Jump to content

Umar Ibn Al-Khattab

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Hazrat Umar)
Umar Ibn Al-Khattab
2. Khalifofi shiryayyu

22 ga Augusta, 634 - 3 Nuwamba, 644
Sayyadina Abubakar - Sayyadina Usman dan Affan
Rayuwa
Haihuwa Makkah, 586
ƙasa Khulafa'hur-Rashidun
Mutuwa Madinah, 3 Nuwamba, 644
Makwanci Masallacin Annabi
Yanayin mutuwa kisan kai (stab wound (en) Fassara)
Killed by Abu Lu'lu'a (en) Fassara
Ƴan uwa
Mahaifi Al-Khattab bin Nufayl
Mahaifiya Ḥantamah bint Hishām
Abokiyar zama Ummu Kulthum bint Ali
Umm Kulthum bint Jarwal (en) Fassara
Quraiba bint Abi Umayya
Umm Kulthum bint Asim (en) Fassara
Atika bint Zayd (en) Fassara
Zaynab bint Madhun (en) Fassara
Yara
Ahali Zayd ibn al-Khattab (en) Fassara da Fatimah bint al-Khattab (en) Fassara
Ƴan uwa
Karatu
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a statesperson (en) Fassara, Caliph (en) Fassara, Liman, shugaban addini da Sahabi
Aikin soja
Ya faɗaci Badar
Yaƙin Uhudu
Yaƙin gwalalo
Yaƙin Khaybar
Imani
Addini Musulunci
Fayil:Rashidun Caliphs Umar dan Al-Khattāb - عُمر بن الخطّاب ثاني الخلفاء الراشدين.svg

Umar, ko kuma a Turanci Omar a Larabci kuma عمربن الخطاب Umar dan Al'Khattab hausa Umaru dan Kaddabi Allah ya kara yarda da shi.

Ɗaya ne daga cikin manyan Sahabban Annabi Muhammad (s.a.w), Wanda ake wa laƙabi da suna Faruk (wato me rarrabe Ƙarya da Gaskiya), kuma shine na biyu cikin halifofin Musulunci. Yana ɗaya daga cikin Halifofinnan guda huɗu na Halifancin Annabta, sannan kuma yana ɗaya daga cikin sahabbai goman da Annabi yayima bushara da Aljanna tun suna Duniya. Umar ya kasance mai taka tsan-tsan tare da gudun duniya, kasancewar sa mutumin da yayi kaurin suna kwarai wajen rarrabewa tsakanin gaskiya da ƙarya ne yasa akayi masa laƙabi da Al'faruk, ma'ana mai raba ƙarya da gaskiya. Umar ya kasance babban jagora, kuma dukkannin hadisan ruwayar shi ana kallonsu a matsayin hadisai ingantattu.

Farkon rayuwar sa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Sayyidina Umar a birnin Makka daga ƙabilar Banu Adiy. Mahaifinsa Al'Kattab ibn Nufayl mahaifiyar sa itace Hantama bintu Hisham, ƴar kabilar Banu Makhzun. A lokacin ƙuruciyar sa, Umar ya kasance yana taya mahaifin sa kula da raƙuman sa.

Tun a lokacin ƙuruciyar sa Sayyidina Umar ya kasance mai sha'awar koyon rubutu da karatu. Hakane yasa ya samu ƙwarewa wajen iya rubutu da karatu, harma ya zama gagara-badau wajen iya rubuta waƙe-waƙe kamar yadda larabawa suka shahara wajen rubuce-rubuce na waƙe-waƙe a zamanin kafin zuwan Musulunci ana danganta basirar Umar da gado daga wajen Mahaifin sa wato wanda ya haifeshi.

Hakanan dai a zamanin ƙuruciyar Sayyadina Umar, ya zama babban ɗan kaasuwa inda yake zuwa ƙasashen Romaniya da Farisa fatauci. Sai dai harkar kasuwancin bata karɓe shiba sosai kamar sauran takwarorin sa.

