Yobe
Yobe | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Suna saboda | Komadugu Yobe | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Damaturu | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 3,294,137 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 72.4 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 45,502 km² | ||||
Wuri a ina ko kusa da wace teku | Komadugu Yobe | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Jihar Borno | ||||
Ƙirƙira | 27 ga Augusta, 1991 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | executive council of Yobe State (en) | ||||
Gangar majalisa | Majalisar dokokin Jihar Yobe | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-YO | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | yobestate.gov.ng |
Yob Arewacin Najeriya Yobe jiha ce daga cikin jerin jihohin shiyyar Arewa[1] Maso Gabashin Najeriya.[2] [3]Tana da yawan kasa kimanin murabba'in kilomita 45,502 da yawan jama’a miliyan ɗaya da dubu dari hudu da sha- daya da dari hudu da tamanin da ɗaya "1,411,481" (a kidayar yawan jama'a ta shekarar 1991).[4] [2]Babban birnin jihar shi ne Damaturu. Mai Mala Buni[5] shi ne gwamnan jihar tun zaɓen shekara ta dubu biyu da goma sha biyar 2015 zuwa yau[6]. Mataimakin[7] gwamnan shi ne Idi Barde Gubana[8].Jihar dai tana da bangarori guda uku: bangaren gabas, kudu da kuma arewa[7].'yan majalisar Dattijan jihar su ne: Ahmed Ibrahim Lawan[9] mai wakiltar shiyyar arewaci, Bukar Abba Ibrahim Ibrahim Gaidam[10] shiyyar gabashi da, Ibrahim Mohammed Bomai shiyyar kudanci.
Jihar Yobe tana da iyaka da jihohi hudu, Kamar haka: Bauchi, Borno, Gombe da kuma Jigawa. Tana kuma da iyaka da jamhuriyar Nijar.[3]
TARIHI
[gyara sashe | gyara masomin]An kirkiri jihar Yobe ne a ranar 27 ga watan Agustan 1991.[11] An ciro ta ne daga jihar Borno a zamanin mulkin Ibrahim Badamasi Babangida kuma an yi hakan ne don a sauƙaƙa sha'anin tafiyar da mulki a yankin. Ranar 14 ga watan Mayun 2013, Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya rattaba dokar ta baci a jihar Yobe da Borno da kuma Adamawa. Saboda harin ta'addanci na kungiyar Boko Haram . Karkashin Abubakar Shekau, shugaban kungiyar ta Boko Haram, haifaffen kauyen Shekau ne na jihar Yobe.
Kananan Hukumomi
[gyara sashe | gyara masomin]Jahar Yobe tana da kananan hukumomi guda goma sha bakwai (17) wadanda suka hada da:
Harsuna
[gyara sashe | gyara masomin]Wadannan su ne harsunan mutanen Jihar da kuma kananan hukumomin da ake samun su:[12]
Kananan Hukumomi | Harsuna |
---|---|
Bade | Bade; Duwai |
Bursari | Fulbe Bade |
Damaturu | Kanuri; Fulani |
Fika | Karaikarai; Ngamo; Fulani Bolewa |
Fune | Fulani,Abore |
Geidam | Kanuri |
Gujba | Fulani,Kanuri, |
Gulani | Maaka, Fulani |
Jakusko | Fulani, Bade, |
Nangere | Karai-karai da fulani |
Nguru | Kanuri; Hausa; Bade |
Potiskum | Karai-karai, Ngizimawa, bolawa |
Tarmuwa | Fulani, kanuri |
Yunusari | Kanuri, Fulani |
Yusufari | Kanuri, Fulani |
Machina | Mangawa |
Sauran harsunan da ake samu a jihar Yobe sun haɗa da Baburawa, Mangawa da kuma Zarmawa da kuma Fulani da kuma ngizim da kuma Kare-kare.[12]
Jami'o'i na Jihar
[gyara sashe | gyara masomin]- Yobe State University
Hotunan wasu sassa na Yobe
[gyara sashe | gyara masomin]-
Yobe state railway
-
Yobe state government
-
Yobe river
-
yobe station
-
Yobe river transportation
Fitattun mutane a jihar
[gyara sashe | gyara masomin]- Bulama Bukarti - Lauya mai kare hakkin dan Adam.
- Usman Albishir - (15 Yuni 1945 – 2 Yuli 2012) tsohon Sanata kuma shugaban marassa rinjaye a Majalisar Dattawa.
- Mai Mala Buni - (an haife shi a ranar 11 ga watan Nuwambar 1967) ɗan siyasa, tsohon sakataren jam'iyyar APC na ƙasa kuma Gwamnan jihar Yobe na yanzu.
- Ibrahim Gaidam, Dan Siyasa ne Kuma shine tsohon gwamnan jihar Yobe kuma a yanzu dan majalisar dattawa mai wakiltar shiyyar gabashin jihar a Majalisar Dattawa.
