Usman Ibn Affan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Sayyadina Usman)
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Usman Ibn Affan
Khalifofi shiryayyu

5 Nuwamba, 644 - 17 ga Yuni, 656 (Gregorian)
Sayyadina Umar - Sayyadina Aliyu
Rayuwa
Haihuwa Makkah, 574
ƙasa Hijaz
Khulafa'hur-Rashidun
ƙungiyar ƙabila Larabawa
Ƙuraishawa
Mutuwa Madinah, 17 ga Yuni, 656 (Gregorian)
Makwanci Al-Baqi'
Madinah
Yanayin mutuwa kisan kai (blunt trauma (en) Fassara)
Killed by Abdullah ibn Saba' (en) Fassara
Yan'uwa
Mahaifi Affan ibn Abi al-'As
Mahaifiya Urwa bint Kariz
Abokiyar zama Umm Amr Bandage Jundub (en) Fassara
Ramlya bint Shayba (en) Fassara
Umm al'-Banin bint Ayni (en) Fassara
Fatima Bint Al-Waleed (en) Fassara
Q68678851 Fassara
Ummu Kulthum  (624 -
Na'ila bint al-Farafisa (en) Fassara  (641 -  17 ga Yuni, 656)
Rukayyah  (unknown value -  624)
Yara
Siblings Umm Kulthum bint Uqba (en) Fassara, Walid ibn Uqba (en) Fassara, Khàlid ibn Uqba ibn Abi-Muayt (en) Fassara, Aminah bint Affan (en) Fassara da Umara ibn Uqba (en) Fassara
Karatu
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci

Uthman ibn Affan (larabci: عثمان بن عفان‎),Uthman ibn Affan ko, Usman, Osman, Uthman. ya kasan ce yayi rayuwa daga shekara ta (579 zuwa 17 Yunin 656). An kuma haife shi ne a shekara ta 579 (42 BH) wanda ke garin ɗaif, dake a Saudiya, ya kuma rasu ne a shekara ta 17 ga watan wanda tayi dai dai da (17 Dhūl Al-Qa‘dah 35 AH) (shekara ta 656 ) (ya rayu tsawon shekaru 77) an birne shi ne a garin Madinah, wanda ake kira Jannatu al-Baqi dake Madinah. Yakasance sirikin Manzon Allah , tsira da aminci su tabbata agareshi, Halifan Musulunci na Uku, Ɗaya daga cikin Halifofi shiryayyu, ɗan zuri'ar Banu Umayyah daga ƙabilar Kurayshawa.[1] Sanda Sayyidina Umar yarasu da shekaru 59/60, ʿUthmān, yana da shekaru 64/65 a duniya sai ya gaji Umar bin Khaddab bayan rasuwarsa. Uthman ibn Affan Yayi Halifanci daga 6 ga watan Nuwamba shekara ta 644 zuwa 17 ga watan Yuni shekara ta 656.

Ƙarƙashin jagorancin Uthman, Khalifancin Rashidun ya faɗaɗa zuwa Fars ( Iran ta yau) a cikin 650, da wasu yankuna na Khorāsān ( Afganistan a yau) a shekara ta 651. An fara cin Armeniya a cikin 640s.[2] Haka kuma mulkinsa ya yi ta fama da zanga-zanga da tashe -tashen hankula wanda a karshe ya kai ga tayar da makamai da kuma kashe shi .

Usman bin Affan yarasu ne sanadiyar farmaki da aka afka masa. An samu wasu yan tada kayan baya game da addinin Musulunci tare da kin shugabancin sa. Wanda suka afka masa alhali yana karatun alqurni. Tarihi ya nuna an kashe shi ne akan zalumci wanda hakan yasa aka haura katangan gidansa sannan aka kashe shi. Ali Ibn Abi-Talib ne ya gaje shi bayan rasuwarsa. Matayensa; "Ummu 'Amr" Asma'u bintu Abi Jahal, Ruqayyah bintu Muhammad, Ummu Kulthum bint Muhammad, Fakhitah bintu Ghazwan_ Ummu al-Banin bintu Uyayna, Fatima bintu al-Walid Daughter of Khalid ibn Asid Umm 'Amr Umm Najm bint Jundub Ramla bint Shayba, Bunana Na'ila bint al-Furafisa, Zaynab bintu Hayyan. Bakurayshe (Banu Umayya) Mahainfinsa: Affan ibnu Abi al-'As Mahaifiyarsa: Arwa bintu Kurayz

Uthman ya auri yar Manzon Allah Ruqayyah, kuma bayan ta rasune, Manzon Allah yasake aura masa yar'sa Umm Kulthum. Dukkaninsu sun kasance manyan ya'yan Manzon Allah Muhammad kuma yayyi ga Fatimah yar Manzon Allah matar Aliyu bin Abi Dalib, saboda ya aura yayan Manzon Allah biyu ne yasa ake kiransa da Dhū al-Nurayn ("Wanda ya mallaki Haske biyu").

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. Tabatabai, Sayyid M. H. (1987). The Qur'an in Islam : its impact and influence on the life of muslims. Zahra Publ. ISBN 978-0710302663.
  2. Ochsenweld, William; Fisher, Sydney Nettleton (2004). The Middle East: A History (6th ed.). New York: McGraw Hill. ISBN 978-0-07-244233-5.