Zamanin Annabi Muhammad (s.a.w)[gyara sashe | gyara masomin]

Takobin Sayyadina Umar

Kafin Musuluntar sa[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta ɗari shida da ɗaya miladiyya, 601 C.E. Umar bai bayar da gaskiya ga Annabi ba da farko. Harma ya kasance babban mai adawa da Annabi Muhammad (S.A.W). Sakamakon takurawar da Umar da sauran kafiran makkah na lokacin sukema Annabi da wadanda suka musulunta ne yasa Annabi Muhammad (S.A.W) ya umarci wasu daga cikin musulmai da suyi hijirah daga makkah zuwa kasar Sham. Lokacin da sahabbai sukabi umarnin Annabi (s.a.w) ne sai ganin haka ya kara tayar da hankalin Sayyadina Umar harma ya fara shirye shiryan kashe Annabi Muhammad (s.a.w).

Musuluntar Sayyadina Umar[gyara sashe | gyara masomin]

Umar ya shiga musulunci ne a shekarar 616 Miladiya. wato shekara daya kenan bayan hijirar Musulmai zuwa Sham. Ibn Ishak, yayi rubutu a lattafin sirar shi game da Musuluntar Sayyadina Umar.

Ga tarihin, a ranar da Umar ya yake shawarar "a yau" zai kashe Annabi Muhammad (S.A.W), ya dauko takobin sa ya nufi inda Annabi Muhammad (S.A.W) yake, sai ya hadu da wani sahabi, yace mishi me zai hana ka fara daga dangin ka, abun ya bawa Sayidina Umar mamaki, sai wancan ya ce miishi shin baka ji cewa knwarka ta Musulunta ba? Daga nana ya kama hanya, sai gindan yar'uwar shi, yasame ta da mijinta suna karatun Alqurani, sai yaji da kunnensa alhali baisan sun muslumta ba, sai yayi fushi mai tsanani har yakaiga ya bugi dan uwan nasa, matar dan uwan nasa tace Ashhadu an laa ilaha illallahu wa anna Muhammadan Rasulullahi, sai jikin sa yayi sanyi, sai umar ya umurceta da ta bashi fallen Al-Kur'ani yagani, sai ta bashi ya karanta ayoyin qurani, sai yace don wannan Kuraishu suke azabtar da mutane? kai tsaye ya wuce zuwa Darul-Arqam da ke karqashin dutsen Safa wanda kuma nan Manzon Allah (s.a.w) ya samu mafaka. Da isar Sayyadina Umar (r.a) wannan gida sai ya kwankwasa kofa. “ Sai mai gadin Gidan yace Wanene yake kwanKwasa kofar?” Sayyadina Umar ya amsa da “Umar ne”. Da mai gadin ya leko ya gan shi da takobi zare, sai ya yi shakkar bude kofar. Sai Sayyadina Hamza (r.a) ya ce da shi, “Bude masa idan da alheri ya zo muna maraba da shi idan kuma da akasin haka ya zo ai sarkin yawa ya fi sarkin karfi”. Aka bude masa ya shiga, Da shigarsa sai Sayyadina Hamza (r.a) ya dakume shi ya ce da shi “Umar, me ke tafe da kai?” Sauran Musulmi kuma suka zazzare takubbansu suka yi masa kawanya (suka zagayeshi) da zimmar ko da zai tada jijiyar wuya sai su cimmasa. Da jin wannan hayaniya sai Manzon Allah (s.a.w) ya fito daga dakinsa ya ce da Sayyadina Hamza (r.a) “kyale shi ya karaso gare ni”. Da Sayyadina Umar (r.a) ya kusanci Manzon Allah (s.a.w) sai Manzan Allah (s.a.w) ya ce da shi “Wane irin lokaci za ka dauka kana fada da Musulunci? Har yanzu lokacin da za ka karbi Addinin gaskiya bai yi ba?” Sai Sayyadina Umar (r.a) ya ce: “Hakika lokacin da zan karbi Addinin gaskiya ya yi. Na zo ne na yi imani”. Sai Manzan Allah (s.a.w) ya mikar da hannunsa shi kuma Sayyadina Umar (r.a) ya dora nasa a kan Na Manzan Allah (s.a.w) cikin ladabi sannan ya ce “Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Muhammadu Manzon Allah ne”.

