Jump to content

Tarihin Masarautar Zazzau

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Tarihin Masarautar Zazzau

Tarihin Masarautar Zazzau Zazzau, sunane da ya samo asali daga sunan takobi wanda kuma daga baya ya koma sunan wata babbar masarauta mai daɗaɗɗen tarihi daga cikin masarautun Arewancin Nijeriya. Ɗalhatu (2002), ya kawo cewa, duk wanda ke riƙe da wannan takobi to shi ne sarki, sannan kuma suna kiransa da sunan ‘Maɗau Zazzau’, ma’ana, wanda ke ɗauke da Zazzau. Ya zo a Bryant (shekarar bugu ta goge), cewa, shi wannan takobi mai suna Zazzau, abu ne da jama’ar wasu yankuna na masarautar Zazzau ɗin ke girmamawa, rantsuwa ma idan za su yi da shi suke yi.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Wannan masarauta na ɗaya daga cikin manyan masarautun ƙasar Hausa (Arnett, 1920).

Ɗalhatu (2012) ya faɗi cewa bincike ya nuna cewa akwai mutane a wannan yankin na masarautar Zazzau tun lokacin da ake kira ‘Stone Age’ a Turance. Shi kuwa wannan lokacin na ‘Stone Age’, lokaci ne da mutane suka riƙa amfani da duwatsu wajen sana’anta makamai da sauran kayan aiki, kamar irinsu kibiyar harbi, wuƙar yanka, dutsen markaɗa ko niƙa kayan abinci, da sauransu. Wannan lokacin, lokaci ne mai nisan gaske. A sassan Turai akwai ƙasashen da suke dangana shi da shekaru miliyan biyu da rabi baya (2.5 Million B.C.), wato shekaru miliyan biyu da rabi kafin aiko Annabi Isa. Sannan kuma ƙarƙarshensa shi ne shekaru dubu biyar baya (5000 B.C.) a wasu sassan na duniya, duba (Schick da Nicholas, 2008). To amma Susan da Roderick (1981), sun tabbatar da faruwar wannan fasaha a sashen Africa ta yamma da kuma suka ambato ƙasar Mali a ciki.

Sai dai su a nasu binciken sun nuna farkon wannan fasaha a Afrika ta Yamma shi ne shekaru dubu goma sha biyu (12,000 B.C.) har zuwa shekaru dubu ɗaya (1000 B.C.).

Saboda haka idan muka ɗauka cewa jama’a sun zauna a wannan yankin tun a wancan lokacin wanda bisa binciken wasu masana kimiyyar ƙasar Amurka wato Susan da Roderick (1981), abin ya yi daidai. Musamman tunda sun ambata sunan Mali a cikin ƙasashen da suka ambata, to akwai yiwuwar faruwar hakan.

Saboda ai ko sarkin Zazzau na farko a jerin sarakunan Fulani, wato Malam Musa Bamalli, tushensa ƙasar Mali ɗin ne. saboda haka akwai daɗaɗɗiyar dangantaka tsakani ƙasar Mali da wannan yankin na ƙasar Hausa.

A wannan lokacin da ake magana a kai, ƙauyukan da suke wannan kewaye sun haɗa da Madarkaci, Kufena, da kuma Tukur-Tukur (Ɗalhatu, 2002; Bryant, shekarar bugun ta yage; Arnett, 1920). Kuma dukkan waɗannan yankuna a gindin duwatsu suke. Jama’ar da ke zaune a waɗannan yankuna kuma a wannan lokaci mai tsawo a baya, basu da wani shugaba guda ɗaya. Sai dai kowane gida suna da shugaban gidan wanda shi ne babba a gidan. Abin da ke haɗa su waje guda shine wancan takobi da suke girmamawa (Bryant, shekarar bugu ta yage).[1][2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]