Alhassan Saeed Adam Jos

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sheikh Dr

Alhassan Saeed Adam Jos
Personal
Haihuwa 1956
Mutuwa 05 ga Afrilu 2017 (Shekaru 61)
Addini Musulunci
Dan kasan Nigeria
Gida Jos
Kabila Hausa
Education PhD
An san shi da Da'awah

Sheikh Dr. Alhassan Sa'eed Adam Jos (1956-2017) fitaccen malamin addinin musulunci ne a Najeriya, malami, kuma marubuci wanda ya shahara wajen bayar da gagarumar gudunmawa ga ilimin addinin musulunci a Najeriya. An haifi Sheik Dr Alhassan Saeed a wani gari da ake kira Mekekiya a kusa da wani kauye da ake kira Mai Zuwo a karamar hukumar Sule Tankarkar a ta Jigawa a shekarar 1956, iyayensa na daga cikin wadanda suka fara zuwa garin.[1]

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Malam ya fara karatunsa a kauyen Dan Kama dake karamar hukumar ta Sule Tankarkar amma saboda hali na rashin yarda da boko da da yawa daga cikin iyaye ke yi a wancan zamani yasa babansa ya cire shi daga makarantar ya maida shi makarantar allo a Jobi cikin jihar Kano gurin wani malami mai suna Malam Adamu Jobi, wanda a wannan lokaci babu wani malami kamarsa a wannan yankin, daga nan wani malami ya dauke shi zuwa Jos inda ya hadu da wani malami mai suna malam Muhammad dan uwan malam Adam na Jobi anan ya cigaba da karatu a gurinsa ya kuma cigaba da karatun boko.

A shekarar 1972 wani malami ya nemi da suje Maiduguri da suka je can ya haddace Alkur’ani a shekara guda, daga nan kuma ya dawo Jos ya cigaba da karatunsa a gurin wasu malamai daga cikinsu akwai:

A 1975 lokacin da gwamnati ta kirkiro Universal Basic Education (UBE) malam ya fara karantarwa, daga bisani ya daina karantarwa ya koma makaranta. A shekarar 1979 ya fara Arabic Teachers College Katsina, inda ya gama a 1984/85 ya fito da sakamako mai kyau wanda yafi na kowa a wannan shekarar har aka bashi kyauta.

A shekarar 1987 malam ya koma Jami'ar Bayero dake Kano inda ya yi diploma a Hausa, Arabic da Islamic Studies. Bayan ya gama sai ya koma Jamiar Jos inda ya yi digiri a Hausa Arabic and Islamic Studies. A shekarar da ya gama Jami'ar Jos ne wasu larabawa daga kasar Saudiya suka zo don shirya bita ga masu karatun addini, malam yaje gaishesu sai suka nemi daya zo ya halarci wannan bita, malam ya halarci bitar inda yazo na biyu, sai larabawan suka ba shi shawara ya cike fam don yin karatu a kasar Saudiya, a nan ne ya yi digirinsa na biyu a tsangayar Alkur’ani.

Bayan ya gama digirinsa na biyu a kasar Saudiya sai ya dawo Jami'ar Jos ya sake wani digiri na biyun, daga baya kuma a shekarar 2007 ya koma Jamiar Usman dan Fodio ya yi digiri na uku (PhD).

Gudumawarsa wajen karatu da karantar da al'umma[gyara sashe | gyara masomin]

Malam ya share rayuwarsa wajen karatu da karantarwa da yada sunnar Annabin rahama (SAW), ko a ranar da zai bar duniya saida ya karantar da littafin Atttargib Wattarhib na Imamul Munziri (karatun da yake ma take da hikimar safiya).

Malam ya rayu cikin Alkur’ani ya kuma koyar duk bayan sallar Asubahi ko Magriba matukar dai yana gari kazo kofar gidansa zaka same shi yana karanta Alkur’ani ko kuma yana karantarwa. Shine farkon wanda ya fara bude halka ta Alkur’ani a garin Jos a layin Mudi na Garba kusa da gidan malam Lawal Maka, mutane sama da 500 sun haddace Alkur’ani a wajensa.

