Jump to content

Lagos (jiha)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Jihar Legas)
Lagos
Lagos State (en)
Ìpínlẹ̀ Èkó (yo)


Suna saboda Lagos,
Wuri
Map
 6°35′N 3°45′E / 6.58°N 3.75°E / 6.58; 3.75
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Ikeja
Yawan mutane
Faɗi 11,000,598 (2016)
• Yawan mutane 3,075.37 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 3,577 km²
Wuri a ina ko kusa da wace teku Tekun Guinea da Lagos Lagoon
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Ƙirƙira 1472Port settlement (en) Fassara
27 Mayu 1967
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa Majalisar Zartaswa ta Jihar Legas
Gangar majalisa Lagos State House of Assembly
• Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu (29 Mayu 2019)
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2 NG-LA
Wasu abun

Yanar gizo lagosstate.gov.ng
Jihar lagos
Cikin Birnin Lagos

Jihar Lagos jiha ce da ke kudu maso yammacin Najeriya. Acikin duka jihohin Najeriya, itace jiha mai Mafi yawan jama'a, Kuma itace mafi banbanta ta fuskar

Girma. Ta hada iyaka da daga kudu da Bight of , daga yamma kuwa da iyaka na kasa da kasa da Jimhurriyar Benin, Jihar Legas ta hada iyaka da Jihar Osun daga gabas da kuma yamma wanda hakan ya sanya ta zamo jiha kadai da ta hada iyaka da wata jiha daga bangarori guda biyu. Ta samo sunanta daga babban birnin na Legas, wanda itace birni mafi girma ta fuskar yawan jama'a a Afirika. Jihar ta samo asali ne daga Jihar Yammacin Najeriya kuma tsohuwar Babban Birnin Najeriya a ranar ashirin da bakwai 27, ga watan Mayun shekara ta dubu daya da dari tara da sittin da bakwai 1967.

Ta fuskar yanayin kasa, Jihar mamaye take da ruwaye wadanda suka mamaye adalla Kason uku cikin hudu na fadin jihar wanda suka hada suka hada da ta kuna, creek da kuma koguna. Mafi girmansu sune tafkin lagoon dake Legas da kuma Lekki a yankin cikin garin inda ruwa daga kogin Osun da na Ogun ke kwararar a cikinsu. Koramu da tafkuna da dama na kwarara a cikin garin kuma suna cikin muhimman hanyoyin sufuri na mutane da kaya a jihar. Akan kasa kuwa, akwai kauyuka da dama a yankunan barin jihar wadanda ke da dabbobi da suka fara kwarewa kaman birrai nau'in Mona, tree pangolin, angulu da sauran tsirarun nau'ikan giwayen Afirka a dazukan. Acikin ruwa kuwa akwai dabbobi iri-iri wadanda suka hada da dabbar African manatee da kadoji.

Kabilu da dama ne ke zaune a Jihar Legas na tsawon shekaru tare da kabilar Yarbawa a matsayin asalin mazauna garin wadanda ke zaune a ko ina a fadin jihar tare da mutanen Ewe da Mutanen Ogu daga can kuryar yammacin jihar. A dalilin hijira da ya wanzu tun a karni na 19, mutane iri iri 'yan asalin Najeriya da kasahen kewaye ke zaune a yankin kamar Mutanen Edo, Fulani, Hausawa, Igbo, Mutanen Ijaw, Mutanen Ibibio da Nufawa da dai sauransu. Har wayau akwai kabilu daga kasashen wajen Najeriya ta yau wnda suka hada da Saro (Mutanen kasar Sierra Leone) da kuma Amaro (Mutanen Brazil) da ke zaune a Najeriya wadanda iyalai ne na bayi da suka dawo Afirka a karni na dubu daya da dari takwas 1800. Tare da sauran 'Yan gudun hijira na kwanannan daga yankunan kasashen Sin, Ghana, Indiya, Togo da kuma Birtaniya wadanda ke taka muhimmin rawa a bangaren bunkasar yawan mutanen jihar. Ta fuskar addinai kuwa, Jihar ta rarrabu tsakanin kaso Hamsin da biyar 55% a Matsayin kiristoci, musulmai kuma Kusan kimanin kaso arba'in 40%, da kuma kaso biya 5% wadanda ke bin addinan gargajiya ko wani hakan.