Da jin haka sai Musulmi suka ce “Allahu Akbar” cikin jin dadi. Sai Manzan Allah (s.a.w) ya rungume shi, sannan sauran Musulmi ma suka rika rugumarsa daya bayan daya.

Sayyadina Umar (r.a) shi ne na arba’in (40) a shiga Musulunci. A wannan ranar da Sayyadina Umar ya Musulunta har Mala’ika Jibrilu (a.s) sai da ya taya Manzan Allah (s.a.w) murna saboda musuluntar sayyadina Umar (r.a). Ya ce da shi, “Ya Manzan Allah jama’ar Aljanna suna murna da musuluntar Umar (r.a) kuma suna mika sakon taya murna gareka”.

Sayyadina Umar (r.a) Saboda tsananin jin dadin musuluntar da ya yi saida ya rika bi kwararo-kwararo sako-sako a Makkah yana shelanta Musuluntar sa.

Hijirar Sayyadina Umar[gyara sashe | gyara masomin]

Sakamakon tsanani yayi yawa daga wajen kafiran Makkah ne sai Annabi Muhammad(s.a.w) ya umarci sahabbai da suyi hijira zuwa birnin da ake kira Yathriba a wancan lokacin wanda daga bisani aka mayar dashi Madinah. Sai sahabbai suka runka bin dare suna sulalewa daga garin Makkah saboda gudun cutarwa daga kafiran Makka na wancan lokacin. Amma shi Sayyadina Umar a fili kuma da rana tsaka yayi tasa hijirar har ma yana fadin Ina wanda yake son matar sa ta zama bazawara ko yayansa su zama marayu? to ya zo ya hana ni Umar yai hijirar sa tare da rakiyar dan dan'uwan sa da kuma dan'uwansa Sa'id dan Zaidu

Rayuwar sa a Madina[gyara sashe | gyara masomin]

A Madinah kuwa, Umar (R.A) na daya daga cikin zaratan mayaka wadanda su kayi ruwa da tsaki wajen kare martabar Addinin Musulunci da ruguza abokan gaba wato Kafirai. Ya kusanci Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama har ya kai matsayin wazirinsa na biyu. A shekara ta uku bayan hijira sai Allah ya karrama shi da surukuta da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama inda Manzo ya nemi auren 'yarsa Hafsah, aka ba shi ita, aka daura masu aure, sai ta zama ita ce ta uku daga cikin matansa bayan rasuwar uwargidansa Khadijah. A wurare da dama Umar (R.A) ya dace da hukuncin Alkur'ani kafin saukarsa. Misali, Umar ne ya ba da shawarar kada Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya halarci sallar jana'iza a kan munafukai, kuma sai AlKur'ani ya sauka da aya da tai daidai da wannan hukuncin. Haka kuma Umar (R.A) ya bai wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shawarar ya hana mutane shiga gidansa, kuma Allah ya saukar da wahayi a kan haka. Shi ne kuma ya nemi a shamakance mata daga maza ta hanyar amfani da hijabi, sai Allah ya saukar da wahayi a kan haka. Ya bada shawarar a kashe fursunonin yaqin Badar, Allah ya karfafi ra'ayinsa a Suratul Ali Imran. Wadannan duka suna nuna irin kaifin basirarsa da kusancinsa ga Allah da sanin abin da Allah yake so da wanda ba ya so.

Khalifancin Sayyadina Umar (r.a)[gyara sashe | gyara masomin]

Taswirar daular Musulunci a zamanin Kalifancin Sayyadina Umar R.A

Sayyadina Abubakar (R.A) say ya ayyana wa Musulmi Umar a matsayin wanda zai gaje shi bisa ga shawararsu. Don haka da Abubakar ya Rasu nan take mutane su kayi masa mubaya'a kuma ya kama aiki. Wani muhimmin abinda ya kamata a sani game da khalifancin Umar (R.A) shi ne kwarjinin da yake da shi matuka a idon jama'a. Amma kuma duk da haka talakawa sun more a lokacin khalifancinsa, domin kuwa ya kasance yana kula da al'amuransu ta ko wane fanni. Bayan dai kulawarsa da tsayuwar addini. Umar (R.A) yana kulawa da jin dadin rayuwar jama'a da inganta lafiyarsu da gyaruwar tattalin arzikinsu da samun kwanciyar hankali da zaman lafiya a tsakaninsu, hakan yasa Umar (R.A) ya sanya wasu daga cikin Sahabban Manzon Allah suka zama Gwamnoninsa dan kula da jama'a da jin kokensu,tin daga lokacin ne aka samo asali na nada mukarraben gwamnati.