- Buba Galadima - Dan siyasa kuma sakataren kasa na tsohuwar jam'iyyar "Congress for Progressive Change (CPC)" .
- Bukar Ibrahim - (shekarar haihuwa Aktoba 1950) tsohon gwamnan jihar Yobe kuma tsohon dan takarar shugabacin kasa a jam'iyyar NNPP a shekarar 2007.
- Khadija Bukar Abba Ibrahim - (shekarar haihuwa 6 Janairu 1967) matar tsohon gwamnan jihar Yobe Bukar Abba Ibrahim, tsohuwar 'yar majalisar wakilai na tarayya kuma Ministar kasa mai kula da harkokin waje karkashin jagorancin Muhammadu Buhari .
- Ahmed Ibrahim Lawan - Sanata[13] tun daga shekarar 1991 kuma shugaban majalisar dattawan Najeriya a yanzu kuma shi ne mutum na 9 a shugabannin majalisar kasar.
- Ibrahim Talba - Dan siyasa kuma tsohon babban sakataren gwamnati a fadar shugaban kasa lokacin mulkin Olusegun Obasanjo kuma Ciroman masarautar Tikau.
- Adamu Waziri - (shekarar haihuwa 14 Satumba 1952) dan siyasa kuma tsohon dan takarar gwamnan jihar Yobe a karkashin jam'iyyar PDP kana tsohon ministan 'yan sanda na kasa kuma tsohon ministan jami'an kula da lafiyar hanya.
- Jamila Babayo - (shekarar haihuwa 17 Mayu, 1983) marubuciya ce da ta kasance mace ta farko a shiryar Arewa Maso Gabashin Najeriya da ta lashe gasar rubutu ta mata zallah ta BBC Hausa.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://dailypost.ng/%3Fp%3D1105568&ved=2ahUKEwjjpL316_GGAxVbWkEAHcp4CFoQxfQBKAB6BAgSEAI&usg=AOvVaw2hNyZSchhjf_x_lnUEDVJx
- ↑ 2.0 2.1 https://www.britannica.com/place/Yobe
- ↑ 3.0 3.1 https://www.britannica.com/place/Yobe
- ↑ https://euaa.europa.eu/country-guidance-nigeria-2021/yobe
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://guardian.ng/please-mai-mala-buni-leave-that-abuja/&ved=2ahUKEwiv8OiX7PGGAxWnW0EAHTikDSYQxfQBKAB6BAgNEAI&usg=AOvVaw22VSRRRY-f3yylKW_Rmpwe
- ↑ https://www.bing.com/ck/a?!&&p=ee9ea83e917a8ea6JmltdHM9MTcxOTAxNDQwMCZpZ3VpZD0yNDE5NGEyMS03NTBiLTZiYjItMzNmMi01ZTg1NzRhMTZhMTkmaW5zaWQ9NTIyOA&ptn=3&ver=2&hsh=3&fclid=24194a21-750b-6bb2-33f2-5e8574a16a19&psq=Mai+Mala+Bun&u=a1aHR0cHM6Ly95b2Jlc3RhdGUuZ292Lm5nL2Fib3V0LTMv&ntb=1
- ↑ 7.0 7.1 7.2 "Yobe State of Nigeria :: Nigeria Information & Guide". www.nigeriagalleria.com. Retrieved 6 March 2022.
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://dailytrust.com/why-yobe-is-deboarding-public-schools-deputy-gov/&ved=2ahUKEwjFqMTC7PGGAxWBWUEAHUhXCWcQxfQBKAB6BAgKEAI&usg=AOvVaw0lgtr92RYqI6ZJxOzYKHpI
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://dailypost.ng/2024/06/12/ex-senate-president-lawan-seeks-prayers-for-tinubu-to-succeed/&ved=2ahUKEwiyq8_w7PGGAxUobEEAHYV8B98QxfQBKAB6BAgPEAI&usg=AOvVaw0KLNk01Uorkl2kr22CRRAv
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://championnews.com.ng/minister-of-police-affairs-sen-gaidam-congratulates-president-bola-tinubu-on-supreme-court-victory/&ved=2ahUKEwj_zMmT7fGGAxXmSEEAHRB9A7cQxfQBKAB6BAgHEAI&usg=AOvVaw0zg9sCGpZT906spTXnTlqB
- ↑ "Climate: Yobe in Nigeria". Worlddata.info (in Turanci). Retrieved 25 November 2022.
- ↑ 12.0 12.1 "Nigeria". Ethnologue (22 ed.).
- ↑ https://hausa.legit.ng/news/1558641-mahaifiyar-sanata-ahmed-lawan-ta-riga-mu-gidan-gaskiya-a-jihar-yobe/
Jihohin Najeriya |
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara |