Mesa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mesa
Scientific classification
KingdomAnimalia
PhylumChordata
ClassReptilia (en) Reptilia
OrderSquamata (en) Squamata
Dangipythons (en) Pythonidae
genus (en) Fassara Python
Daudin, 1803

Mesa tana daga cikin nau'ukan macizai wato macijiya sai dai ita Mesa babbar macijiya ce don kuwa tana da hatsarin gaske, tunda har mutane takan haɗiye ba tare da wani ɓata lokaci ba. Mafi akasari mesa tana rayuwarta ne a daji tana haɗiye namun daji har na ruwa takan haɗiye kada da kifi da sauran halittun ruwa. Ana kuma samunta a yankunan Afirka Asiya da kuma ƙasar Ostireliya (Australia) a waɗannan yankunan Mesa ta fi yawa, sai kuma irin ƙasashen Indiya Bangladesh, Pakistan, China da dai sauransu. [1][2] Ana samun Nau'ukan mesa har kusan kala arba'in da biyu (42) a faɗin duniya. [3][4]

mesa tana ƙoƙarin haɗiye akuya bayan ta kasheta a ƙasar Zinbabuwe

.

Yadda Mesa take haihuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Mesa tana haihuwa ne ta hanyar yin ƙwai kamar ƙadangare, tsaka maciji da dangin su. Matan mesa su ne suke ƙyanƙyashe ƙwansu da kansu. Sai dai duk da haɗarin da ke tattare da mesa mutane suna farautarta sosai saboda wasu suna cin namanta, ana kuma amfani da fatarta wajen ɗinka takalma, jaka da maɗaurin wando (belt) dai sauransu.[5]

Mesar kudancin Indiya

Amfanin da sassan jikin Mesa keyi[gyara sashe | gyara masomin]

mesa a cikin daji ta fito da harshen ta

Ana amfani da wasu sassan jikin mesa don yin waɗansu magunguna, wato masu maganin gargajiya suna amfani da fatarta, jininta da kitsenta don yin wasu magunguna a ƙasashen Afirka kenan su ne suke da waɗannan sirrikan game da mesa. Misali masu maganin gargajiya suna amfani da kitsen mesa don maganin sanyi, dafin maciji da kuma maganin mayu da dai sauransu. Har ila yau dai, su masu bada maganin gargajiya ko kuma ƴan bori suna amfani da fatar mesa don yin kayan sawa wato (walki) sai kuma idan ka je ƙasar Afirka ta Kudu suna ɗaukar mesa a matsayin wata alamar ƙarfi ce shi yasa suke yawan yin amfani da fatu da sauran sassan jikin ta tun ba ƴan ƙabilar zulu ba. Haka ana amfani da kitsen mesa wajen maganin ciwon gaɓoɓi ko kuma gaɓɓai, haƙora da kuma maganin ciwon ido wasu suna ganin har maganin ciwon hauka kitsen mesa yana yi. Haka kuma, ana amfani da jinin mesa wajen magunguna iri-iri. Yaren Sukuma da yake a ƙasar Tanzaniya suna amfani da wasu sassan jikin mesa don yin maganin ciwon baya, ana sawa ne a jikin mutum a bar shi na tsawon kwana biyu ko uku. Idan kuma muka dawo nan gida Najeriya muna amfani da hantar mesa don maganin sauran macizai. Har ila yau, dai a Najeriya ana amfani da kan mesa don maganin mayu. Idan kuma muka koma ƙasar Ghana su kuma suna ganin mesa wata Kariya ce a kan sauran macizai. A takaice dai Mesa macijiya ce mai haɗiyar duk nama ko mutum ko dabba.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Hotunan gumurzu tsakanin Mesa da Kada". bbc hausa. 27 March 2014. Retrieved 11 August 2021.
  2. Ahmad Ilyari, Aliyu (14 August 2021). "Mutanen da suka kashe mesar da ta daɗe tana cinye musu dabbobi". bbc hausa. Retrieved 14 August 2021.
  3. Sulaiman, Abubakar (17 June 2018). "Abin tausayi: Kalli Bidiyon yadda aka zaƙulo matar da Macijiya ta haɗiye". legit hausa. Retrieved 11 August 2021.
  4. Bisset, Victoria (11 September 2020). "Elderly ball python lays eggs 'without male help'". bbc.co.uk news. Retrieved 11 August 2021.
  5. "Female snake living in captivity without a male companion gives birth – again". The Guidian. 17 September 2015. Retrieved 18 September 2021.