Irin kwarjinin da Umar (R.A) yake da shi a zukatan jama'a ya sanya wata mata ta yi barin cikinta a lokacin da ta samu labarin an kai kararta ga Sarkin Musulmi Umar. Wannan ya sanya Umar ya tara jama'a ya nemi shawararsu a kan wannan abinda ya faru don sanin ko diyya ta wajaba a kansa. Ya kuma yi aiki da ra'ayin Sayyadina Ali (R.A) na biyan diyyar jinjirin da aka rasa. Ba za mu yi mamakin wannan mata ba idan muka san cewa, manyan Sahabbai irin su Zubairu dan Awwam da Sa'adu dan Abu Waqqas sukan tafi wajen Umar da nufin gaya masa wata magana ko gabatar da wata bukata, amma su je su dawo ba su samu damar yin haka ba saboda kwarjininsa da ya cika masu fuska. Ibnu Abbas ma duk da irin kusancin da yake da shi ga Umar amma ya yi shekara daya yana son ya tambaye shi game da wata aya bai samu damar haka ba saboda kwarjininsa.

Wani wanzami kuma ya saki iska saboda tsoro a lokacin da Sarkin Musulmi Umar ya yi tari shi kuma yana yi masa aski. Umar (R.A) da kansa ya kan damu wani lokaci da yadda jama'a suke fargabarsa, har ma ya kan ce, Ya Allah! Ka san na fi tsoronka fiye da yadda su ke tsorona.

A game da kulawarsa da talakawa kuwa, Umar (R.A) ya shahara da ziyarar sa ido wadda yake yi a cikin dare yana sintiri a tsakanin hanyoyi da gidaje don sanin halin da kasarsa ta ke ciki. A cikin irin wannan ziyarar ne yake gano idan akwai barayi ko wasu miyagu ko mabarnata masu fakewa a cikin duhun dare su yi aikin assha watau aikin masha'a, ko kuma bako wanda bai samu masauki ba.

Kisan Sayyadina Umar (r.a)[gyara sashe | gyara masomin]

Makwancin Kalifa Umar a masallacin Annabi (s.a.w) Madina. Tagar farko daga dama tana nuna Kabarin Sa

A shekarar 144M. ne wani bawa bafarenshe maisuna Abu Lu'u lu'ul majusi ya kai hari kan Sayyaduna Umar (r.a). Dama ansha shirya kashe Umar watanni kafin aiwatar da kisan. Adaidai lokacin da Sayyaduna Umar yake jagorancin sallar Asuba ne maharin yazo da wuka ya daddabawa Sayyaduna Umar (r.a) har sau shida nakarshe ne ya daba masa ita a makogwaron sa. A kokarin sauran mutanen na ganin a kama maharin Lu'u Lu'u ne sai da ya raunata mutum goma sha biyu(12) . Daga baya shida ko tara na mutanen Allah ya karbi rayuwar su dalilin wannan raunin. Shima Lu'u lu'u daga bisani kashe kansa yayi. Sayyadina Umar ya rasu sakamakon raunukan da maharin wato Lu'u Lu'u (l.a) yayi masa bayan kwana uku. Wato ranar Laraba ta 26 ga watan Dhul Hijja shekara ta 23 bayan hijira. Da Umarnin Aisha ne aka binne mahaifin ta wato Sayyaduna Umar bin khatdab a cikin dakinta gefe kadan da Makwancin Annabi Muhammad (s.a.w) da kuma na Sayyadina Abubakar(r.a).