Tana da yawan fili kimani na kilomita araba’in 3,577, da yawan jama’a miliyan sha bakwai da dubu dari biyar da hamsin da biyu da dari tara da arba'in (jimillar shekarar dubu biyu da sha biyu 2012). Babban birnin tarayyar jahar ita ce Legas. Babajide Sanwo-Olu, shi ne gwamnan jihar tun zaben shekara ta dubu biyu da sha biyar 2015, har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Oluranti Adebule. Dattijai a jihar sun hada da: Bola Tinubu, Oluremi Tinubu, Solomon Olamilekan Adeola da Gbenga Bareehu Ashafa.

Kasuwar kayan miya a lagos

kananan Hukumomi.

[gyara sashe | gyara masomin]
Fayil:Ojota Lagos sha biyu(21).jpg
Lagos

Jihar Lagos ta rabu gida Biyar (5) wurin rabe-raben ayyuka, wadanda suka kara rabuwa zuwa kananan Hukumomi ashirin (20). Sune:[1]

Sunan Karamar hukuma Fadin kasa (km2) Kidayar Jama'a
ta dubu biyu da shida 2006
Cibiyar Karamar hukuma Lambar
Aika Sako
Agege 11 459,939 Agege 100
Alimosho 185 1,277,714 Ikotun 100
Ifako-Ijaye 27 427,878 Ifako 100
Ikeja 46 313,196 Ikeja 100
Kosofe 81 665,393 Kosofe 100
Mushin 17 633,009 Mushin 100
Oshodi-Isolo 45 621,509 Oshodi/Isolo 100
Shomolu 12 402,673 Shomolu 101
Ikeja Division 424 4,801,311
Apapa 27 217,362 Apapa 101
Eti-Osa 192 287,785 Ikoyi 101
Lagos Island 9 209,437 Lagos Island 101
Lagos Mainland 19 317,720 Lagos Mainland 101
Surulere 23 503,975 Surulere 101
Lagos Division 270 1,542,279
Ajeromi-Ifelodun 12 684,105 Ajeromi/Ifelodun 102
Amuwo-Odofin 135 318,166 Festac Town 102
Ojo 158 598,071 Ojo 102
Badagry 441 241,093 Badagry 103
Badagry Division 746 1,841,435
Ikorodu 394 535,619 Ikorodu 104
Ikorodu Division 394 535,619
Ibeju-Lekki 455 117,481 Akodo 105
Epe 1,185 181,409 Epe 106
Epe Division 1,640 298,890
Total 3,474 9,019,534 Ikeja

Sha shidan (16) farko na sunayen dake sama, sun kunshi wurare ne daga cikin garin birnin Lagos. Sauran kananan hukumomi hudun (4) kuma, wato (Badagry, Ikorodu, Ibeju-Lekki ds Epe) suna daga Jihar ne, amma ba daga cikin garin Birnin Lagos ba.

A shekara ta dubu biyu da uku 2003, yawancin kananan hukumomi ashirin (20) dake nan a yanzu, an rarraba su domin harkokin gudanar da aiki zuwa Local Council Development Areas. Wadanda sune a yanzu adadin su ya kai hamsin da shida 56, sune: Agbado/Oke-Odo, Agboyi/Ketu, Agege, Ajeromi, Alimosho, Apapa, Apapa-Iganmu, Ayobo/Ipaja, Badagry West, Badagry, Bariga, Coker Aguda, Egbe Idimu, Ejigbo, Epe, Eredo, Eti Osa East, Eti Osa West, Iba, Isolo, Imota, Ikoyi, Ibeju, Ifako-Ijaiye, Ifelodun, Igando/Ikotun, Igbogbo/Bayeku, Ijede, Ikeja, Ikorodu North, Ikorodu West, Ikosi Ejinrin, Ikorodu, Ikorodu West, Iru/Victoria Island, Itire Ikate, Kosofe, Lagos Island West, Lagos Island East, Lagos Mainland, Lekki, Mosan/Okunola, Mushin, Odi Olowo/Ojuwoye, Ojo, Ojodu, Ojokoro, Olorunda, Onigbongbo, Oriade, Orile Agege, Oshodi, Oto-Awori, Shomolu, Surulere and Yaba.[2]

  1. "Lagos State - Population". Archived from the original on 2011-06-15. Retrieved 2018-12-18.
  2. "Local Government Areas". Archived from the original on 2010-03-24. Retrieved 2010-03-20.


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara