Karnataka

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Mysore Palace Morning.jpg

Fadar Mysore

7th - 9th century Hindu and Jain temples, Pattadakal monuments Karnataka 5.jpg

Pattadakal

Brindavan Gardens.JPG

Lambun Brindavan

Karnataka (lafazi|kn|Karnāṭaka) jiha ce dake a kudu maso yammacin yankin Indiya. An kirkireta ne a 1 November 1956. Asalin sunan jihar shine Jihar Mysore, Sai aka canja sunan zuwa Karnataka a 1973. Jihar na daidai ne da Yankin Carnatic. Babban birnin jihar itace Bangalore (Bengaluru) kuma itace birni mafi girma a jihan.

Karnataka nada iyaka da Kogin Arebiya ta yamma, Goa ta arewa maso yamma, Maharashtra ta arewa, Telangana ta arewa maso gabas, Andhra Pradesh ta gabas, Tamil Nadu ta kudu maso gabas, da kuma Kerala ta kudu. Jihar nada girman kasa da yakai 191,976 square kilometreகள் (74,122 sq mi), ko kashi 5.83 na adadin girman ƙasan Indiya. Haka yasa takasance ta shida a girman jihohin dake a ƙasar indiya. Tana da adadin yawan alumma 61,130,704 a ƙidayar shekara ta 2011, kuma Karnataka itace jiha na takwas a yawan alumma a indiya, tana da gundumomi 30. Kannada, daya daga cikin classical languages dake Indiya, itace yaren da akafi amfani dashi a jihar kuma yaren Jihar tareda yarukan Konkani, Marathi, Tulu, Tamil, Telugu, Malayalam, Kodava da kuma Beary. Karnataka kuma na dauke da daya daga cikin Ƙauyuka a Indiya waɗanda yaren Sanskrit kawai ake amfani dashi.[1][2][3]

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]