Uthman bin Affan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Uthman bin Affan
Uthman.png
Rayuwa
Haihuwa Makkah da Hijaz, 574
ƙasa Hijaz
Khulafa'hur-Rashidun
ƙungiyar ƙabila Larabawa
Quraysh (en) Fassara
Mutuwa Madinah, ga Yuni, 17, 656
Makwanci Al-Baqi'
Madinah
Yanayin mutuwa kisan kai (blunt trauma (en) Fassara)
Template:P Abdullah ibn Saba' (en) Fassara
Yan'uwa
Mahaifi Affan ibn Abi al-'As
Mahaifiya Urwa bint Kariz
Yara
Siblings
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci

Uthman ibn Affan (larabci: عثمان بن عفان‎), wasu na rubutawa Usman ko Osman, yarayu daga shekara ta (579 zuwa 17 Yunin 656). An haife shi shekara ta 579 (42 BH) a garin Taif, dake Saudiya, yarasu a 17 Yuni shekara ta 656 (shekarunsa 76–77) (17 Dhū al-Qa‘dah 35 AH) a garin Madina, An birne shi a Jannat al-Baqi, dake Madinah. Yakasance sirikin manzon Allah Muhammad, tsira da aminci su tabbata agareshi, Halifan musulunci na Uku, Daya daga cikin Halifofi shiryayyu, Dan zuriar Banu Umayya daga kabilar Kurayshawa, Sanda Sayyidina Umar yarasu da shekaru 59/60, ʿUthmān, yana da shekaru 64/65 a duniya sai yagji Umar bayan rasuwarsa.

Yayi Halifanci daga 6 ga watan Nuwamba shekara ta 644 zuwa 17 ga watan Yuni shekara ta 656. Ali Ibn Abi-Talib ne ya gaje shi bayar rasuwarsa. Matayansa; "Umm 'Amr" Asma bint Abi Jahl, Ruqayyah bint Muhammad, Umm Kulthum bint Muhammad, Fakhitah bint Ghazwan_ Umm al-Banin bint Uyayna, Fatima bint al-Walid Daughter of Khalid ibn Asid Umm 'Amr Umm Najm bint Jundub Ramla bint Shayba, Bunana Na'ila bint al-Furafisa, Zaynab bint Hayyan. Bakurayshe (Banu Umayya) Mahainsa: Affan ibn Abi al-'As Mahaifiyarsa: Arwa bint Kurayz

Uthman ya aure yar Manzon Allah Ruqayyah, kuma bayan ta rasune,Manzon Allah yasake aura masa yar'sa Umm Kulthum. Dukkaninsu sun kasance manyan ya'yan manzon Allah Muhammad kuma yayyi ga Fatimah yar Manzon matar Aliyu bin Abutalib, saboda ya aura yayan Manzon Allah biyu ne yasa ake kiransa da Dhū al-Nurayn ("Wanda ya mallaki Haske biyu").