Iyalin Sayyadina Umar (r.a)[gyara sashe | gyara masomin]

Sayyadina Umar(A.S) Ya auri mata Tara ne a iya rayuwar sa. Yana da yaya goma sha hudu, goma maza hudu mata.

Farkon Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Umar a Makka cikin kabilar Banu Adi, wadda ke da alhakin yin sulhu a tsakanin kabilu. Mahaifinsa shi ne Khattab bn Nufayl, mahaifiyarsa kuwa ita ce Hantama bint Hisham, daga kabilar Banu Makhzum .A lokacin kuruciyarsa, ya kasance yana kiwon rakuman mahaifinsa a wani fili kusa da Makka.Mahaifinsa dan kasuwa ne ya shahara saboda hazakarsa a cikin kabilarsa. Umar da kansa ya kan ce: “Babana, al-Khattab, mutum ne mara tausayi.Ya kasance yana sa ni aiki tukuru; idan ban yi aiki ba ya kan yi mini duka, kuma ya kasance yana sani aiki har na gaji.”

Duk da karance- karance ba a saba gani ba a Jahar kafin zuwan Musulunci, Umar ya koyi karatu da rubutu tun yana matashi.Ko da yake ba mawaƙi ba ne shi , ya kasance yana son waƙa da adabi . Kamar yadda al'adar Kuraishawa ta nuna, Umar tun yana matashin sa ya koyi sana'ar yaki da hawan doki da kokawa .Ya kasance dogo ne, mai karfin jiki kuma sanannen dan kokawa. [1] Ya kuma kasance dan baiwa a zance wanda ya gaji mahaifinsa a matsayin mai sasantawa a tsakanin kabilu.

Umar ya zama dan kasuwa kuma ya yi tafiye-tafiye da dama zuwa Rum da Farisa, inda aka ce ya hadu da malamai daban-daban kuma ya yi nazari kan al'ummomin Rumawa da Farisa .A matsayinsa na dan kasuwa ya kasance bai yi nasara ba. [1] Kamar sauran na kusa da shi, Umar ya kasance yana sha’awar shaye- shaye a zamaninsa na jahiliyya.

Farkon aikin soja[gyara sashe | gyara masomin]

Adawa da Musulunci[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin shekara ta 610, Muhammadu (s.a.w) ya fara wa'azin kira zuwa ga Musulunci.Duk da haka, kamar sauran mutane da yawa a Makka, Umar ya yi adawa da Musulunci har ma ya yi barazanar kashe Muhammadu.Ya kuduri aniyar kare addinin mushrikan Larabawa na gargajiya .Ya kasance mai tsayin daka da zalunci wajen adawa da Muhammadu, kuma ya yi fice wajen tsananta wa Musulmai. Ya bada shawarar kashe Muhammad. Ya yi imani da hadin kan Quraishawa, kuma yana ganin sabon addinin Musulunci a matsayin sababin rarrabuwa da sabani. [2]

Saboda tsanantawa, Muhammadu ya umurci wasu mabiyansa da su yi hijira zuwa Abyssiniya.Lokacin da wasu tsirarun musulmai suka yi hijira, Umar ya damu da hadin kan Quraishawa a nan gaba, kuma ya yanke shawarar a kashe Muhammad.

Komawa zuwa Musulunci da hidima karkashin Muhammadu[gyara sashe | gyara masomin]

Umar ya musulunta a shekara ta 616, shekara daya bayan hijira zuwa Habasha.An kawo labarin a cikin Sirah na Ibn Ishaq .A hanyarsa ta zuwa kashe Muhammad, Umar ya gamu da babban amininsa Nu'aym bn Abd Allah wanda ya musulunta a asirce amma bai gaya wa Umar ba.Da Umar ya ba shi labarin cewa ya yi niyyar zai je ya kashe Muhammadu, Nu’aym ya ce: “Wallahi ka yaudari kanka ya Umar!Kana tsammanin Banu Abd al-Manaf zasu bar ka da rai kana yawo da zarar ka kashe ɗansu Muhammad?Me ya sa ba za ka koma gidanku ba, ka daidaita shi a ƙalla?”

