Delta (jiha)
Delta | |||||
---|---|---|---|---|---|
Delta State (en) | |||||
| |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Asaba | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 5,663,362 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 320 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 17,698 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Bendel State (en) | ||||
Ƙirƙira | 27 ga Augusta, 1991 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | Delta State Executive Council (en) | ||||
Gangar majalisa | Delta State House of Assembly (en) | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Lambar aika saƙo | 320001 | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-DE | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | deltastate.gov.ng |
Jihar Delta Jiha ce dake kudu maso kudancin Najeriya. Jihar ta samo sunanta ne daga yankin Niger Delta[1] - wacce mafi akasarinta ke cikin jihar. An kirkiri jihar ne daga yankin tsohuwar Jihar Bendel a ranar ashirin da bakwai 27 ga watan Agusta, shekara ta dubu daya da dari tara da cassa'in da daya 1991. Jihar Delta ta hada iyaka da Jihar Edo daga arewa, daga gabas kuma da jihohin Anambra da Rivers, sannan daga kudu kuma da Jihar Bayelsa, sannan daga yamma kuma da yankin Bright of Benin,[2] wacce ta mamaye a kalla kilomita dari da sittin 160 na yankin ruwayen garin. An kirkiri jihar ne daga farko da kananan hukumomi Sha biyar 15 a shekarar 1991 sai daga baya aka kara ta koma sha tara 19 sannan daga bisani kuma zuwa kananan hukumomi ashirin da biyar. Babban birnin Jihar itace Asaba wacce ke yankin Kogin Neje daga karshen arewa maso Gabashin jihar, a yayin da Warri ke taka rawa a matsayi cibiyar kasuwancin daga kudu maso yammacin gabar ruwan jihar.
Acikin jihohi talatin da shida 36 da ke a kasar Najeriya, Jihar Delta ita ce ta ashirin da uku a fadin kasa kuma ita ce ta sha biyu 12 a yawan jama'a da mutane kimanin miliyan biyar da dugo shida 5.6 a bisa kiyasin kidayar shekara ta dubu biyu da sha shida 2016.[3] Jihar, ta fuskar yanayin kasa ta kasu zuwa Mangrove na Afirka ta tsakiya daga yankin ruwa na kudu maso yamma da kuma dajika masu kwari irin na Najeriya wacce ta mamaye daukacin jihar da kuma dazuka masu fadama daga kuryar Kudancin jihar. Wani muhimmi al'amari a jihar sune gabar Kogin Neja da rassan sa da kuma Sauran ruwayen kaman Kogin Forçados wanda ke gudana daga yammaci da gabashin iyakokin Jihar Delta kuma ya fada Kogin Neja, da kuma Kogin Escravos wacce ke kwarara ta Warri sa'annan kuma yawancin yankunan ruwayen garin na dauke ne da dimbin dananan rafuka wadanda suka samar da akasarin yammacin Niger Delta. Mafi akasarin dabbobi da ake samu a yankin sun hada da; kadoji, tsuntsaye Parrot, nauyin kerkeci na African fish eagle, da birai na Mona, da kuma damisan Afirka, da kuma nau'in biran chimpanzee na Najeriya da Kamaru.[4][5]
Jihar Delta ta yau ta kunshi kabilu da dama na tsawon lokaci wanda suka hada da kabilar Isoko da Harshen Eruwa wanda suka mamaye yankunan tsakiyar jihar; kabilar Ukwuani daga gabas; yayinda kabilar Ika, Olukumi da kuma Ozanogogo suka mamaye arewa maso Gabashin jihar; Anioma daga arewa maso yamma; kabilu Ijaw, Itsekiri, Urhobo, da Uvwie daga yankin arewa maso yamma. Kafin zuwan Turawan mulkin mallaka, yankin Jihar Delta ta yau ta kasu zuwa masarautu masu mulkin kansu kamar su MasaraWarri da Masarautar Agbon kafin su zamo yankin mulkin mallakar Turawa na Oil River Protectorate a shekara ta dubu daya da dari takwas da tamanin da hudu 1884. A shekara ta dubu daya da dari tara 1900, Turawa sun hade yankin (wato Niger Coast Protectorate) da yankin Mulkin Mallakan Turawa na Kudu wacce daga bisani ta zamo Najeriya ta Burtaniya. Duk da haka, Turawan mulkin mallaka basu gama samun cikakken iko akan yankin ba sai a shekarar 1910 a dalilin rikice-rikicen Ekumeku Movement. Kamar yadda aka sani, acikin Jihar Delta akwai yankunan da ke karkashin ikon kasar Faransa wanda turawan Burtaniya suka sake wa Faransa Yankunan Forcados da Badjibo a tasakanin shekara ta 1903 zuwa shekara ta 1930.
