hakan tare da yakar Yahudawa.

Tun daga nan yankin ya yi ta cigaba tare da canza salo kala-kala har zuwa ranar 15 Nuwamba, a shekarar 1988, inda shugaban Falsdinawa Yaseer Arafat, ya ayyana kafa kasar ta Falasdinu a birnin [[Aljas]] na kasar AljeriyaShekara daya kuma bayan sa hannun kan yarjejeniyar Osla Accords a shekara ta 1993 gwamnati ta kafu a kasar Falsdinu.

Kasashe 136 daga cikin mambobi a majalisar dinkin duniya ne suka amince da Falasdinu a matsayin kasa. Kasar har yanzu ba mamba ba ce ba a Majalisar dinkin Duniya, amma kuma mamba ce a kungiyar kasashen larabawa wato G77, da kuma Hukumar wasanni ta Olympic da sauran manyan kungiyoyin duniya.

Asiya    

Kasashen tsakiyar Asiya l

KazakystanKyrgystanTajikistanTurkmenistanUzbekistan

Gabashin Asiya

SinJapanMangoliaKoriya ta ArewaKoriya ta KuduJamhuriyar Sin

Yammacin Asiya

ArmeniyaAzerbaijanBaharainGeorgiaIrakIsra'ilaJordanKuwaitLebanonOmanQatarSaudiyyaSiriyaTurkiyaTaraiyar larabawaFalasdinuYemen

Kudu maso gabashin Asiya

BruneiKambodiyaIndonesiyaLaosMaleshiyaMyanmarFilipinSingaforaThailandTimor-LesteVietnam

Tsakiya da kudancin Asiya

AfghanistanBangladashBhutanIndiyaIranMaldivesNepalPakistanSri Lanka

Arewacin Asiya

Rasha

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.