Jump to content

Babban shafi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Muƙalar mu a yau
Muhammadu Bello
Muhammed Bello (Larabci: محمد بلو) Shi ne sarki na biyu. Sarkin Musulmi ya yi mulki daga shekara ta alif ɗari takwas da sha bakwai 1817A.c, har zuwa shekara ta alif ɗari takwas da talatin da bakwai 1837A.c. Ya kasance marubucin tarihi ne wanda kuma ke da Ilimin addinin Musulunci. Ɗan Usman Ɗan Fodio ne kuma mai masa hidima, wanda shine ya kafa Daular Sokoto kuma shi ne Sultan (Sarkin Musulmi) na farko. Lokacin mulkinsa, ya ƙarfafa da'awar yaɗa Musulunci a dukkanin yankunan Ƙasar Hausa, da tsarin karantar da mata da maza, da kuma kafa kotunan Musulunci, Ya rasu a watan Octobar, a ranar 25, shekarar alif ɗari takwas da talatin da bakwai, 1837, ƙaninsa Abu Bakar Atiku ne ya gaje shi, daga nan sai ɗansa mai suna Ali Babba bin Bello ya gaji sarautar a gurin Abubakar Atiku.
Wikipedia:A rana irin ta yau 26 ga Yuni, A rana irin ta yau

Yau 23 ga Janairu na 2024 Ga wasu muhimman abubuwa na tarihi da suka faru a wannan rana.

  • A 2015, Sarki Salman na Saudiyya ya hau karagar sarautar Saudi Arabia bayan rasuwar tsohon sarkin kuma ɗan uwansa.
  • A 1973, aka yi yarjejeniyar Paris Peace Accord wadda ta kawo ƙarshen mamayar Amurka a yaƙin ƙasar Vietnam. Lamarin da yayi sanadiyar samuwar ƙasashen Vietnam, Laos da Kambodiya.
  • A 1556, akayi girgizar ƙasa a lardin Shaanxi, wanda ta kashe fiye da mutane 830,000 a Jihar Shaanxi, ta ƙasar Sin. Itace girgizar ƙasa mafi muni a tarihin Yankin.
  • A 1789, aka kafa Makarantar Katolika ta Georgetown ta farko.
  • A 2020, Sin ta rufe birnin Wuhan da wasu biranen kusa da ita, da suka shafi fiye da mutane miliyan 50, domin kare fitowar Sabuwar cutar Korona.
Ko kun san...?
  • Cententennial shine ƙwan fitila mafi daɗewa a duniya, yana ci tun 1901.
  • Gini mafi tsayi a duniya shine Burj Khalifa a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa. Yana tsaye a tsayin mita 828 (ƙafa 2,717).
  • Babbar Ganuwar Ƙasar Sin tana da nisan mil 13,170 (kilomita 21,196).
  • Rana a Venus ta fi shekara guda akan Venus? Venus tana jujjuyawa a kan kusurwarta a hankali, tana ɗaukar kwanaki 243 a duniya, amma tana ɗaukar kimanin kwanaki 225 ne kawai don kewaya rana.
  • Yaƙi mafi gajarta a tarihi shine tsakanin Birtaniya da Zanzibar a ranar 27 ga Agusta, 1896 Minti 38 kawai ya yi.
  • A ranar 8 ga watan Afrilu miliyoyin mutane suka kalli Husufin Rana a yankin Amurka.
  • A ranar 7 ga Afrilu 2024, Kasar Rwanda ta cika shekaru 30 da kisan kare dangi wanda yayi sanadiyar mutuwar dubban mutane.
  • Ƙasar Indonesiya ta bi sahun ƙasar Afirka ta Kudu wajen shigar da ƙasar Isra'ila ƙara a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya dake birnin Hague, bisa ga mamata da kisan gillar da ƙasar Isra'ila take yima Falasdinawa.
  • Tsohon Firaministan ƙasar Asturaliya Scott Morrison, ya fitar da sanarwar barin dukkanin harkokin siyasa.
  • Ƙungiyar Tarayyar Turai ta sake jadadda matsayar ta na samar da kasar Falasdinu mai cikakken iko kusa da Isra’ila, tana mai cewa wannan ita kadai ce hanyar da za’a kawo karshen rikicin da aka shafe shekaru ana gwabzawa.
  • Najeriya ta lallasa Guinea-Bissau da ci 1-0, a fafatawar da suka yi a gasar lashe kofin Afirka a filin wasa na Félix Houphouet-Boigny da ke Abidjan na kasar Ivory Coast, yayin da Gini Ikwatoriya ta lallasa mai masaukin baki Ivory Coast da ci 4-0.

Zaka iya duba babban shafin English Wikipedia
Hotan mu na yau

Hoton mu na wannan ranan

Ragaya, ma'ajiyar kayayyaki na al'adun Hausawa

Sautin mu na wannan ranan

Tamburan ban girma na Algaita

Problems playing this file? See media help.

Bidiyon mu na wannan ranan

Yayan masu mulkin gargajiya na Hausawa akan dawaki.

Yan uwan Wikimedia
Wikimedia Foundation
Wikiqoute
Azanci
Wikitionary
Ƙamus
Wikinews
Labarai
Wikisource Wikisource
Wikisource
Commons
Fayiloli
Wikidata
Wikidata
Wikibooks
Litattafai
Meta-Wiki Meta-Wiki
Meta
Shafuka na musamman

Hausa Wikipedia

domin Ƙirƙirar sabuwar maƙala ana iya rubuta sunan maƙalar a akwatin da ke ƙasa: Zuwa yau, muna da Maƙaloli 47,621