Bayan samun 'yancin kai, yankin Jihar Delta ta yau na daga cikin yankin Jihar Yammacin Najeriya bayan samun 'yancin Najeriya, har zuwa shekarar 1963, lokacin da aka raba yankin kuma jihar ta fada karkashin Yankin Yamma ta Tsakiya ta Najeriya. Haka zalika a shekarar 1967 ne yankin Inyamurai watau tsohuwar Yankin Gabashin Najeriya ta suka so kafa sabuwar kasar Biyafara kuma suka kaiwa Yankin Yamma ta Tsakiya hari tare da nufin kame Jihar Lagos kuma su kawo karshen Yakin amma an hanasu kuma an kora su na dan lokaci amma daga baya suka kame yankin (harda Jihar Delta ta yau) suka rada mata suna Tarayyar Benin. Acikin wannan hali, anyi kazamin barna a tsakanin sojojin Biyafara da kuma mutane mazauna yankin Jihar Delta ta yau, tare da kisan gilla da 'yan Bifara ke yiwa 'yan ainihin kabilun Hausa, Urhobo da kuma Kabilar Ijaw; haka zalika, sojojin Najeriya a yayin amsar jihar sun gudanar da Kisan kiyashin Asaba ga mutanen asalin yaren Igbo. Yakin ya kawo karshe kuma an mayar da Yankin Yamma ta Tsakiya cikin Najeriya, har zuwa shekarar 1976 lokacin da aka sauya mata suna zuwa Jihar Bendel. A shekarar 1991, an raba Jihar Bendel, arewacinta ta zamo Jihar Edo, yayinda kudancinta ta zamo Jihar Delta.[6]
Tattalin arzikin jihar[7] sun ta'allaka ne akan samar da man fetur da gas, a matsayin daya daga cikin muhimman jihohin dake samar da man fetur a Nejeriya.[8] Kadan daga cikin muhimman masana'antun sun hada da noma yayin da jihar ke samar da isashhen manja, doya da rogo dangane da kamun/kiwon kifi da samar da fure. Dangane da albarkacin man fetur, jihar ita ce ta hudu acikin Jerin Jihohi Najeriya dangane da Ma'aunin Cigaban Jama'a a kasar; duk da haka, rikice-rikice tsakanin kamfanonin mai da kuma mutanen garin sun kawo cikas dangane da cin hanci da rashawa wanda suka janyo rashin ci gaba musamman a yankunan da ake hako man.[9][10]
Yanayin kasa
[gyara sashe | gyara masomin]Jihar na da fadin fili na kimanin 18,050 km2 (6,970 sq mi) wanda fiye da kashi 60% doron kasa ne. Jihar na nan a lambobin wuri a kalla 5°00' da 6°45' E da kuma 5°00'da 6°30' N.[11] Tana nan a Yankin Yamma ta Tsakiyan Najeriya kuma ta hada iyaka da Jihar Edo daga arewa, daga gabas kuma da jihohin Anambra da Rivers, sannan daga kudu kuma da Jihar Bayelsa, sannan daga yamma kuma da yankin Bright of Benin wanda ya mamaye kilomitoci 160km na yankin ruwan jihar. Jihar Delta na kan kwari ne ba tare da tudu ko guda ba. Akwai yankunan ruwa da dama a jihar wadanda suke hade da koramu wanda suka samar da yankin Kogin Niger Delta.[12]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]An kirkiri Jihar Delta ne daga tsohuwar Jihar Bendel a ranar 27 ga watan Augustan shekara ta 1991.[13] An samar da jihar ne a sanadiyyar riritawa don samar da jiha ta daban da mutanen ainihi na Gundumar Delta suka yi.[14] Haka zalika akwai bukata ta sabuwar jihar mai suna "Jihar Anioma" wanda ta hada da yankunan Asaba da Agbor na yankin tsohuwar Yankin Yamma ta Tsakiya.[15] Shugaban kasa soja na lokacin Gen. Ibrahim Babangida ya zaba Jihar Delta tare da Asaba wata shahararriyar birnin a yankin arewa maso yammacin Niger a matsayin babban birnin jihar. Jihar Delta ta kasance a da daga cikin Yankin Yamma ta Tsakiya daga shekarar ta 1963 zuwa ta 1976, daga bisani kum Jihar Bendel a tsakanin shekara ta 1976 zuwa shekaran ta 1991. Sunan "Bendel" ta samo asali daga tsaffin gundomomin Benin da Delta na Yankin Yammacin Delta don nuna muhimmancin gundumomin guda biyu (Benin da Delta).[16]
Mutane
[gyara sashe | gyara masomin]Mazauna Jihar Delta sun hada da kabilu kamar haka: Urhobo, Isoko, Ika, Aniocha-Oshimili, Itsekiri, da kuma Olukumi.[17]
Kabilar Urhobo-Isoko na da mafi rinjayen mutane kuma a yanzu akwai mutum akalla miliyan 2.6 a jihar.[18] Gungun yaruka na Iboid na jihar sun hada da Mutanen Anioma (mutanen gari mai kyau).[19] kabilar Itsekiri na amfani da yare mai kama da yarbanci amma yana da alaka da al'adun kabilar Edo na Jihar Edo, hadi da yarukan Urhobo da Ijaw. Kabilar Ijaw mutane ne masu alaka da makwabtansu na Jihar Bayelsa,[20] yayinda yaren Olukumi suka fara bacewa ta fuskar al'ada da yare,[21] a dalilin cudanya da wasu harsunan.
Gwamnati
[gyara sashe | gyara masomin]An zabi Arthur Okowa Ifeanyi, dan takara a karkashin jam'iyyar PDP a matsayin gwamnan Jihar Delta a cikin watan Afrilun 2015.[22] Mataimakinsa shi ne Kingsley Otuaro.[23] Jihar na da mazabu uku (Arewa, Kudu da Tsakiya). Sanatocin da aka zaba a zaben shekara ta 2011 zuwa shekara ta 2013 sune James Manager, Arthur Okowa Ifeanyi da kuma Emmanuel Aguariavwodo wanda ya maye gurbin Pius Ewherido wanda ya rasu a shekara ta 2013 a Asibitin Tarayya dake Abuja.[24] An zabi Chief Ighoyeta Amori a zaben shekara ta 2015, amma an soke nasa zaben kuma an rantsar da Sanata Ovie Omo-Agege a matsayin sanata mai wakiltar Delta ta Tsakiya.[25][25] James Manager ya koma kujerarsa kuma an zabi Peter Nwaoboshi a matsayin sanata mai wakiltar Arewacin jihar.
Gwamnatocin gaba da na baya
[gyara sashe | gyara masomin]- Ifeanyi Okowa - a ranar 29 ga watan Mayu shekaran ta 2015 har zuwa yau PDP[26]
- Emmanuel Uduaghan -a ranar 29 ga watan Mayun shekara ta 2007 zuwa 29 ga watan Mayun 2015 (PDP)[27]
- James Ibori - a ranar 29 Mayun 1999 zuwa 29 ga watan Mayun 2007 (PDP)[28]
- Walter Feghabo - a ranar 12 ga watan Augustan 1998 zuwa 29 ga watan Mayun 1999 (mulkin soja)
- John Dungs - 22 Augustan 1996 zuwa 12 Augustan 1998 (mulkin soja)
- Ibrahim Kefas - a ranar 26 ga watan Satumba 1994 zuwa 22 ga watan Agustan 1996 (mulkin soja)[29]
- Bassey Asuquo - a ranar 10 ga watan Disamba 1993 zuwa 26 Satumban 1994 (mulkin soja)[30]
- Abdulkadir Shehu - 17 November 1993 - 10 December 1993 (mulkin sojay)[31]
- Luke Chijiuba Ochulor - 28 August 1991 - January 1992 (mulkin soja)[32]
- Felix Ibru - January 1992 - November 1993 (SDP)[33]
Kananan Hukumomi
[gyara sashe | gyara masomin]Jihar Delta tana da adadin Kananan hukumomi guda ashirin da biyar (25), an kawo su a jere a jadawalin dake kasa tare da kasafin kidayar shekara ta 2006:
Shiyar Sanata na Tsakiyar Jihar Delta | 1,575,738 | Shiyar Sanata ta Jihar Delta ta Arewa | 1,293,074 | Shiyar Sanata ta Jihar Delta ta Kudu | 1,229,282 | ||
---|---|---|---|---|---|---|---|
Ethiope ta Gabas | 200,942 | Aniocha ta Arewa | 104,062 | Bomadi | 86,016 | ||
Ethiope ta Yamma | 202,712 | Aniocha ta Kudu | 142,045 | Burutu | 207,977 | ||
Okpe | 128,398 | Ika ta Arewa maso Gabas | 182,819 | Isoko ta Arewa | 143,559 | ||
Sapele | 174,273 | Ika ta Kudu | 167,060 | Isoko ta Kudu | 235,147 | ||
Udu | 142,480 | Ndokwa ta Gabas | 103,224 | Patani | 67,391 | ||
Ughelli ta Arewa | 320,687 | Ndokwa ta Yamma | 150,024 | Warri ta Arewa | 136,149 | ||
Ughelli ta Kudu | 212,638 | Oshimili ta Arewa | 118,540 | Warri ta Kudu | 311,970 | ||
Uvwie | 188,728 | Oshimili ta Kudu | 150,032 | Warri ta Kudu maso Yamma | 116,538 | ||
Ukwuani | 119,034 |
Kananan hukumomi da harsuna
[gyara sashe | gyara masomin]Harsunan Jihar Delta dangane da kananan hukumominsu:[34]
Albarkatun kasa
[gyara sashe | gyara masomin]Akwai ma'adanai iri-iri a jihar kamar su: industrial clay, silica, lignite, kaolin, tar sand, duwatsu na ado, limestone da dai sauransu.[35] Ana amfani da wadannan ma'adanai a ma'aikatu wajen hada ceramic, kwalba, gilasai, alli, wayoyi, da makamantansu.[36]
Har ila yau, akwai tarin arzikin man fetur a Jihar Delta, kuma tana daya daga cikin muhimman garuruwan da ke samar da kayan da ake hadawa daga man fetur a Najeriya. Tattalin arzikin jihar sun ta'allaka ne matuka a wajen cinikin man fetur.
Manyan Makarantu
[gyara sashe | gyara masomin]Makarantun gaba da sakandare na jihar sun hada da:[37]
- Federal University of Petroleum Resources Effurun[38]
- Delta State University[39]
- Delta State University of Science and Technology, Ozoro
- University of Delta, Agbor
- Delta State Polytechnics (Polytechnic guda biyu, daya a Oghara, daya a Ogwashi-Uku)[40][41]
- Makarantar wasan kwakwayo na Film and Broadcast Academy, Ozoro[42]
- Kwalejin Ilimi Warri.[43]
- Federal College of Education Technical, Asaba[44]
- Kwalejin Ilimi, Mosogar[45]
- Delta State College of Health Technology, Ughelli
- Petroleum Training Institute, Effurun[46]
- Western Delta University, Oghara[47]
- Novena University, Ogume-Amai[48]
- National Open University of Nigeria (three study centres, one at Asaba, one at Emevor and another at Owhrode).[49][50][51]
- Delta State School of Marine Technology, Burutu[52]
- Nigeria Maritime University, Okerenkoko, Warri[53]
- Conarina School of Maritime & Transport Technology, Oria-Abraka[54]
- University of Information and Communication Technology, Agbor[55]
- State School of Midwifery, Asaba[56]
- School of Nursing (two schools, one at Agbor and another at Warri)[57]
- Baptist School of Nursing, Eku[58]
- Edwin Clark University, Kiagbodo[59]
- Eagle Heights University, Omadino, Warri[60]
- Admiralty University of Nigeria at Ibusa and Sapele[61]
Wuraren bude idanu
[gyara sashe | gyara masomin]A Jihar Delta, akwai wuraren tarihi, al'adu da zamantakewa na siyasa, wuraren bude idanun da ke jan hankalin 'yan kallo daga ko'ina a fadin duniya.Wasu daga cikin wadannan wurare sun hada da:[25]
- Fadar Nana (The Nana's Palace) wanda Chief Nana Olomu na Ebrohim ya gina. Ya shahara a karni na 19, kuma dan kasuwa ne na garin da yayi hulda da turawa. Daga baya huldar ta baci. An mamaye daga baya (ba tare da anyi fada ba) sai suka koma kasar Ghana. Abubuwan da ya bari sun hada da katafaren fadar sa dake gidansa.[Ana bukatan hujja]