Nuaimal Hakim ya ce masa ya tambayi gidansa inda yayarsa da mijinta suka musulunta.Da isarsa gidanta, Umar ya tarar da kanwarsa da kuma surukinsa Saeed bin Zaid (dan baffan Umar) yana karatun ayoyin Alqur'ani daga suratu Ta-Ha . sai ya fara husuma da surukinsa.Sa’ad da ‘yar’uwarsa ta zo ta ceci mijinta, sai itama ya soma rigiman da ita.Amma duk da haka suka ci gaba da cewa "za ka iya kashe mu amma ba za mu bar Musulunci ba".Jin wannan maganar, sai Umar ya mari kanwarsa da karfi har ta fadi kasa tana zubar da jini daga bakinta.Da yaga abin da ya yi wa ‘yar uwarsa, sai ya huce saboda laifin da ya aikata, sai ya ce ma ‘yar uwarsa ta ba shi abin da take karantawa.'Yar'uwarsa ta amsa, da cewa, "Kai marar tsarki ne, kuma ba mai ƙazanta da zai iya taɓa Nassi."Ya dage amma yayarsa bata shirya ta barshi ya taba shafukan ba sai dai idan ya wanke jikinsa.Daga karshe Umar ya yarda.Ya wanke jikinsa sannan ya fara karanta ayoyin da ke cewa: Lallai ni ne Allah: babu abin bautawa da gaskiya sai Ni; Sabõda haka ku bauta Mini, kuma ku tsayar da salla dõmin ambatoNa (Alƙur´ãni 20:14).Sai ya yi kuka ya ce, “Hakika wannan maganar Allah ce.Ina shaidawa Lallai Muhammadu Manzon Allah ne”.Da Jin haka, sai Khabbab ya fito daga ciki ya ce: “Ya Umar!Albishir a gare ka.Jiya Muhammad ya roki Allah, 'Ya Allah!Ka Qarfafa Musulunci da Umar ko Abu Jahal, duk wanda Kake so acikin su.Kamar dai an karɓa masa addu’arSa da kai ne .”

Daga nan sai Umar ya je wurin Muhammad da takobin da ya yi niyyar kashe shi da shi, sai ya karbi Musulunci a gabansa da sahabbansa.Umar ya kasance yana da shekara 39 a duniya lokacin da ya musulunta.

A cewar wani labari, bayan musuluntar sa, Umar yana Sallah a fili a dakin Ka'aba kamar yadda aka ruwaito shugabannin Quraishawa, Abu Jahl da Abu Sufyan, suna kallon sa cikin fushi . Wannan kuma ya kara taimakawa musulmai wajen samun kwarin gwiwa wajen aiwatar da Musulunci a fili.A wannan mataki Umar ya ma kalubalanci duk wanda ya kuskura ya hana musulmai yin sallah, duk da cewa babu wanda ya kuskura ya yi wa Umar katsalandan a lokacin da yake salla a bayyane.

Musuluntar Umar ya baiwa musulmai iko da karfi kuma imanin Musulunci a Makka.Bayan faruwar wannan ne musulmai suke gudanar da salloli a bayyane a masallacin Harami a karon farko.Abdullahi Ibn Masud yace:

Hijira zuwa Madina[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin shekara ta 622 CE, saboda amincin da Yathrib (daga baya aka sake masa suna Medinat an-Nabī, ko kuma Madina kawai), Muhammad ya umurci mabiyansa su yi hijira zuwa garin Madina.Mafi yawan musulmai sun yi hijira da daddare ne saboda tsoron turjiya daga Quraishawa, amma an ruwaito Umar ya fita a fili da rana yana cewa: "Duk wanda yake son ya mayar da matarsa bazawara, 'ya'yansa marayu to ya zo ya same ni a bayan wannan dutse." Umar ya yi hijira zuwa Madina tare da rakiyar kaninsa kuma surukinsa Saeed bn Zaid . [3]

Rayuwa a Madina[gyara sashe | gyara masomin]

Takobin Umar

Lokacin da Muhammadu ya isa Madina, sai ya hada kowane dan hijira ( Muhajir ) da daya daga cikin mazaunan garin ( Ansari ), ya hada Muhammad bn Maslamah tare da Umar, ya mai da su ‘yan uwa a musulunci.Daga baya a zamanin Umar a matsayin sa na khalifa, Muhammad bn Muslamah za a nada shi ofishin Babban insifecta na Accountability.Musulmai sun zauna lafiya a Madina kusan shekara guda kafin Quraishawa su kafa runduna ta kai musu hari.A shekara ta 624, Umar ya halarci yakin farko tsakanin musulmai da Quraishawa na Makka, watau yakin Badar .A shekara ta 625, ya halarci yakin Uhudu .A kashi na biyu na yakin, a lokacin da dakarun dawakan Khalid bn Walid suka far wa musulmai na baya-bayan nan, inda suka karkata akalar yakin, aka yi ta yada jita-jitar mutuwar Muhammad, aka fatattaki mayakan musulmai da dama daga fagen fama, Umar yana cikinsu.Amma da jin cewa Muhammadu yana raye, sai ya je wurin Muhammad a dutsen Uhud ya shirya domin kare dutsen. Daga baya kuma a cikin shekarar Umar ya kasance wani bangare na yaki da kabilar Banu Nadir yahudawa .A shekara ta 625, aka aurar da ‘yar Umar Hafsah ga Muhammad. Daga baya a shekara ta 627, ya halarci yakin mahara da kuma yakin Banu Qurayza . A shekara ta 628, Umar ya shaida yarjejeniyar Hudaibiyyah . [4]A cikin 628, ya yi faɗa a yakin Khaybar .A shekara ta 629, Muhammadu ya aika Amr bn al-A'as zuwa Zaat-ul-Sallasal, bayan haka, Muhammad ya aiki Abu Ubaidah bn al-Jarrah da wasu dakaru da suka hada da Abubakar da Umar, inda suka kai farmaki suka fatattaki makiya. A shekara ta 630, lokacin da sojojin musulmai suka yi gaggawar buge Makka, yana cikin wannan rundunar.Daga baya a shekara ta 630, ya yi yakin Hunain da kewayen Ta'if .Yana cikin rundunar musulmai da suka fafata yakin Tabouk karkashin jagorancin Muhammad, kuma an ruwaito cewa ya bayar da rabin dukiyarsa domin shirya wannan balaguro.Ya kuma halarci aikin Hajjin bankwana na Muhammad a shekara ta 632.

Wafatin Annabi Muhammad[gyara sashe | gyara masomin]

Lokacin da Muhammadu ya rasu ranar 8 ga watan Yuni, shekarar 632 Umar ya karyata da farko cewa ya rasu. An ce Umar ya yi alkawarin sare kan duk mutumin da yace Muhammadu ya rasu.Umar ya ce: “Bai mutu ba, sai dai ya tafi zuwa ga ubangijinsa ne kamar yadda Annabi Musa (A.S) ya tafi, ya bar mutanensa da dare arba’in bayan ya koma wurinsu.Wallahi manzon Allah hakika zai dawo kamar yadda Musa ya koma (zuwa ga mutanensa) kuma sai ya yanke hannaye da kafafuwan wadanda suka yi ikrarin ya rasu.” Sai Abubakar ya fito fili ya yi magana da jama’a a cikin masallaci, yana mai cewa:

" Ya Umar, kazauna. Se yace, Ya ku mutane!!! Wanda Allah yake bautawa, muna sheda muku Allah baya mutuwa, amma Wanda yake bautawa Muhammadu (SAW) to hakika muna sheda masa yau kam ya Rasu ya bar Duniya.

[5] Da jin haka sai Umar ya durkusa kan gwiwowinsa cikin baqin ciki da yarda.Musulmai Ahlus-Sunnah sun ce wannan musun mutuwar Muhammadu ya faru ne saboda tsananin kaunarsa gare shi. [6]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named haykal-ch1
  2. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named haykal-p51
  3. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named Tahthib 2002 page 170
  4. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named Maghazi
  5. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named http://sunnah.com/bukhari/62/19
  6. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named Suyuti54-61