Ba nan kawai malalm ya tsaya ba, ya rike mukamai da yawa da bada gudumawa don cigaban addinin musulunci, daga ciki akwai:

Mu'amalarsa da yan uwansa da sauran al'umma[gyara sashe | gyara masomin]

Malam ya kasance mutum mai kyakkyawar dabi'a ga yan uwansa da sauran al’umma da yak tare da su, mutum ne mai hakuri da juriya bisa abun da aka masa, inda za a masa abu na cutarwa kace zaka rama mai kokarin hana mutum yake yi yace a barsu da Allah.

Malam ya kasance mai kyakkyawar mu'amala da sauran abokansa na da’awa, duk wani abokin da’awa da suke tare da shi zaka samu yana fadan alakairi akansa domin sun san cewa mutum ne mai basira da hangen nesa, baya gaggawar bada fatawa akan addini akan abin da bai sani ba. An sha masa tambaya yace bai sani ba a bari sai ya tambayi malamansa su ba shi amsa.

Littafan da ya karantar a lokacin rayuwarsa[gyara sashe | gyara masomin]

Malam ya karantar da littafai da dama a rayuwarsa daga ciki akwai;

Rubuce-rubucensa[gyara sashe | gyara masomin]

Malam ya yi rubuce da dama daga ciki akwai nasihatu dalibu li alimul arbab, bidayatu dalib fi ilmul tajwid (wanda ake karantarwa a duk makaratun IZALA musamman makaratun IZALA bangaren Sheik Sani Yahya jingir.

Dalibansa[gyara sashe | gyara masomin]

Malam yana da dalibai da yawa da suka yi karatu a gunsa daga cikinsu akwai:

  • Malam Shehu Sulaiman (wanda ya wakilci Najeriya a gasar karatun Alkur’ani da aka yin a duniya a kasar Saudia)
  • Malam Sani Ahmad (yaje musabakar Alkur’ani na kasa da ake shiryawa a Usman dan Fodio)
  • Malam Ibrahim Idris Darussa’ada
  • Muhammad Nuru Kalid (tsohon limamin masallacin yan majalisa dake Apo Abuja)
  • Dr Abdurrahman Idris (Malami a Aminu Kano College for Legal and Islamic Studies)
  • Gwani Muhammad Adam Alkadi (dan London)
  • Malam Mika’il Muhammad Mika’il
  • Malam Salihu Fari
  • Malam Ibrahim (Abu Farhan)
  • Malam Hashim Sani Hashim
  • Muhammad Kabir (Qari'u)
  • Malam Sani Ahmad (Abu Rukayya)

Matansa da yayansa[gyara sashe | gyara masomin]

Malama yana da mata guda 4 da yaya 27 da jikoki da yawa, daga cikin yayansa akwai

  1. Abdulbasid
  2. Mubarak
  3. Adda’urrahman
  4. Najib
  5. Hamza
  6. Kadija
  7. Rukayya
  8. Ahmad
  9. Maryam
  10. Aisha
  11. Yusra
  12. Ibrahim
  13. Aliyu
  14. Umar
  15. Mardiya
  16. Fadl
  17. Fudail
  18. Muhammad da sauransu.

Mutuwarsa[gyara sashe | gyara masomin]

Malam ya mutu ranar Laraba 08-07-1438 / 05-04-2017 yana da shekaru 61 a garin Kano, Shugaban Kungiyar IZALA Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau ne ya masa salla, dubbannin al’umma sun halarci janazarsa daga Najeriya da kasashen waje.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. How I succeeded Dr. Gumi - Sheikh Alhassan Jos. Daily Trust (in British English). 4 Sep 2010. Retrieved 02-10-2024.