- Rafin Ethiope iwanda ake ikirarin cewa shine ruwa mafi zurfi acikin garuruwan Afurka (zurfi 176 km). Mabubbugar ruwan na kusa da wani katafaren bishiya silikin auduga dake Umuaja a karamar hukumar Ukwuani sannan tana kwararar ta kananan hukumomin jihar source is at the foot of a giant silk-cotton tree at Umuaja in Ukuami sannan su kwarara zuwa Sauran yan kananan hukumomin jihar. Wurin bauta ne na addinin gargajiya na Olokun sannan kuma wurin bautar na mabiya addinin Agbe.[62]
- Yankin Bible na Araya wanda ke dauke da kwafi na Littafin mai tsarki na Bible. An yarda da cewa Littafin Bible ya sauka a wannan yankin cikin al'ajabi daga sama a cikin watan Augusta, 1914. Littafin na bible ya sauko ne acikin wani jikakken doya daga ruwan sama amma bai jike ba. Yankin na janyo dubunnan mabiya addinin kirista duk shekara.[63]
- Demas Nwoko Edifice wanda aka gina da kayan aiki na gargajiya, tsari da salon gini na cigaban mutanen Igbo wanda Demas Nwoko wani mai zane, ma gini kuma mai fasaha na duniya daga garin Idumuje-Ugboko, a karamar hukumar Aniocha ta Arewa, Jihar Delta.[64]
- Gidan shakatawa na "Mungo Park House" wanda a yanzu Gidan Tarihi ne na Kasa, a Asaba. Royal Niger Company suka gina gidan a shekara ta 1886 kuma turawa sunyi amfani dashi a matsayin hedikwatan, gidan sojojin, hedikwatan gidan Gwamnatin turawa, gindin RNC, da kuma mazauni Gundumar Birni a lokuta daban daban.[65]
- Gabar tekun Ogulagha Beach
- Gadar Niger Bridge wacce ta hade Jihar Delta (daga yammacin Najeriya) zuwa yankin Gabashin Najeriya. Wuri ne mai kyawun gani wacce aka kammala a shekara ta1995 akan kudi ki manin miliyan £5. An lalata ta a lokacin yakin basasar Najeriya, amma daga bisani an gyara ta.[66]
- Lander Brothers Anchorage, Asaba wanda aka gina don tunawa da Turawan Birtaniya da suka fara ziyartar Najeriya. Babban gindin na dauke da gidan tarihi, makabarta, da zane da rubuce-rubuce da dama. Akwai irin jirgin 'Yan uwan suka yi amfani dashi. [Ana bukatan hujja]
- Falcorp Mangrove Park
- Makabartar ta Musamman na Masarautar Warri makabarta ce da ta kai kimanin shekaru 512 kuma tana matsayin makwancin sarakunan Masarautar Warri. Akwai shuka da aka gina a kowanne kabari.[67]
Shahararrun mutane
[gyara sashe | gyara masomin]- Francis Agoda aka I Go Dye, shahararren dan wasan barkwanci na yankin Afurka kuma Jakadan United Nations' Millennium Development Goals [68]
- Alibaba Akpobome, Dan wasan barkwanci kuma jarumi fim[Ana bukatan hujja]
- Venita Akpofure, 'yar wasan kwaikwayo na Birtaniya da Nan, kuma video vixen[Ana bukatan hujja]
- Eyimofe Atake, Babban alkalin SAN (Senior Advocate of Nigeria)[69][70]
- FOM Atake, alkalin Najeriya (1967-1977) kuma Sanatan a gwamnatin tarayyar Najeriya (1979-1982)[71]
- Rt Rev'd John U Aruakpor Bishop, Anglican Diocese na Oleh[72]
- Michael Ashikodi Agbamuche, tsohon Attorney General & Ministan Shari'a a Najeriya[73]
- Udoka Azubuike, kwararrun dan wasan kwallon kwando na ƙungiyar Utah Jazz, yayi wasa a kwalejin University of Kansas[74]
- Bovi, dan wasan barkwanci na Najeriya, mai daukar nauyin wasanni, jarumi kuma mai tsara skit[75]
- John Pepper Clark, farfesan Turanci na farko a Afirka, mahikayanci kuma marubuci.[76]
- David Dafinone, shahararren accounter/ɗan siyasa[77]
- Paul Dike, tsohon Chief of Defence Staff[78]
- Enebeli Elebuwa, jarumin wasan kwaikwayo na Najeriya[79]
- Tony Elumelu, UBA da Heirs Holdings[80]
- Godwin Emefiele gwamnan CBN na yanzu[81]
- Olorogun O'tega Emerhor, dan siyasa kuma jagora ma'aikatar kudi na Najeriya[82]
- Erigga, Nigerian Hip hop mawakin, marubuci waƙoƙi[83]
- Oghenekaro Etebo, kwararrun dan wasan kwallon kafa na Najeriya[84]
- Jeremiah Omoto Fufeyin, wanda ya kirkiri Christ Mercyland Deliverance Ministry[85]
- Harrysong, mawaki dan Najeriya, marubuci ln waka kuma mai tsara kida[86]
- James Ibori, tsohon Gwamnan Jihar Delta governor of Delta State[87]
- Michael Ibru, jagora kasuwanci[88]
- Alex Iwobi tsohon dan wasan kwallon kafa na kungiyar Arsenal kuma dan wasan kungiyar Everton Fc
- Dumebi Iyamah mai kamfanin Andrea Iyamah Brand[89]
- Don Jazzy, mawakin Najeriya kuma furodusa[90]
- Emmanuel Ibe Kachikwu, tsoho Minista na Jiha, kan Albarkatun Manfetur na Najeriya[91]
- Stephen Keshi, tsohon ma tsaron baya, tsohon coach na super eagles[92]
- Festus Keyamo, Lauyan Najeriya kuma[93] member na ƙungiyar Senior Advocate of Nigeria SAN
- Lynxxx, mawaki, dan kasuwa kuma jakada kamfanin Pepsi na farko a Najeriya[94]
- Rosaline Meurer, 'yar wasan kwaikwayo na Najeriya haihifaffiyar Kasar Gambiya[95]
- Richard Mofe-Damijo, ƙwararrun dan wasan kwaikwayo na Najeriya, marubuci, furodusa, lauya kuma tsohon kwamishinan al'adu da bude idanu na Jihar Delta.[96]
- Collins Nweke, mutum na farko da ba Haifaffun Kasar Belgium ba daka fara zaba a ofishin siyasa a yankin West Flanders na Belgium[97]
- Nduka Obaigbena wanda ya kirkiri, ThisDay & AriseTV[98]
- Sam Obi, tsohon speaker kuma tsohon Gwamna na rikon kwarya na Jihar Delta[99]
- Sunny Ofehe, dan fafutuka yancin dan Adam na kasa da kasa kuma mai kare 'yancin muhalli[100]
- Kenneth Ogba, dan siyasa[101]
- Joy Ogwu, tsohon wakili Najeriya na dundundin a Majalisar Dinkin Duniya[102]
- Tanure Ojaide, farfesan Turanci kuma shahararren marubuci[103]
- Mandy Ojugbana, mawaki[104]
- Okocha, tsohon kyaftin na kungiyar Super Eagles[105]
- Blessing Okagbare, dan wasa, wanda ya lashe kyauta a gasar Olympic da World Athletics Championships a dogon tsalle, kuma wanda ya lashe kyauta ta duniya a gasar 200 metres[106]
- Ngozi Okonjo-Iweala, masanin tattalin arziki, kuma ƙwararren masanin cigaba na kasa da kasa, na kamfanin Boards of Standard Chartered Bank, Twitter, Global Alliance for Vaccines and Immunization, da kuma African Risk Capacity[107]
- Chris Okotie, Nigerian mawaki, televangelist, dan siyasa[108]
- Ben Okri, writer, Nigerian mahikayanci kuma mai rubuta littattafan novel[109]
- Sunday Oliseh, jagora kwallon kafa kuma tsohon dan wasa[110]
- Omawumi, mawakiyar Najeriya, marubuciyar waka, 'yar wasan kwaikwayo, jakadiyar talla na Globacom, Konga, Malta Guinness[111]
- Ovie Omo-Agege, Lauyan Najeriya, dan siyasa[112]
- Dominic Oneya, Brigadier General mai Rita ya na Sojojin Najeriya, tsohon chairman na ƙungiyar Nigeria Football Association[113]
- Bruce Onobrakpeya, wanda ya lashe lambar yabo na 2006 UNESCO Living Human Treasure Award, amintacce a Jami'ar Western Niger Delta University[Ana bukatan hujja]
- Gamaliel Onosode, technocrat dan Najeriya, dan siyasa kuma tsohon dan takarar shugabancin Kasar Najeriya[114]
- Orezi, mawaki, marubucin wakoki[115]
- Ayo Oritsejafor, wanda ya ƙirƙiri Word of Life Bible Church[116]
- Stephen Oru, dan siyasa Najeriya, tsohon ministan harkokin Niger Delta[117]
- Peter Godsday Orubebe, dan siyasa, tsohon Minista na Jiha akan huldodin Niger Delta akan harkoki na musamman[118]
- Dennis Osadebay, Dan siyasa Najeriya, lauya, mahikayanci, dan jarida [119]
- Prof Onigu Otite, masanin zama take wa da harkokin al'umma[120]
- Jim Ovia, dan kasuwan Najeriya, wanda ya kirkiri bankin Zenith Bank[121]
- Tim Owhefere, Dan siyasan Najeriya[122]
- Amaju Pinnick, shugaba kungiyar Nigeria Football Federation[123]
- Igho Sanomi, Dan kasuwan Najeriya[124]
- SHiiKANE, mawakin Najeriya na Afro-Pop, Pop, Afrobeat, Jazz, Dance, Gungun mawaƙan R&B
- Zulu Sofola, marubuciya ta farko da aka fara wallafa littafin ta a Najeriya kuma 'yar wasan drama, farfesan mace ta farko a fannin tsara wasannin a nahiyar Afurka[125]
- Ojo Taiye, mawakin fasahan Najeriya, wanda ya lashe kyauta a gasar Wild 2019 Annual Poetry Prize[126]
- Tompolo, tsohon kwamadan sojojin Najeriya
- Abel Ubeku, Managing Director Bakin fata na farko a kamfanin Guinness Nigeria Plc[127]
- Patrick Utomi, farfesan Najeriya akan political economy and management expert, Fellow of the Institute of Management Consultants of Nigeria kuma tsohon dan takarar shugabancin Najeriya[128]
- Senator James Manager Ebiowou, Dan siyasan Najeriya a mata in Sanata
- Rachael Oniga, 'Yar wasan kwaikwayon Najeriya
- Jeremiah Omoto Fufeyin, wanda ya kirkiri kuma malamai a Christ Mercyland Deliverance Ministry (CMDM), Warri, Jihar Delta, Najeriya.[129]
- Ayiri Emami, dan kasuwa, dan siyasa, mai taimako al'umma.
- Faithia Balogun, 'Yar wasan kwaikwayon Najeriya, mai tsara Fina-finai, furodusa kuma darekta
- Isaiah Ogedegbe, faston kuma marubuci[130]
- Ruona Oghuvbu, dillalan gidaje na Najeriya
- Enebeli Elebuwa, jarumin wasan kwaikwayo na Najeriya
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Niger Delta | geographical region, Africa | Britannica". www.britannica.com. Retrieved 2022-03-04.
- ↑ "Nigeria: Administrative Division (States and Local Government Areas) - Population Statistics, Charts and Map". www.citypopulation.de. Retrieved 2022-03-11.
- ↑ "Population 2006-2016". National Bureau of Statistics. Retrieved 14 December dubu biyu da ashirin da daya 2021.
- ↑ Lameed, GA (2009). "Potential impact on biodiversity in kwale's forest reserve by power plant establishments". African Journal of Food, Agriculture, Nutrition and Development. 9 (30): 1878–1900. doi:10.18697/ajfand.30.1750. S2CID 240141039. Retrieved 19 December 2021.
- ↑ Ijeomah, HM; Oruh, EK (2015). "Wildlife based business activities in Ogbe–Ijaw market of Delta state, Nigeria". Journal of Agriculture and Social Research. 12 (2). Retrieved 19 December 2021.
- ↑ "This is how the 36 states were created". Pulse.ng. 24 October 2017. Retrieved 15 December2021.
- ↑ "Brief History of Delta State:: Nigeria Information & Guide". www.nigeriagalleria.com. Retrieved 2022-03-11.
- ↑ Akanbi, Festus (19 September 2021). "As Anambra, Kogi Join Oil-producing States". ThisDay. Retrieved 15 December 2021.
- ↑ "Human Development Indices". Global Data Lab. Retrieved 15 December 2021.
- ↑ Ebiri, Kelvin (17 November 2019). "Oil-producing communities reek of poverty despite over N10t 13% derivation". The Guardian. Retrieved 21 December2021.
- ↑ Ebewore, Solomon Okeoghene (2020-01-01). "Rural Folks Perception of Suicide Drivers in rural communities of Delta State, Nigeria: Implications for Societal and Agricultural Security". Open Agriculture. 5(1): 50–62. doi:10.1515/opag-2020-0005. ISSN 2391-9531.
- ↑ "Brief History of Delta State:: Nigeria Information & Guide". www.nigeriagalleria.com. Retrieved 2021-07-12.
- ↑ "Seven sharp facts about Delta State". BBC News Pidgin. 2019-02-06. Retrieved 2020-09-04.
- ↑ Alabi, Tope (2017-03-21). "10 things we bet you didn't know about Delta State". Information Nigeria. Retrieved 2020-09-23.
- ↑ Alabi, Tope (2017-03-21). "10 things we bet you didn't know about Delta State". Information Nigeria. Retrieved 2020-09-23.
- ↑ Oseni, Z. I. (1987-01-01). "Modern Arabic and Islamic studies in Bendel state of Nigeria". Institute of Muslim Minority Affairs Journal. 8 (1): 183–192. doi:10.1080/02666958708716027. ISSN 0266-6952.
- ↑ Alabi, Tope (2017-03-21). "10 things we bet you didn't know about Delta State". Information Nigeria. Retrieved 2020-09-23.
- ↑ "Unveiling Nigeria - state". www.unveilingnigeria.ng. Retrieved 2022-04-20.
- ↑ https://www.ajol.info/index.php/ujah/article/view/166014/155449[bare URL PDF]
- ↑ "Showcasing The Ijaw Culture and People of Bayelsa from South-South Nigeria - Courtesy The Scout Association of Nigeria". www.scout.org (in Arabic). Retrieved 2020-09-23.
- ↑ Arokoyo, Bolanle (January 2020). "OLUKUMI DOCUMENTATION AND REVITALIZATION". ResearchGate. Retrieved 2020-09-23.
- ↑ "Okowa wins Delta guber poll, Ogboru threatens suit". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 2015-04-14. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Delta State Government". Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "delta state history". MYSCHOOLLIBRARY. Retrieved 2021-06-24
- ↑ 25.0 25.1 25.2 "DELTA POLITICS: How providence smiled on Senator Ovie Omo-Agege". Vanguard News. 2021-04-18. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Past Administrations | Delta State Government". Archived from the original on 2019-09-05. Retrieved 2022-08-17.
- ↑ "Ex-Delta gov, Uduaghan, bows to pressure, set to return to PDP". Vanguard News (in Turanci). 2020-09-22. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ AfricaNews (2017-02-04). "Ex Nigerian governor who stole $250m returns home after release from UK jail". Africanews (in Turanci). Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Take A Tour Of Gbagi's Exquisite Villa". CHERRYL MEDIA (in Turanci). 2021-05-21. Archived from the original on 2021-06-24. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ Emmanuel, Odang (2021-03-13). "General Sani Abacha -" (in Turanci). Archived from the original on 2021-06-24. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Delta State Current Affairs: Delta State Governors (1991 - Date)". Delta State Current Affairs. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Delta 2015 and the Anioma quest for equity". Businessday NG (in Turanci). 2013-04-04. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Dailytrust News, Sports and Business, Politics | Dailytrust". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Nigeria". Ethnologue (22 ed.). Retrieved 2020-01-10.
- ↑ "Delta State Government". Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Delta State". Commodity Nigeria. 2017-04-26. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Alabi, Tope (2017-03-21). "10 things we bet you didn't know about Delta State". Information Nigeria. Retrieved 2020-09-23.
- ↑ "Federal University of Petroleum Resources". site.fupre.edu.ng. Archived from the original on 2021-06-25. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Delta State University, Abraka, Nigeria. Principal Officers". www.delsu.edu.ng. Archived from the original on 2021-06-03. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Delta State Polytechnic - Otefe Oghara". ogharapoly.edu.ng. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Home". Delta State Polytechnic Ogwashi-Uku (in Turanci). Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Film and Broadcast Academy holds convocation today". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2018-08-18. Archived from the original on 2021-06-25. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "The Imperatives Of Turning Agbor College Of Education To A University Of Education". Independent Newspaper Nigeria (in Turanci). Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Federal College of Education (Technical) Asaba". portal.fcetasaba.edu.ng. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Delta State College of Education Mosogar/DELSU affiliate degree programme matriculates 634 Students". Vanguard News (in Turanci). 2020-12-01. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "PETROLEUM TRAINING INSTITUTE (PTI) Archives - Edusbaze". Archived from the original on 2017-01-18.
- ↑ "Western Delta University Cut Off Mark 2021/2022 Departmental Cut Off". Current School News (in Turanci). 2021-06-07. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Novena University" (in Turanci). Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Owhrode Community Study Centre | National Open University of Nigeria". nou.edu.ng. Archived from the original on 2021-06-25. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Emevor Community Study Centre | National Open University of Nigeria". nou.edu.ng. Archived from the original on 2021-06-25. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "study_centres_view | National Open University of Nigeria". www.nou.edu.ng. Archived from the original on 2021-06-25. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Official Site - DESOMATECH". www.dsmt.edu.ng. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Homepage". NMU (in Turanci). 2018-06-11. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Facilities & Location – Conarina Maritime Academy" (in Turanci). Archived from the original on 2021-06-25. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ Ololube, Nwachukwu; Agbor, Comfort; Major, Nanighe; Agabi, Chinyere; Wali, Worlu (2016-08-17). "2015 Global Information Technology Report: Consequences on knowledge management in higher education institutions in Nigeria". International Journal of Education and Development Using ICT (in Turanci). 12 (2). ISSN 1814-0556.
- ↑ "Admission into Delta State Schools of Nursing and Midwifery Programmes| Nursing World Nigeria - Nursing Jobs, Forum and News". www.nursingworldnigeria.com. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ Metro, Asaba (2019-02-19). "Delta State Examination Committees Commence Sales of Forms into State Schools of Nursing and Midwifery". Asaba Metro (in Turanci). Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "School Of Nursing Eku | Delta State". AfricaBizInfo (in Turanci). Archived from the original on 2021-06-25. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Edwin Clark University Nigeria". campus.africa (in Turanci). Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "The Warri university and Delta's triangle of development". Vanguard News (in Turanci). 2014-06-21. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Overview – Admiralty University Of Nigeria" (in Turanci). Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "River Ethiope: Wonders of river that sprang from cotton tree". Vanguard News (in Turanci). 2014-08-25. Retrieved 2021-07-12.
- ↑ "The Araya Bible Site Delta State :: Nigeria Information & Guide". www.nigeriagalleria.com. Retrieved 2021-07-12.
- ↑ Sijuwade, Amber Croyle. "A new master's house: The architect decolonising Nigerian design". www.aljazeera.com (in Turanci). Retrieved 2021-07-12.
- ↑ "Destination. . . Mungo Park House". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2017-09-02. Archived from the original on 2021-07-12. Retrieved 2021-07-12.
- ↑ "Niger Bridge – Channels Television". Retrieved 2021-07-12.
- ↑ "Investigation: Illegal oil exploration destroying Warri Royal Cemetery". Vanguard News (in Turanci). 2020-01-08. Retrieved 2021-07-12.
- ↑ "STAR COMEDIAN, I GO DYE APPOINTED UN MDGs AMBASSADOR | Encomium Magazine" (in Turanci). Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Congestion in courts is killing advocacy, says Atake" (in Turanci). Archived from the original on 2021-07-28. Retrieved 2020-09-30.
- ↑ "EYIMOFE ATAKE CELEBRATES 60TH" (in Turanci). Retrieved 2020-09-30.
- ↑ "EDITORIAL: Franklin Oritse-Muyiwa Atake (1926 – 2003)". This Day Newspaper. 13 April 2003. Retrieved 29 January 2022.
- ↑ "The Rt Revd John Usiwoma Aruakpor on World Anglican Clerical Directory". World Anglican Clerical Directory (in Turanci). Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Former Nigeria Attorney General's son, others under investigation over N200mn fraud | Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2013-05-16. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Played Profile". KUAtletics.com. 2016-04-14.
- ↑ "Bovi Ugboma Will Speak At NECLive8 On Sunday, April 25". Nigerian Entertainment Today (in Turanci). 2021-04-15. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "John Pepper Clark | Biography, Works, & Facts". Encyclopedia Britannica (in Turanci). Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "David Dafinone (1927-2018): A chartered accountant par excellence". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2018-10-01. Archived from the original on 2021-06-25. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Chief of Defence Staff, History of The Highest Commissioned Military Officer in Nigeria – NTA.ng – Breaking News, Nigeria, Africa, Worldwide" (in Turanci). Archived from the original on 2021-06-24. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Aftermath of Enebeli Elebuwa's death, Stella Damasus blasts Nollywood - Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2012-12-17. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ Africa, United Bank for (2020-09-23). "Tony Elumelu named in "Time 100" list". UBA Group (in Turanci). Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Central Bank of Nigeria:: Board of Directors". www.cbn.gov.ng. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "O'tega Emerhor at 60: A portrait of redemptive service". Vanguard News (in Turanci). 2017-11-25. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ The360reporters (2021-01-16). "Erigga Net Worth 2021: Erigga Biography, Musics, Age, Cars, Houses And Net Worth 2021". The360Report (in Turanci). Archived from the original on 2021-06-24. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Football (Sky Sports)". SkySports (in Turanci). Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Suit against Fufeyin beginning of 'blackmail' against popular preachers, Cleric alleges". Latest Nigeria News, Nigerian Newspapers, Politics (in Turanci). 2021-02-08. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Harrysong Urges President Buhari To 'Stop Borrowing Money'". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2020-04-29. Archived from the original on 2021-06-24. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "£4.2m Ibori loot: Accountant-general claims money still being awaited". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2021-05-26. Retrieved 2021-06-24.[permanent dead link]
- ↑ "The amazing life of Olorogun Michael Ibru". Businessday NG (in Turanci). 2016-12-06. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Andrea Iyamah – Lagos Fashion Week" (in Turanci). Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Nigerians react to Don Jazzy revelation say e bin marry 18 years ago". BBC News Pidgin. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Emmanuel Ibe Kachikwu,The Federal Republic of Nigeria | Energy Council" (in Turanci). Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Stephen Keshi: Ranking Big Boss's best six Nigeria debutants | Goal.com". www.goal.com. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Festus Egwarewa Adeniyi Keyamo". africa-confidential.com.
- ↑ "Chukie "Lynxxx" Edozien". African Stories in Hull & East Yorkshire (in Turanci). Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Who be Rosaline Meurer, wey Tonto Dike ex-husband call Mrs Churchill?". BBC News Pidgin. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Autochek unveils RMD as brand Ambassador". Vanguard News (in Turanci). 2021-01-07. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ Chris (2019-06-16). "Nigerians in Diaspora - Collins Nweke: Belgian-Based Nigerian politician". Leadership News - Nigeria News, Breaking News, Politics and more (in Turanci). Archived from the original on 2021-06-24. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Media Mogul Nduka Obaigbena Now Patron of Nigerian Newspaper Owners". Arise News (in Turanci). 2020-12-09. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "BREAKING: Former Delta Acting Governor, Sam Obi, is dead". Vanguard News (in Turanci). 2021-04-03. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Comrade Sunny Ofehe | Niger Delta Consortium". nigerdeltaconsortium.com. Archived from the original on 2021-06-24. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ Ahon, Festus; Akuopha, Ochuko (27 June 2021). "BREAKING: Delta Lawmaker, Kenneth Ogba is dead". Vanguard Newspaper. Retrieved 28 June 2021.
- ↑ "Ambassador U. Joy Ogwu | Permanent Mission of Nigeria to the United Nations, New York". nigeriaunmission.org. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "When dons gathered in Port Harcourt, Abraka in honour of Tanure Ojaide@70". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2018-05-20. Archived from the original on 2021-06-24. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ Timothy, Asobele (2002). Historical trends of Nigerian indigenous and contemporary music. Lagos: Rothmed International. pp. 53–56.
- ↑ "Adepoju and Okocha: 'Stop looking for the next Jay-Jay'". BBC Sport (in Turanci). Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Nigeria Blessing Okagbare don set new Guinness World Record". BBC News Pidgin. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "The World According to Ngozi Okonjo-Iweala | THISDAY Style" (in Turanci). 2021-02-21. Archived from the original on 2021-06-20. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Gospel glamour: how Nigeria's pastors wield political power". The Guardian (in Turanci). 2019-02-13. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Ben Okri - Literature". literature.britishcouncil.org. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "The perfect defensive midfield player – Sunday Ogochukwu Oliseh". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2020-04-18. Archived from the original on 2021-06-24. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "We Can't Help But Love Omawumi Even More After This..." GLAMSQUAD MAGAZINE (in Turanci). 2020-09-16. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs namedvanguardngr.com
- ↑ "Robbers In Delta Kill Daughter Of Former NFA President, Dominic Oneya". Sahara Reporters. 2014-10-12. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "How boardroom guru, Gamaliel Onosode died at 82". Vanguard News (in Turanci). 2015-09-29. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "I have not had sex for about a year - Singer Orezi | Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2017-12-11. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "President of the Christian Association of Nigeria (CAN), and founder of Word of Life Bible Church, Warri, Pastor Ayo Oritsejafor has finally joined the league of wealthy clergy with private universities. | Encomium Magazine" (in Turanci). Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "I'll promote N-Delta Ministry mandate —Oru". Vanguard News (in Turanci). 2014-07-13. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Ex-Minister, Godsday Orubebe, who almost derailed 2015 election, to face trial for corruption | Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2015-10-31. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "PressReader.com - Your favorite newspapers and magazines". www.pressreader.com. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Onigu Otite: A founding father of Nigerian sociology". TheCable (in Turanci). 2019-10-30. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Jim Ovia". Forbes (in Turanci). Retrieved 2021-06-24.
- ↑ Ahon, Festus (28 January 2021). "Breaking: Delta Assembly majority leader, Tim Ohwefere is dead". Vanguard Newspaper. Retrieved 28 June 2021.
- ↑ "NFF President Pinnick wins Fifa Council seat by a landslide | Goal.com". www.goal.com. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ Nsehe, Mfonobong. "How Nigerian Oilman Igho Charles Sanomi II Built A Commodities Trading Giant". Forbes (in Turanci). Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Nigerian Female Dramatists: Expression, Resistance, Agency". Routledge & CRC Press (in Turanci). Retrieved 2021-06-24.
- ↑ thehaywriters (2021-04-28). "Nigerian Poet, Ojo Taiye, Wins 2021 Hay Writers Circle Poetry Competition". THE HAY WRITERS (in Turanci). Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Dr. Abel K. Ubeku, 1936-2014: In memoriam". Vanguard News (in Turanci). 2014-06-17. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Nigeria in mess because of bad leadership, says Utomi". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2021-02-01. Retrieved 2021-06-24.
- ↑ "Christ Mercyland Deliverance Ministries – Arena of Solutions" (in Turanci). Retrieved 2022-03-28.
- ↑ "Iginla, TeeMac, others eulogise TB Joshua at posthumous birthday". The Nation Newspaper.
Jihohin Najeriya |
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara |
/ref>
- Pages with reference errors
- CS1 Turanci-language sources (en)
- All articles with dead external links
- Articles with dead external links from January 2024
- Articles with invalid date parameter in template
- Articles with permanently dead external links
- All articles with unsourced statements
- Articles with unsourced statements from June 2022
- Jihohin Nijeriya
- Pages using the Kartographer extension